Kano da Wasu Jihohi 10 Sun Ragewa Mutane Wahala a Tsarin Dokar Haraji a Najeriya
- Kwamitin gyaran haraji na shugaban kasa ya bayyana cewa jihohi 11 sun karbi sabuwar dokar da ta soke karbar kudin haraji a hannu
- Shugaban kwamitin, Taiwo Oyedele ya ce dokar ta kuma soke wasu kananan haraji da ake karba daga hannun jama'a
- Ya ce akwai wasu karin jihohi 10 da suka tura dokar ga majalisar dokoki domin amincewa da ita gabanin ta fara aiki a hukumance
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Jihohi 11 a Najeriya sun amince da tsarin sabuwar dokar harajin bai-daya wadda ta kawo karshen karbar kudin haraji daga jama'a a hannu.
Wannan dokar ta soke wasu kananan haraji masu addabar jama’a kamar harajin rediyo da talabijin da harajin caca, sannan ta haramta sanya shinge a kan tituna domin karbar kudi daga hannun ’yan kasuwa.

Source: Twitter
Jihohi 11 da suka sauya tsarin haraji
Leadership ta ruwaito cewa jihohin da suka amince da sabuwar dokar sun hada da: Bayelsa, Anambra, Ekiti, Gombe, Kogi, Nasarawa, Filato, Kwara, Zamfara, Kano, da Kuros Riba.
Bugu da kari, wasu karin jihohi 10 sun tura makamanciyar wannan doka zuwa majalisun dokokinsu, yayin da wasu ke dab da kammala shirin amincewa da ita.
Wannan mataki na nuni da hadin kan siyasa da ba a saba gani ba domin gyara tsarin kudaden shiga na kasar, in ji rahoton Daily Post.
Shugaban kwamitin shugaban kasa kan manufofin kudi da gyaran haraji, Taiwo Oyedele, ne ya bayyana hakan a wajen taron tattaunawa da hukumar SMEDAN ta shirya a Abuja.
Oyedele ya fadi amfanin tsarin harajin
Ya bayyana matakin a matsayin gagarumin sauyi, wanda zai kawo karshen tsawon shekarun da aka shafe ana karbar haraji ba bisa ka'ida ba.
"Wannan ya nuna cewa kasar nan ta fuskanci matsalar da ta durkusar da sana'o'i na shekaru da dama. Yadda jihohi ke yi wajen amincewa da wadannan dokoki ya zarce yadda ake tsammani," in ji Oyedele.
Muhimman abubuwan da dokar ta gyara sun hada da soke karbar kudin haraji a hannu, haramta kafa shingaye a hanya domin karbar haraji daga kananun 'yan kasuwa da soke kananun haraji.

Source: Twitter
Oyedele ya bayyana cewa kafin yanzu, tsarin harajin Najeriya ya rarrabu sosai tsakanin gwamnatin tarayya, jihohi, da kananan hukumomi, wanda hakan ke sa 'yan kasuwa biyan haraji iri daya sau da dama.
A cewarsa, Najeriya na da haraji fiye da 60 da aka sani a hukumance, baya ga wasu da dama da ba sa cikin tsarin da gwamnatocin jihohi da kananan hukumomi ke karba.
Ya jaddada cewa yawancin kudaden da ake karba da tsabar kudi suna tafiya ne zuwa aljihun wasu daidaikun mutane maimakon asusun gwamnati.
Ndume ya tabbatat da cushe a dokar haraji
A wani labarin, kun ji cewa Sanata Ali Ndume ya tabbatar da cewa an samu banbanci a dokar harajin da Majalisa ta amince da ita da wacce Shugaba Bola Tinubu ya sanya wa hannu.
Ndume, mai wakiltar Borno ta Kudu a Majalisar dattawa ya yi ikirarin cewa gwamnatin tarayya na wasa da hankalin ‘yan Najeriya kan lamarin.
Ya ce Taiwo Oyedele, shugaban kwamitin shugaban kasa kan gyaran haraji, ya amince cewa akwai “bambance-bambance," wanda ya sa aka samu nau'i biyu na dokar haraji.
Asali: Legit.ng

