Ana Batun Komawar Abba APC, An Kama Wanda Zai bada Shaida Mai Karfi a Shari'ar Ganduje
- 'Yan sanda sun cafke wanda ya amince zai ba da shaida a shari'ar tsohon shugaban APC, Abdullahi Ganduje da gwamnatin jihar Kano
- Rahoto ya nuna cewa jami'an tsaro sun cafke shaidar mai suna Ahmad Rabiu a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano yau Laraba
- Gwamnatin Kano ta maka Ganduje da wasu mutane a gaban kotu ne kan badakalar mallakar tashar tsandauri ta Dala
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Rahotannin da muka samu yanzu haka sun nuna cewa an kama Ahmad Rabiu, wanda ya ahirya ba da shaida a shari’ar tsohon shugaban APC na kasa, Abdullahi Ganduje.
Wanda aka kama shi ne babbar shaida a takaddamar mallakar tashar jirgin ruwa ta biliyoyin Naira da ta shafi tsohon gwamnan jihar Kano, Ganduje

Source: Facebook
Jaridar Premium Times ta tattaro cewa an kama shaidar ne a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano ranar Laraba.
Yan sanda sun kama shaidar gwamnatin Kano
Jami’an ‘yan sanda sanye da kayan gida daga rundunar ‘yan sandan jihar Kano ne suka kama Ahmad Rabiu a filin jirgin sama, a cewar mataimakinsa, Hanif Umar, wanda ya tattauna da manema labarai.
Dakarun tsaron sun tare Ahmed Rabiu ne a lokacin da yake shirin shiga jirgin kamfanin Air Peace da zai nufi babban birnin tarayya, Abuja.
A lokacin da aka kama shi, yana tare da Aminu Dabo, fitaccen dan siyasar Kano kuma tsohon shugaban hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa ta Najeriya (NPA).
Ahmad Rabiu, a cikin wata sanarwa da ya aika wa lauyoyinsa, ya yi zargin cewa ana barazanar kashe shi bayan ya amince zai ba da shaida a gaban Kotun Jiha a shari’ar gwamnatin Kano da Ganduje.
Ganduje ya kalubalanci gwamnatin Kano
A ranar 14 ga watan Janairu, Ganduje ya shigar da korafi yana kalubalantar yadda aka mika masa takardun shigar da kara gaban kotu.
Lauyan Ganduje, A.S. Gadanya (SAN), ya ki amincewa da bukatar gwamnatin jiha na neman a bayar da sammacin kamo Ganduje saboda rashin halartar kotu da kansa.
Da yake martani kan kama Ahmad Rabiu, tsohon shugaban hukumar yaki da rashawa ta Kano, Muhuyi Magaji, ya bayyana cewa an yi hakan ne domin a kawo cikas ga shari’ar da ake gudanarwa.

Source: Facebook
Abubuwan da ake zargin Ganduje
Gwamnatin Kano ta zargi Ganduje da wasu da kulla makircin tura kashi 80% na hannun jarin tashar jirgin ruwan ta Dala, ciki har da kashi 20% na jihar, zuwa ga wasu mutane a karkashin sunan bogi na kamfanin “City Green Enterprise”.
Haka kuma, ana zarginsu da karkatar da sama da N4.49bn na kudaden jihar Kano wajen yin ayyukan more rayuwa kamar tituna, wutar lantarki, da katangar tashar, domin amfanin kansu da iyalansu.
An samu tsaiko a shari'ar Ganduje
A wani rahoton, kun ji cewa Babbar Kotun Kano ta dage shari’ar tsohon shugaban APC, Dr. Abdullahi Ganduje da wasu mutum bakwai zuwa 3 ga Fabrairu, 2026.
Lokacin da aka dawo zaman shari’ar a watan Nuwamba, 2025 lauyan gwamnatin Kano, Jedidiah Akpata ya shaida wa kotu cewa ba su shirya ci gaba da zaman ba.
Alkalin kotun, Mai Shari'a Amina Adamu-Aliyu ta amince da buƙatar ƙarin lokaci da gwamnati ta nema sannan ta dage shari’ar zuwa 3 ga Fabrairu, 2026.
Asali: Legit.ng


