Yadda Jinkirin Gyara Dokokin Zabe ke Jefa Shakku kan Sahihancin Siyasar 2027

Yadda Jinkirin Gyara Dokokin Zabe ke Jefa Shakku kan Sahihancin Siyasar 2027

  • Kungiyoyin farar hula sun fara matsa wa majalisar tarayya kan jinkirin amincewa da kudurin gyaran dokar zabe, suna gargadin cewa hakan na iya kawo cikas
  • Yayin da Majalisar Wakilai ta riga ta amince da kudurin tun karshen 2025, Majalisar Dattawa ta dakatar da tattaunawa, tana neman karin nazari kan sassan dokar
  • Masana da masu sa ido kan zabe sun ce wannan jinkiri ya jefa hukumar INEC da jam’iyyun siyasa cikin rudani, inda ba a san wane tsari za a bi ba a halin yanzu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Ana ci gaba da samun matsin lamba kan majalisar tarayya, musamman majalisar dattawa, sakamakon jinkirin amincewa da kudurin gyaran dokar zabe ta 2025.

Kungiyoyin farar hula da sauran masu ruwa da tsaki kan harkar zabe sun bayyana damuwa cewa jinkirin na iya lalata ingancin shirye-shiryen zabe da kuma rage amincewar jama’a.

Kara karanta wannan

Bayan shiga APC, Abba zai kawo karshen rikicin Sanusi II da Aminu Ado Bayero

Shugaban INEC da Godswil Akpabio
Farfesa Joash Amupitan da Godswill Akpabio. Hoto: Nigerian Senate|INEC Nigeria
Source: Twitter

Rahoton Daily Trust ya nuna cewa sun ce duk da muhimmancin dokar, har yanzu majalisar dattawa ba ta kammala aikinta a kai ba, lamarin da ke kara tayar da kura a fagen siyasa.

Maganar majalisar tarayya kan dokar zabe

Rahotonni sun bayyana cewa majalisar wakilai ta riga ta yi nazari tare da amincewa da Kudurin Gyaran Dokar Zabe a watan Disamba, 2025, kafin ‘yan majalisa su tafi hutun Kirsimeti da Sabuwar Shekara.

A daya bangaren kuma, an ce majalisar dattawa ba ta kammala aikin ba kafin shiga hutun, kuma hakan ya kara jinkirta tafiyar kudurin.

A wani zama da aka yi, majalisar dattawa ta sake dage duba rahoton kudurin, inda ta yanke shawarar mayar da shi wani zaman sirri domin yin karin nazari dalla-dalla.

Dalilan jinkiri daga bangaren 'yan majalisa

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya ce dole ne majalisar ta yi taka-tsantsan wajen duba kudurin saboda tasirinsa ga dimokuradiyyar Najeriya.

Kara karanta wannan

Akpabio ya saɓa da kwamitin majalisa, ya kare Tinubu kan zargin cushe a dokokin haraji

Punch ta ce ya jaddada cewa gaggawa ba tare da cikakken nazari ba na iya jawo rigingimun shari’a bayan takara, maimakon samar da sahihin zabe.

Sanata Godswill Akpabio a majalisa
Sanata Godswill Akpabio yayin zaman majalisar dattawa. Hoto: Nigerian Senate
Source: Facebook

An kuma bayyana cewa rashin halartar shugaban kwamitin da ke kula da harkokin zabe ya kara kawo tsaiko, wanda hakan ya sa aka dage gabatarwa da muhawara kan kudurin.

Korafi daga kungiyoyin farar hula

A bangare guda, kungiyoyin farar hula sun fito zanga-zanga a harabar Majalisar Tarayya a Abuja, suna kira da a gaggauta amincewa da kudurin ba tare da wani jinkiri ba.

Masu zanga-zangar sun rike alluna masu dauke da sakonni da ke bukatar a fifita gyaran dokar zabe domin inganta sahihancin zaben 2027.

Sun bayyana cewa jinkirin da ake yi, musamman daga majalisar dattawa, ba shi da dalili mai karfi duba da karatowar lokacin zabe.

Tasirin jinkirin ga INEC da zabe

Shugaban wata kungiya mai sa ido kan zabe, Bukola Idowu, ya ce jinkirin ya jefa hukumar INEC cikin rudani, domin doka ta wajabta ta fitar da jadawalin zabe a kalla shekara guda kafin zabe.

Ya bayyana cewa INEC ba za ta iya tsara jadawali ba, ganin cewa ba a san ko wasu muhimman sassan dokar zabe za su sauya ba.

Kara karanta wannan

Juyin mulki: Yadda Kanal na soja ya tsara kifar da Gwamnatin Bola Tinubu

A cewarsa, wannan yanayi ya shafi jam’iyyun siyasa, hukumomin tsaro, bangaren shari’a har ma da kasashen waje, lamarin da ka iya yin illa ga sahihanci da amincewar zaben 2027.

Ana neman sauke shugaban INEC

A wani labarin, kun ji cewa majalisar shari'ar Musulunci ta kasa ta yi kira ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan sauke shugaban INEC.

Dr Bashir Aliyu Umar ne ya bayyana haka yayin wani taro da majalisar shari'a ta shirya game da watan Ramadan a birnin tarayya Abuja.

Majalisar ta ce shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan ya taba rubuta labaru marasa tushe yana cewa ana yi wa Kiristoci kisan kare dangi a Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng