Ma'auratan da Suka Yi Garkuwa da Kansu Sun Karbi Fansa N10m

Ma'auratan da Suka Yi Garkuwa da Kansu Sun Karbi Fansa N10m

  • Wasu ma’aurata a jihar Legas sun shirya satar kansu domin karɓar kuɗin fansa N10m daga iyalai da abokan arziki
  • Tuni dai asirin wadannan ma'aurata ya tonu, bayan ‘yan sanda sun cafke su a Mushin bayan gano kuɗin fansar a jaka
  • Hukumar ‘yan sanda ta ce za a gurfanar da su a gaban kotu bayan kammala bincike a kan wannan mugu hali da suka yi

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Lagos – Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta cafke wasu ma’aurata da aka bayyana da sunayen Fred da Goodness.

An kama su ne bisa zargin shirya satar kansu da kansu, tare da karɓar kuɗin fansa Naira miliyan 10 daga iyalansu da abokan arziki.

Yan sanda sun kama wasu ma'aurata a Legas
Wasu daga cikin dakarun yan sandan Najeriya Hoto: Nigeria Police Force
Source: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa rahotanni sun ce ma’auratan sun ƙirƙiri labarin an sace su ne domin tara kuɗin da mijin ke bukata don komawa Amurka.

Kara karanta wannan

Jarumin Nollywood ya shiga hannu a kan zargin shirin juyin mulki

Yadda ma'aurata suka shirya sace kansu

Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a ranar 7 ga Janairu, 2026, lokacin da ma’auratan suka tuntubi ‘yan uwa daga bangarorin iyalai biyu.

A lokacin, sun sanar da su cewa an yi garkuwa da su, tare da buƙatar a tura kuɗin fansa cikin gaggawa.

Saboda tsoro da damuwa, iyalan sun haɗa kai, suka tara N10m cikin kwanaki uku, suna zaton hakan ne kaɗai zai ceci rayukan ‘yan uwansu.

Sai dai wata majiya daga rundunar ‘yan sanda ta bayyana cewa shirin an yi shi ne da amincewar ma’auratan gaba ɗaya.

Ta ce mijin yana da niyyar komawa Amurka, amma saboda rashin kuɗi, suka yanke shawarar shirya satar kansu a matsayin hanya ta tara kuɗi cikin sauri.

'Yan sanda sun gano 'karyar ma'auratan

Bisa ga bayanan ‘yan sanda, ma’auratan sun tsara wani wuri a makaranta da ke Cappa, a yankin Mushin na jihar Legas, inda za a kai kuɗin fansar.

Kara karanta wannan

Sai Tinubu: 'Dan Atiku ya sha alwashi, za a hadu da shi a kada mahaifinsa a 2027

An kama ma'auratan suna tsaka da karban kudin fansa
Taswirar jihar Legas inda ma'aurata suka yi garkuwa da kansu Hoto: Legit.ng
Source: Original

Jami’an tsaro da ke sa ido a yankin sun lura da matar ta shiga makarantar ita kaɗai, yayin da mijin ya iso bayan wasu mintuna.

Sai dai hankalin jami’an ya tashi lokacin da suka ga su biyun sun fito tare suna ɗauke da jaka, wacce alamu suka nuna da nauyinta.

An dakatar da su nan take, aka binciki jakar, inda aka gano kuɗin fansar N10m. Wannan ya sa aka cafke su a wurin.

A yayin bincike, matar ta amsa cewa ita ce ta ƙarfafa mijinta su shirya wannan shiri na satar kansu domin samun kuɗi.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Legas, Abimbola Addebisi, ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce za a gurfanar da ma’auratan a gaban kotu bayan kammala bincike.

An yi garkuwa da mutane a Kaduna

A wani labarin, kun ji cewa aƙalla ‘yan kasuwa huɗu ne suka faɗa hannun wasu mahara a Kaduna yayin da suke kan hanyarsu ta komawa gida bayan sun kammala sayayya a kasuwa.

Kara karanta wannan

An gano jiha 1 da Tinubu zai iya amincewa a kirkira a Najeriya

Rahotanni sun tabbatar da cewa yan bindigar sun yi wa 'yan kasuwar kwanton bauna a hanyar Maro zuwa Kajuru, suka tattara su suka yi awon gaba da su zuwa cikin daji.

Wata majiya da ta tabbatar da faruwar lamarin ta bayyana cewa ‘yan kasuwar sun haɗu da matsala ne a kan titin Maro zuwa Kajuru, inda wasu ‘yan bindiga suka yi musu kwanton bauna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng