Musulmai za Su Ki Yarda da Zaben Najeriya sai An Sauke Shugaban INEC

Musulmai za Su Ki Yarda da Zaben Najeriya sai An Sauke Shugaban INEC

  • Majalisar Shari’a ta Najeriya ta sake nuna rashin amincewa da shugaban hukumar INEC, tana mai cewa halayensa na iya lalata amincewar jama’a da zaɓen 2027
  • Majalisar ta yi gargaɗin cewa Musulmi ba za su amince da duk wani zaɓe da aka gudanar ƙarƙashin jagorancinsa ba, bisa dalilan da ta ce sun shafi rashin adalci da gaskiya
  • Wannan matsaya ta fito ne a wani taron addini da aka gudanar a Abuja, inda manyan baki suka yi tsokaci kan makomar Najeriya da haɗin kan kasa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Majalisar Koli ta Shari’a a Najeriya ta sake kira a cire shugaban INEC, Joash Amupitan, tana mai bayyana shi a matsayin barazana ga sahihanci da amincewar tsarin dimokuraɗiyyar Najeriya gabanin zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

Akpabio ya saɓa da kwamitin majalisa, ya kare Tinubu kan zargin cushe a dokokin haraji

Majalisar ta ce duk wani zaɓe da aka gudanar a ƙarƙashin shugabancinsa ba zai samu amincewa daga al’ummar Musulmi ba, bisa zargin cewa halayensa da ra’ayoyinsa na baya sun nuna rashin adalci da nuna bangaranci.

Shugaban INEC da Sheikh Bashir Aliyu Umar
Shugaban INEC a hagu, taron majalisar Shari'a a tsakiya, Sheikh Bashir Aliyu Umar a dama. Hoto: Plateau State Government|Aminu Sani Jaji|Dr Bashir Aliyu Umar
Source: Facebook

Daily Trust ta rahoto cewa shugaban Majalisar Koli ta Shari’a a Najeriya, Sheikh Bashir Aliyu Umar, ne ya bayyana hakan yayin jawabi a taro kan Ramadan da babban taron majalisar na shekarar 2026 da aka gudanar a Abuja.

Dalilan kiran a cire shugaban INEC

Sheikh Bashir Umar ya ce wannan ba shi ne karo na farko da Majalisar ke bayyana irin wannan matsaya ba, yana mai jaddada cewa abin da ya sa suke dagewa shi tarihin ayyukan shugaban INEC da ke haifar da shakku kan adalcinsa.

Ya ce akwai wani rubutaccen bayanin da ake dangantawa da Amupitan, wanda a cikinsa aka yi ƙoƙarin nuna cewa ana aiwatar da kisan kare dangi ga Kiristoci a Najeriya, ikirarin da Gwamnatin Tarayya ta sha musantawa.

A cewarsa, irin wannan matsaya ta saba da abin da ake tsammani daga shugaban hukumar zaɓe, domin wanda ke jagorantar zaɓe dole ne ya kasance mai cikakken adalci da rashin nuna son rai.

Kara karanta wannan

An gano jiha 1 da Tinubu zai iya amincewa a kirkira a Najeriya

Musulmi ba za su yarda da zabe ba

Shugaban Majalisar ya bayyana cewa daga mahangar su, mutunci da gaskiyar shugaban INEC sun riga sun samu matsala, don haka ya kamata ya yi murabus cikin mutunci ko kuma gwamnati ta ɗauki matakin cire shi daga muƙamin.

Ya ƙara da cewa Musulmi ba za su yarda da sakamakon duk wani zaɓe da mutum mai irin wannan tarihin ya jagoranta ba, yana mai jaddada cewa bai kamata a yi wasa da sahihancin dimokuraɗiyya ba.

Rahoton Arise News ya nuna cewa majalisar ta bayyana cewa ta san cewa wasu ƙungiyoyi sun riga sun garzaya kotu domin ƙalubalantar ci gaba da riƙe muƙamin shugaban INEC.

Shugaban hukumar INEC, Farfesa Joash Amupitan
Shugaban INEC, Joash Amupitan na bayani ga jami'an hukumar zabe. Hoto: INEC Nigeria.
Source: Twitter

Wasu abubuwan da aka tattauna a taron

Baya ga batun zaɓe, Majalisar Koli ta Shari’a ta kuma nuna damuwa kan matsalar tsaro, tsadar rayuwa, matsalar aiwatar da kasafin kuɗi, da abin da ta kira rashin daidaito wajen naɗa mukamai a matakin tarayya.

Haka kuma, majalisar ta ƙi amincewa da labaran da ke cewa ana kisan kare dangi ga Kiristoci a Najeriya, tana mai gargadin cewa irin ikirarin na iya rarraba al’umma da barazana ga haɗin kan ƙasa.

Kara karanta wannan

Akwai kura: Hannatu Musawa ta yi gargadi kan ajiye Kashim Shettima a 2027

Ra’ayoyin baki a taron majalisar Shari'a

Da yake jawabi a taron, Shugaban Kwamitin Majalisar Wakilai kan Muhalli, Aminu Sani Jaji, ya ce lokaci da taken taron sun dace da halin da ƙasar ke ciki, yana mai kira da a yi hattara wajen yaɗa bayanan da ba a tantance ba.

Shi ma shugaban taron, Madakin Zazzau, Malam Muhammadu Munir Ja’afaru, ya ce Majalisar Koli ta Shari’a ta dade tana taka rawa wajen kare muradun al’ummar Musulmi da inganta zaman lafiya, adalci da haɗin kan Najeriya ta hanyar tattaunawa mai ma’ana.

Izala ta tura malamai tafsirin Ramadan

A wani labarin, kun ji cewa kungiyar Izala mai hedkwata a birninJos na jihar Filato ta tura malamai tafsirin Ramadan da za a yi a shekarar 2026.

Shugaban malaman kungiyar, Sheikh Sani Yahaya Jingir zai yi tafsir a jihar Filato yayin da mataimakinsa, Sheikh Yusuf Sambo zai yi a Kaduna.

Izala ta sanar da cewa ta tura malamai sama da 100 yankuna daban-daban na Najeriya tare da wasu ƙasashen Afrika da sauransu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng