Sheikh Gumi Ya Gargaɗi Amurka, Isra'ila kan Ƙoƙarin Raba Najeriya? Gaskiya Ta Fito

Sheikh Gumi Ya Gargaɗi Amurka, Isra'ila kan Ƙoƙarin Raba Najeriya? Gaskiya Ta Fito

  • An yi ta yada wasu rahotanni game da Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi bayan Amurka ta kawo hari a Najeriya
  • Rahoton ya ce Sheikh Gumi ya gargadi Amurka da Isra’ila kan raba Najeriya, inda aka gano cewa babu wata hujja da ke tabbatar da hakan
  • A labarin wai Gumi ya fadi haka ne bayan harin da aka kawo Sokoto da aka ce ikirarin ya bazu ne a shafukan sadarwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kaduna - A kwanakin baya, Amurka ta kawo hari a jihar Sokoto da Kwara kan yan ta'adda da ke kai hare-hare.

An yi ikirarin cewa fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya gargadi Amurka da Isra’ila kan raba Najeriya.

An karyata rahoton gargadin Gumi ga Amurka da Isra'ila
Shugaba Donald Trump da Sheikh Ahmad Mahmud Gumi. Hoto: Donald J Trump, Dr. Ahmad Mahmud Gumi.
Source: Facebook

Bincike kan rahoton cewa Gumi ya gargadi Amurka

Sai dai wani bincike da shafin Dubawa ya yi, ya duba gaskiyar lamarin da kuma kalaman da ake danganta wa ga Sheikh Gumi.

Kara karanta wannan

Amurka ta tsananta barazana, ta tura tankokin yaki zuwa Iran

Ikirarin ya nuna cewa Gumi ya ce duk wani yunkuri na raba Najeriya zai haifar da korar Fulani, kuma za a fuskanci turjiya mai tsanani daga gare su.

An tabbatar da cewa labarin yaudara ne, domin babu wata hujja da ke nuna Sheikh Gumi ya taba ambaton Isra’ila ko shirin raba Najeriya.

Yadda aka yada rahoton karya a kafofin sadarwa

Bayan harin sama da Amurka ta kai a Sokoto ranar 25 ga Disamba, 2025, Sheikh Gumi ya zama sanadin kirkirar labaran bogi daga masu rubuce-rubuce a kafofin sadarwa.

A ranar 27 ga Janairu, 2025, wani rubutu ya bayyana a Facebook yana cewa Gumi ya zargi Amurka da Isra’ila da shirin ‘yantar da Biafra da raba Najeriya.

Wasu masu amfani da kafafen sada zumunta sun yarda da ikirarin, yayin da wasu suka nuna shakku, suna tambayar inda aka samo kalaman da ake jingina masa.

An ƙaryata labarin cewa Gumi ya gargadi Amurka da Isra'ila
Malamin Musulunci a Najeriya, Sheikh Ahmad Mahmud Gumi. Hoto: Dr. Ahmad Mahmud Gumi.
Source: Facebook

Yadda Gumi ya soki hadin guiwa da Amurka

An bincika kafafen yada labarai da shafin Facebook na Sheikh Gumi, amma ba a samu wata shaida da ke goyon bayan ikirarin ba duk da yana yawan magana kan tsaro.

Kara karanta wannan

Ta'addanci: Kotu ta yi hukunci da Nnamdi ke neman ɗauke shi a gidan yarin Sokoto

Ko da yake Gumi ya soki hadin gwiwar soji da Amurka, yana ba da shawarar a nemi kasashe masu zaman kansu, bai taba maganar raba Najeriya ba.

Binciken ya kammala da cewa babu wata hujja da ke nuna Sheikh Gumi ya yi barazana ga Amurka da Isra’ila kan zargin raba Najeriya ko korar Fulani.

Ministan tsaro ya gargadi Sheikh Ahmad Gumi

Mun ba ku labarin cewa Ministan tsaro, Janar Christopher Musa mai ritaya, ya gargadi Sheikh Ahmed Gumi da duk masu nuna goyon baya ga ‘yan ta’adda da ‘yan fashin daji.

Janar Christopher Musa ya bayyana cewa abokin barawo, barawo ne kuma ba za a sassauta wa duk wanda ya ke ci gaba da goyon bayan 'yan ta'adda ba.

Ya bayyana cewa addini, kabila ko yanki ba shi da alaka da aikin ta'addanci da wasu ke da shi na ta'addanci da jawo asarar rayuka a sassan Najeriya gaba daya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.