'Yan Najeriya na cikin Alheri, Sun Fara Cewa Arahar Abinci Ta Yi Yawa a Mulkin Tinubu'
- Sanata Adams Oshiomhole ya bayyana cewa arahar abinci ta fara yi wa 'yan Najeriya yawa saboda matakan da Shugaba Tinubu ya dauka
- Oshiomhole, mai wakiltar yankin Edo ta Arewa a Majalisar dattawa, ya yi ikirarin cewa su kansu yan Najeriya sun fara fadin sauki ya yi yawa
- Sai dai jam'iyyar ADC ta ce wannan sauki ba alheri ba ne domin ya kashe manoma, wadanda suka saye takin zamani da tsada lokacin damina
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Sanata mai wakiltar mazabar Edo ta Arewa, Adams Oshiomhole, ya bayyana cewa wasu 'yan Najeriya na nuna cewa farashin abinci ya fara yin arha da yawa.
Oshiomhole, tsohon gwamnan jihar Edo ya yi ikirarin cewa farashin abinci ya sauka ne sakamakon tsare-tsaren da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta bullo da su.

Kara karanta wannan
'Waye ya ce ka yi': Gwamna Fintiri ya hasala da aka yi masa ihun 'ba mu yi' a Adamawa

Source: Facebook
Adams Oshiomhole ya ce abinci ya yi araha
Sanata Oshiomhole ya fadi hakan ne yayin wata tattaunawa da tashar Channels TV ta yi da shi a makon da ya gabata.
“Gaskiyar ita ce, mun yi alkawarin kawo sauye-sauye masu amfani. Kuma a yanzu akwai 'yan Najeriya da ke cewa abinci ya fara yin araha da yawa,” in ji shi.
Da aka tambaye shi ko da wace nasara Shugaba Bola Tinubu zai yi yakin neman tazarce a 2027, tsohon gwamnan na Edo ya ce sauye-sauyen gwamnatin sun fara haifar da sakamako mai kyau.
Sanatan APC ya caccaki 'yan adawa
Oshiomhole ya ce ya ji wasu jagororin jam’iyyun hamayya su na zargin shugaban kasa da yin amfani da dabarun siyasa wajen fado da farashin abinci da karfi.
"Don haka suna fushi ne saboda farashin abinci ya sauka, wanda ba haka suka so ba," in ji shi.
Sanatan ya nuna goyon bayansa ga sababbin dokokin haraji na shugaban kasa, inda ya bayyana su a matsayin "tsari na cigaba" wanda ya dora nauyi ga masu kudi, sannan ya saukaka wa talakawa ko ma ya yafe musu harajin.
ADC ta maida martani kan arahar abinci
Da take maida martani kan lamarin, jam’iyyar ADC ta zargi gwamnatin Tinubu da yin amfani da farashin abinci domin neman farin jini gabanin zaben 2027.
Sakataren yada labarai na ADC, Bolaji Abdullahi, ya bayyana cewa raguwar farashin abincin da aka gani a baya-bayan nan a Najeriya, na bogi ne.

Source: Getty Images
Ya ce hakan ya faru ne saboda dage harajin shigo da abinci daga waje, wanda ya sa kasuwanni suka cika da abincin kasashen waje mai arha, cewar rahoton The Cable.
Ya ce shigo da abinci daga waje da sauke farashinsa ba alheri bane domin yana cutar da manoman gida da ke fama da tsadar kayan noma da rashin tsaro.
An nemi Tinubu ya rufe iyakokin Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa an fara neman Gwamnatin tarayya karkashin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta dakatar da shigo da shinkafa daga kasashen ketare.
An ji kwamitin tsara manufofin harkar noma da gwamnatin tarayya ke marawa baya ya ba da shawarar rufe dukkan kofofin shigo da shinkafa a hukumance.
Kwamitin ya dogara ne da raguwar hauhawar farashin abinci da hujjojin da ke nuna cewa yawaitar shinkafa a Najeriya ta samo asali ne daga yawan shigo da ita daga waje.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
