Gwamnatin Kasar Turkiyya Ta Yi Magana kan Tuntuben da Shugaba Tinubu Ya Yi
- Gwamnatin Turkiyya ta yi mamakin yadda labarin tuntuben da Bola Tinubu ya yi a kasar ya dauki hankali a kafafen yada labaran Najeriya
- Shugabar hukumar NIDCOM, Abike Dabiri-Erewa ta ce wasu jami'an Turkiyya sun dauki yadda ake yada labarin a matsayin shashanci da neman rigima
- Fadar shugaban kasa dai ta ce Shugaba Tinubu ya ci gaba da harkokin da suka kai shi kasar Turkiyya kamar yadda aka tsara bayan tuntuben
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Ankara, Turkey - Gwamnatin kasar Turkiyya ba ta dauki 'dan karamin tuntuben da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi a kasar, a matsayin wani babban abin damuwa ba.
Shugabar hukumar kula da 'yan Najeriya mazauna kasashen waje (NIDCOM), Abike Dabiri-Erewa, ce ta bayyana hakan yayin da take martani kan ce-ce-ku-cen da ake yi kan lamarin.

Kara karanta wannan
Gwamna Abba ya shiga APC da kafar dama, ya kara samun karbuwa daga masoyan Tinubu

Source: Twitter
Abin da Turkiyya ta ce kan tuntuben Tinubu
Ta bayyana cewa jami’an kasar Turkiyya sun siffanta dan tuntuben Tinubu ya yi a lokacin ziyararsa a matsayin “marar muhimmanci,” kamar yadda Tribune Nigeria ta kawo.
Shugabar NIDCOM ta ce jami'an gwamnatin Turkiyya sun nuna mamakin yadda lamarin ya dauki hankali a kafafen yada labaran Najeriya.
Dabiri-Erewa, wadda ke cikin tawagar shugaban kasa, ta mayar da martani ne a ranar Laraba ga wani rubutu da wani mai amfani da kafar sadarwa ta X, Oguntoye Opeyemi, ya yi.
“Haka yake. A nan birnin Ankara, jami’ansu sun yi mamakin jin cewa wannan ya zama babban abin magana a kafafan yada labarai da shafukan yanar gizo na Najeriya,” in ji ta.
A cewar Dabiri-Erewa, daya daga cikin jami’an Turkiyyan ma ya ayyana surutun da ake yi kan lamarin a matsayin “shashanci da neman rigima,” tana mai jaddada cewa ita kanta ziyarar Tinubu ana ta murnar ta a fadin kasar Turkiyya.
Kafafen yada labaran Turkiyya sun yi shiru
A nasa bangaren, Opeyemi ya lura cewa babu wata babbar kafar yada labarai ta Turkiyya da ta ruwaito abin da ya faru.
“Babu ko tasha daya ta talabijin a Turkiyya da ta nuna dan zamiyar da Shugaban ya yi domin ba wani abu ba ne. Amma talabijin na Najeriya da jaridun kasa sun maida shi babban labari,” in ji shi.

Source: Twitter
Kafin nan Legit Hausa ta ruwaito cewa Shugaba Tinubu ya dan yi tuntube ne yayin wani taron faretin maraba da aka shirya masa a Ankara, babban birnin Turkiyya.
Tun bayan faruwar hakan, ya ci gaba da gudanar da ayyukansa kamar yadda aka tsara, ciki har da tattaunawa da Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdoğan.
Abin da ya faru da Tinubu a Turkiyya
A baya, kun ji cewa Fadar shugaban kasa ta yi bayanin abin da ya faru da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a taron maraba da aka shirya masa a Turkiyya.
Fadar ta ce Tinubu ya dan rasa daidaito na dan lokaci a ranar Talatabayan ya taka wani karfe a lokacin ziyarar aiki da yake gudanarwa a birnin Ankara, Turkiyya.
Fadar Shugaban Kasar ta bukaci jama’a da su yi watsi da duk wani yunkuri na rura wutar labarin ko sanya tsoro, inda ta sake jaddada cewa Tinubu bai fadi ba kuma yana cikin koshin lafiya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

