Ana Tsaka da Tuhumar Yahaya Bello, Kotu Ta ba Shi Damar Tafiyar Saudiyya
- Kotun Tarayya da ke Abuja ta amince wa tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello, ya je Saudiyya domin yin Umrah ta shekarar 2026
- Alkali Emeka Nwite ya bayar da umarnin sakin fasfo dinsa na wucin gadi duk da shari’ar almundahanar N80.2bn da EFCC ke masa
- EFCC ta ce ba ta hana tafiyar Umrah ba, amma ba za ta amince da jinkirta ranakun shari’ar da kotu ta riga ta tsayar ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta ba tsohon gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello, izinin tafiya zuwa kasar Saudiyya.
Kotun ta ba shi wannan damar domin shiga Saudiyya saboda gudanar da Umrah ta shekarar 2026 da muke ciki.

Source: Facebook
An sahalewa Yahaya Bello zuwa Saudiyya
Alkalin kotun, Mai shari’a Emeka Nwite ya bayar da umarnin sakin fasfon kasa da kasa na Bello na wucin gadi, wanda ke hannun kotu, domin ya samu damar yin wannan ibada, cewar Punch.
A halin yanzu, Bello na fuskantar shari’a a gaban kotun kan zargin karkatar da kudade, shari’ar da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta EFCC ta shigar da shi.
Hukumar EFCC na tuhumar tsohon gwamnan da aikata safarar kudi da ya kai kimanin Naira biliyan 80.2, zargin da Bello ya musanta lokacin da aka gurfanar da shi a gaban kotu.
A cikin wata bukata da aka shigar ranar 20 ga watan Janairu, tare da goyon bayan rantsuwar bayanai mai sakin layi 24 da Bello kansa ya yi, ya roki kotu ta ba shi izinin tafiya Saudiyya domin yin addu’o’i.
Lauyan da ke jagorantar lauyoyinsa, Joseph Daudu, SAN, ya shaida wa kotu cewa an shigar da bukatar ne domin bai wa wanda ake tuhuma damar ziyartar Kasa Mai Tsarki a watan Ramadan domin yin Umrah.
Daudu ya kara da cewa Bello bai ziyarci Kasa Mai Tsarki ba sama da shekaru takwas, yana mai cewa akwai bukatar ya je ya roki Allah ya tsarkake shi daga zarge-zargen da EFCC ta shigar masa.

Source: Facebook
Dalilin barin Yahaya Bello ya je Saudiyya

Kara karanta wannan
Jerin manyan sojoji 16 da hedkwatar tsaro 'ta gano' suna da hannu a shirin kifar da Tinubu
Da take mayar da martani, babbar lauyar masu gabatar da kara, Kemi Pinheiro, SAN, ta ce bangaren tuhuma ba zai hana Bello yin tafiyar Umrah ba, amma ta jaddada cewa ba za su amince da jinkirta kowanne ranar shari’a da kotu ta riga ta tsayar ba.
A cikin gajeriyar hukunci, Mai shari’a Nwite ya amince da bukatar sakin fasfon kasa da kasa na Bello, wanda aka ajiye a hannun magatakardar kotu, cewar TheCable.
Alkalin ya ce:
“Na saurari dukkan hujjojin lauyoyi a wannan shari’a, kuma na ga ya dace a amince da bukatar.”
Saboda haka, kotun ta amince da sakin fasfon daga ranar 13 ga Maris, 2026, na tsawon kwanaki 10, tare da dage shari’ar zuwa Juma’a, 30 ga Janairu, domin ci gaba da sauraron shaidar shaida ta bakwai ta bangaren tuhuma.
An gano batan miliyoyi a badakalar Yahaya Bello
Kun ji cewa Shaida a kotu ta bayyana yadda Hukumar Haraji ta Jihar Kogi ta rika tura makudan kudi zuwa wani kamfani mai zaman kansa.
Shaidu sun ce an canja ma'ajiyar kudade sama da miliyan 57 zuwa 242 daga KSIRS zuwa wani kamfani daban.
EFCC na tuhumar tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello, da karkatar da fiye da ₦110bn, duk da cewa ya musanta zargin.
Asali: Legit.ng
