Masu Safarar Makamai ga Tantirin Jagoran 'Yan Bindiga Sun Shiga Hannun Jami'an Tsaro

Masu Safarar Makamai ga Tantirin Jagoran 'Yan Bindiga Sun Shiga Hannun Jami'an Tsaro

  • Jami'an tsaro sun samu nasarar yin caraf da wasu mutane da ke safarar makamai a jihar Sokoto da ke yankin Arewa maso Yammacin Najeriya
  • Mutanen dai an cafke su ne lokacin da suke yunkurin karbo makamai domin kai wa ga tantirin jagoran 'yan bindiga a jihar Zamfara
  • Majiyoyi sun bayyana yadda jami'an tsaron suka samu nasarar cafke mutanen da ake zargi wadanda suke tafiya a kan babura

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Sokoto - Jami’an tsaro a jihar Sokoto sun cafke wasu mutane biyu da ake zargin masu safarar makamai ne.

Jami'an tsaron sun cafke mutanen ne yayin da suke kokarin kai makamai zuwa hannun wani fitaccen jagoran ‘yan bindiga a jihar Zamfara.

Jami'an tsaro sun cafke masu safarar makamai a Sokoto
Shugaban rundunar sojojin kasan Najeriya, Waidi Shaibu Hoto: @NigerianArmyInfo
Source: Twitter

Masani kan harkokin tsaro a yankin tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

An 'gano' wani shiri da masu juyin mulki suka yi domin hana Buhari ba Tinubu mulki

Yadda aka cafke masu kai wa Baleri makamai

Wata majiya ta ce a ranar 27 ga Janairun 2026, da misalin karfe 10:00 na dare, jami’an PMF 7 da ke gudanar da aikin bincike na yau da kullum a Bimasa da ke karamar hukumar Tureta, sun tare wasu mutane.

Jami'an tsaron dai sun dakatar da mutanen guda biyu da ke kan babura bayan da suka nuna alamun shakku.

An bayyana sunayen wadanda ake zargin da Alkamatu Nasiru da Shahidu Ibrahim, dukansu ‘yan kauyen Yan Matankari ne a karamar hukumar Anka ta jihar Zamfara.

Masu safarar makamai sun shiga hannu

Bayan bincike, an same su sanye da rigunan kariya masu kama da na sojoji a karkashin kayan jikinsu, tare da wukake biyu a hannunsu.

“Wadanda ake zargin sun amsa cewa suna kan hanyarsu ta karbar bindigogin AK-47 ne domin kai su ga Abdul Baleri, wani sanannen jagoran ‘yan bindiga da ke aikata ta’addanci a jihar Zamfara."

- Wata majiya

Kara karanta wannan

'Dan bindiga da ya hana Turji, yaransa sakewa ya mutu, an kashe shi wurin sulhu

A halin yanzu, ana ci gaba da bincike domin gano tushen makaman, tare da bankado sauran mutanen da ke da hannu a haramtacciyar harkar safarar makamai.

Jami'an tsaro sun cafke masu safarar makamai a Sokoto
Taswirar jihar Sokoto, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Karanta wasu labaran kan 'yan bindiga

'Yan bindiga sun kafa sharudda a Kaduna

A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga sun kafa sharuddan da suke so a cika musu kafin su saki masu ibada a coci da suka yi garkuwa da su a jihar Kaduna.

Mai unguwar kauyen da lamarin ya auku, ya bayyana cewa ’yan bindigan da suka sace kusan masu ibada 177 sun buƙaci a biya Naira miliyan 250 tare da babura 20 domin sakin su.

Jami'an tsaro sun gano inda aka kai mutanen da aka sace, amma ’yan bindigan na amfani da su a matsayin garkuwa domin hana kai hare-haren sama kan sansaninsu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng