Maganar Cire Shugaban INEC Ta Girma, CAN Ta Ƙalubalanci Majalisar Shari'ar Musulunci

Maganar Cire Shugaban INEC Ta Girma, CAN Ta Ƙalubalanci Majalisar Shari'ar Musulunci

  • Kungiyar CAN ta Arewa ta soki kiran cire Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, tana cewa ƙoƙari ne na siyasantar da addini
  • CAN ta gargadi cewa amfani da addini wajen sukar jami’an gwamnati abu ne mai hatsari, yana iya tayar da rikicin addini da barazana ga haɗin kai
  • Shugabannin Kiristocin sun bukaci a duba kwarewa da nagarta maimakon addini, tana kira ga Amupitan ya mayar da hankali kan zaɓe adalci

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) a jihohi 19 na Arewa da Abuja ta yi martani ga Musulmi da ke kiran cire shugaban INEC.

CAN ta ki amincewa da kiran cire Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan saboda wasu zarge-zarge na bambancin addini.

An kaure da cacar baki tsakanin Kirista da Musulmi kan shugaban INEC
Shugaban hukumar INEC, Joash Amupitan. Hoto: INEC Nigeria.
Source: Twitter

INEC: CAN ta gargadi saka addini a siyasa

Kara karanta wannan

Musulmai za su ki yarda da zaben Najeriya sai an sauke shugaban INEC

A sanarwar da shugabannin CAN na Arewa suka fitar, sun tambayi wanda ke daukar nauyin kiran da dalilin amfani da dandamalin addini, cewar Vanguard.

CAN ta ce kiran da Majalisar Shari’a ta Musulunci ta yi yunƙuri ne na siyasantar da addini da kuma raunana muhimmiyar hukuma ta ƙasa.

A baya, Majalisar Shari’a ta nemi a cire shi tare da gurfanar da Shugaban INEC, tana danganta hakan da wata takardar shari’a da ta shafi Kiristoci.

Kungiyar CAN ta gargadi cewa amfani da addini wajen tantance amincin jami’an gwamnati na iya tayar da rikice-rikicen addini a ƙasa.

CAN ta ce Farfesa Amupitan na da ‘yancin bin addininsa kamar kowane ɗan Najeriya, kuma hakan ba hujjar nuna son kai ba.

Kungiyar ta tuna cewa Musulmai da dama sun rike manyan mukamai duk da alaƙarsu da addini, ba tare da irin wannan suka ba.

An taso shugaban INEC a gaba kan kujerarsa
Sabon shugaban INEC, Joash Amupitan. Hoto: INEC Nigeria.
Source: Twitter

Yabon da CAN ta yi wa Bola Tinubu

CAN ta ce ce-ce-ku-cen na kara nuna koke-koken wariyar addini ga Kiristoci, musamman wajen nada mutane a muhimman mukamai.

Kungiyar ta yabawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan nada Kirista a matsayin Shugaban INEC, tana cewa hakan alama ce ta haɗin kai.

Kara karanta wannan

Akpabio ya saɓa da kwamitin majalisa, ya kare Tinubu kan zargin cushe a dokokin haraji

CAN ta bukaci Majalisar Shari’a ta bayyana wadanda ke bayan wannan kamfen, tana gargadin kada a rika boye siyasa da sunan addini.

Kungiyar ta shawarci Farfesa Amupitan da kada ya bari ce-ce-ku-cen ya dauke masa hankali daga aikinsa na shirya zaɓe nagari.

CAN ta kuma gargadi cewa jefa siyasa cikin addini gabanin zaɓen 2027 na iya raba kan ‘yan Najeriya da barazana ga haɗin kai, cewar The Guardian.

Tinubu ya ware N1tr saboda zaben 2027

Mun ba ku labarin cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ware sama da Naira tiriliyan 1 ga hukumar INEC a kasafin kuɗin 2026 domin fara shirin babban zaɓen 2027.

Kasafin kudin ya nuna an yi tanadin kuɗin tun da wuri, abin da INEC ta dade tana nema domin samun cikakkiyar damar gudanar da zaɓe.

Rahotanni sun nuna cewa dokar zaɓen Najeriya ta 2022 ta wajabta sakin kuɗin zaɓe ga INEC akalla shekara guda kafin babban zaɓe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.