Bayan Jirgi Marar Matuki Ya Hallaka Sojoji, Rundunar Ta Fadi Matakin da Ta Dauka

Bayan Jirgi Marar Matuki Ya Hallaka Sojoji, Rundunar Ta Fadi Matakin da Ta Dauka

  • Rundunar Sojin Najeriya ta ce tana aiki da hukumomi domin gano tushen jiragen sama marasa matuka da ‘yan ta’adda ke amfani da su
  • DHQ ta bayyana cewa bincike ya kai matakin gaba, kuma nan ba da jimawa ba za a ɗauki matakai na zahiri
  • Sojoji sun kashe ‘yan ta’adda da dama, sun cafke masu taimaka musu, tare da ceto mutanen da aka sace a Arewa maso Gabas

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja – Hedikwatar Tsaro ta Ƙasa ta yi martani bayan harin ta'addanci da aka kai wa dakarun sojoji a jihar Borno.

Rundunar ta ce tana aiki tare da wasu hukumomin gwamnatin tarayya domin gano da kuma dakile amfani da jiragen sama marasa matuƙa da ‘yan ta’adda ke amfani da su wajen kai hare-hare.

Kara karanta wannan

Sojoji sun kai hari kasuwa a Yobe bayan samun bayanai kan Boko Haram

Rundunar tsaro ta yi martani bayan harin a'addanci kan sojoji
Hafsan sojojin Najeriya, Laftanar-Janar Waidi Shaibu. Hoto: HQ Nigerian Army.
Source: Facebook

Shirin Sojoji na yakar yan ta'adda

Daraktan Yaɗa Labaran Tsaro, Manjo Janar Michael Onoja, ya bayyana hakan ne a Abuja yayin da yake bayani kan nasarorin da sojoji suka samu a kwanan nan, cewar Punch.

A ‘yan watannin baya-bayan nan, ‘yan ta’adda a yankin Arewa maso Gabas sun fara amfani da manyan jirage marasa matuka na zamani wajen kai hari kan fararen hula da jami’an tsaro, lamarin da ya ƙara tayar da hankulan jama’a da masana tsaro.

Manjo Janar Onoja ya ce hukumomin tsaro na bincike kan yadda ake shigo da wadannan jirage cikin ƙasa da kuma hanyoyin da suke bi zuwa hannun ‘yan ta’adda.

Ya ƙara da cewa a cikin ‘yan kwanaki ko watanni masu zuwa, gwamnati za ta ɗauki matakai masu ƙarfi kan lamarin.

Ya ce:

“Mun kai wani mataki mai muhimmanci wajen tsare-tsare tare da sauran hukumomin gwamnatin tarayya domin gano inda wadannan jiragen ke fitowa.
“Mun riga mun tuntubi hukumomin da ke da ƙarfin dakile amfani da jiragen, kuma muna da tabbacin cewa za a ɗauki mataki nan ba da jimawa ba."

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun gwabza fada da 'yan bindiga a Gombe, an kashe 'yan ta'adda

Da yake mayar da martani kan zargin da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa ana tilasta wa sojoji a wuraren bincike a Jihar Bauchi biyan kuɗi na mako-mako ga shugabanninsu, Onoja ya ce har yanzu zargi ne kawai, amma sojoji za su bincika idan an kawo hujjoji.

“Rundunar soji hukuma ce mai gaskiya. Idan an tabbatar da zargin, za a ɗauki matakin da ya dace."

- Cewar sanarwar

An farmaki sojoji da jirage marasa matuka
Taswirar jihar Borno da ke fama da matsalar ta'addanci. Hoto: Legit.
Source: Original

Sojoji sun magantu kan yan gudun hijira

Game da dawowar ‘yan gudun hijirar Najeriya daga Kamaru, Onoja ya ce hakan na nuna nasarar da sojoji suka samu wajen dawo da tsaro a yankunan da rikici ya shafa.

Ya ce rundunar sojoji, tare da gwamnatin tarayya, ta yi iya bakin ƙoƙarinta domin tabbatar da tsaro, kuma dawowar ‘yan gudun hijira alama ce ta nasarar ayyukan soji.

Onoja ya kuma yi bayani kan ayyukan rundunar Operation Hadin Kai a Arewa maso Gabas, inda ya ce sojoji sun hana Boko Haram, ISWAP da Jama’atu Ahlis Sunna Lidda’awati wal-Jihad damar yin abin da suke so, cewar PM News.

Jirage marasa matuka sun farmaki sojoji

Kun ji cewa 'yan ta'addan ISWAP sun kai wani mummunan hari kan dakarun sojojin Najeriya wanda ya yi masu illa sosai.

Kara karanta wannan

Sojoji sun shiga har dajin Sambisa sun yi wa 'Yan Boko Haram jina jina

Harin ta'addancin ya faru ne jihar Borno a yankin Arewa maso Gabas inda rahotanni suka ce sojoji da dama sun rasa rayukansu.

Tsagerun 'yan ta'addan sun yi amfani da jirage marasa matuka a harin da suka kai kan wani sansanin sojoji cikin tsakar dare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.