Solar: Gwamnati Ta Ware N7bn don Samar da Wuta Ta Hasken Rana a Fadar Shugaban Kasa
- Gwamnatin Tarayya ta ware N7bn domin ci gaba da aikin sanya wutar lantarki ta hasken rana a Fadar Shugaban Ƙasa
- Kasafin kuɗin 2026 ya nuna an ƙara yawan kudi sosai ga ɓangaren wutar lantarki, inda aka ware sama da Naira tiriliyan 1.1
- Wadannan bayanai na fito wa ne a lokacin da Najeriya ke fama da matsalolin wutar da lalacewar turakun samar da wutar lantarki
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ware N7bn domin aikin da ake ci gaba da yi na sanya wutar lantarki ta hasken rana a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.
Ana daukar wannan mataki ne a ƙoƙarin magance matsalar ƙarancin wutar lantarki da ta daɗe tana addabar ƙasar nan.

Source: UGC
Jaridar Punch ta wallafa cewa an bayyana ware kuɗin ne a cikin Kundin Kasafin Kuɗin 2026 da gwamnatin ta miƙa wa Majalisar Ƙasa a watan Disamba, 2025.
Kasafin wutar lantarkin gwamnati a 2026
The Cable Darakta Janar na hukumar samar da wutar lanarki, Abba Aliyu, ya ce Najeriya ce ke da mafi yawan mutanen da ba su da wutar lantarki a duniya.
Ya bayyana cewa sama da mutane miliyan 82 ke rayuwa a yankunan da ba su da ko kuma ke samun wuta kaɗan.

Source: Facebook
Jimlatan, gwamnatin tarayya ta ware sama da Naira tiriliyan 1.1 ga ɓangaren wutar lantarki a 2026, fiye da N900bn da aka ware a 2025.
Duk da haka, masu ruwa da tsaki sun nuna damuwa cewa babu tanadin kuɗi kai tsaye domin tallafin farashin lantarki, wanda ake hasashen ya kai kusan N200bn a kowane wata.
Yadda aka ware kudin 'solar' a kasafin kudi
A shekarar da ta gabata, an ware Naira biliyan 10 domin irin wannan aiki a kasafin kuɗin 2025 kuma har mutane suka yi ta surutu a kai.
Ana sa ran hakan zai rage kuɗin makamashi, musamman ta rage dogaro da janareto masu amfani da dizal.
Sai dai a 2025, matakin ya jawo suka daga jama’a bayan bayyanar rahotannin ware N10bn domin aikin samar da hasken wutar lantarki a Fadar Aso Rock.
Duk da haka, Darakta Janar na Hukumar Makamashi ta Najeriya, Mustapha Abdullahi, ya kare aikin, yana mai cewa ba za a iya ci gaba da biyan kuɗin lantarki na kusan Naira biliyan 47 a duk shekara ba.
Ya ce shigar da tsarin samar da wutar lantarki daga hasken rana zai samar da tsaftatacciyar wuta ba tare da katsewa ba, tare da rage nauyi a kan turakun wuta.
Za a dawo da sola Fadar gidan gwamnati
A baya, mun wallafa cewa gwamnatin tarayya ta amince da ware zunzurutun kudi N10bn a cikin kasafin kudin 2025 domin samar da wutar sola a fadar shugaban kasa da ke Aso Rock, Abuja.
Rahotanni sun bayyana cewa karin kudi a kasafin fadar shugaban kasa daga N47.11bn zuwa N57.11bn ya samo asali ne saboda samar da wutar sola da ake shirin yi.
Shirin zai taimaka wajen takaita kashe kudin lantarki da gwamnati ke yi, musamman duba da cewa kudin lantarki ga masu amfani da layin Band A ya tashi tun shekarar 2024.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

