An ‘Gano’ Wani Shiri da Masu Juyin Mulki Suka Yi domin Hana Buhari ba Tinubu Mulki

An ‘Gano’ Wani Shiri da Masu Juyin Mulki Suka Yi domin Hana Buhari ba Tinubu Mulki

  • Rahotanni sun bayyana cewa wasu manyan sojoji sun shirya juyin mulki domin katse mika mulki a ranar 29 ga watan Mayun 2023
  • Rahoton ya ce an zargi tsohon gwamnan Bayelsa, Timipre Sylva, da daukar nauyin shirin bayan gano makudan kudi da aka yi amfani da su
  • Jami’an tsaro sun bankado shirin ne bayan sirrin bayanai daga soja da DSS, lamarin da ya kai ga cafke mutane da wasu jami’ai da dama

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Karin bayanai na ci gaba da fitowa game da yunkurin juyin mulki da aka yi a Najeriya kan gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.

Yayin da ‘yan Najeriya ke shirin murnar mika mulki a ranar 29 ga Mayu, 2023, wasu jami’an soji sun shiga wani shiri a boye domin kifar da dimokuradiyyar kasar.

Kara karanta wannan

Masu safarar makamai ga tantirin jagoran 'yan bindiga sun shiga hannun jami'an tsaro

Yadda aka yi 'yunkurin' hana Buhari mikawa Tinubu mulki
Shugaba Bola Tinubu da marigayi Muhammadu Buhari. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Yadda aka shirya dakile mulkin dimukradiyya

Rahoton Premium Times ya ce an shirya kifar da gwamnatin da kuma hallaka manyan shugabannin siyasa a fadin kasar,

Majiyoyi sun nuna cewa wadanda ake zargin sun shirya tayar da rikici mai tsanani domin katse mika mulki daga marigayi Muhammadu Buhari zuwa Bola Ahmed Tinubu.

Majiyoyi sun bayyana cewa jagoran shirin juyin mulkin shi ne Alhassan Ma’aji, wani Kanal a rundunar sojin kasa mai lambar aiki N/10668, dan asalin jihar Neja, kabilar Nupe.

An ce an tsara juyin mulkin ne a ranar rantsar da shugaban kasa, amma aka dakatar da shirin saboda karancin kudade da matsalar dabaru.

Sai dai rahoton ya ce a shekarar 2025 aka sake farfado da shirin bayan tsohon gwamnan jihar Bayelsa, Timipre Sylva, ya aika kudade kusan Naira biliyan 1 zuwa wasu asusun bankuna uku.

Daga baya hukumar EFCC ta ayyana Sylva a matsayin wanda ake nema, bayan sojoji sun kai samame gidansa bisa binciken shirin kifar da gwamnatin Tinubu, duk da cewa ya musanta hannu a lamarin.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: An fallasa yadda aka shirya kashe Tinubu, Shettima da wasu mutum 2

Bayanai sun fito kan yunkurin juyin mulki a Najeriya
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Facebook

Manyan da aka shirya hallakawa a juyin mulkin

Bincike ya nuna cewa masu shirya juyin mulkin sun yi niyyar kashe Bola Tinubu, Mataimakinsa, Kashim Shettima, Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio da Kakakin Majalisar Wakilai,Tajudeen Abbas.

Haka kuma an ce sun shirya hallaka manyan hafsoshin tsaro, ciki har da Shugabannin Rundunonin Soji da Kwamandan 'Guards Brigade'.

An kuma ware wasu jami’ai domin kwace iko da fadar shugaban kasa, sansanin barikin Niger, hedikwatar rundunonin soji da filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe.

Yadda aka bankado shirin kifar da gwamnati

Rahoton ya ce hadin gwiwar sirrin leken asiri tsakanin hedikwatar sojoji da hukumar DSS ne ya dakile shirin kifar da gwamnati.

An ce wani soja da ke da cikakken bayani kan shirin ne ya sanar da Shugaban Rundunar Sojin Kasa a wancan lokaci, Olufemi Oluyede, saboda tsoron kada a hada shi da laifin cin amanar kasa.

Haka nan, DSS ta samu bayanan sirri masu zaman kansu da ke nuna cewa wasu sojoji na shirin girgiza gwamnati da lalata dimokuradiyyar Najeriya.

Kara karanta wannan

'Dan bindiga da ya hana Turji, yaransa sakewa ya mutu, an kashe shi wurin sulhu

Juyin mulki: Za a hukunta sojoji 16 a kotu

Kun ji cewa akalla jami’an soji 16 da ake zargi da yunkurin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

An ce sojojin za su fuskanci hukunci mai tsanani idan kotu ta tabbatar da laifinsu inda rahotanni suka tabbatar da samunsu da hannu a yunkurin kifar da gwamnati.

Biyo bayan lamarin, wasu tsofaffin hafsoshin soji sun ce dokar sojin Najeriya ta tanadi hukuncin kisa ga duk wanda aka samu da laifin yunkurin kifar da gwamnati.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.