'Yan Bindiga Sun Yi Wa 'Yan Sanda Kwanton Bauna a Katsina, An Samu Asarar Rayuka
- 'Yan bindiga dauke da makamai sun yi wa jami'an 'yan sanda masu aikin samar da tsaro kwanton bauna a jihar Katsina
- Tsagerun 'yan bindigan sun shirya kwanton baunan ne lokacin da jami'an 'yan sandan ke gudanar da sintiri na yau da kullum
- Harin na 'yan bindigan ya jawo asarar rayukan 'yan sanda tare da raunata wasu daga cikinsu bayan an yi musayar wuta tsakanin bangarorin biyu
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Katsina - 'Yan bindiga dauke da makamai sun kai wani harin kwanton bauna kan jami'an 'yan sanda a jihar Katsina.
Harin da 'yan bindigan suka kai a kan hanyar Guga-Bakori ya jawo 'yan sandan Najeriya huɗu sun rasa rayukansu, yayin da wasu biyu suka jikkata.

Source: Facebook
Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.

Kara karanta wannan
Shiri ya baci: 'Yan Boko Haram sun kashe sojoji, sun cafke wani babban soja a Borno
'Yan bindiga sun farmaki 'yan sanda a Katsina
Majiyoyi sun bayyana cewa harin ya faru ne a ranar Talata, 27 ga Janairun 2026 da misalin karfe 12:45 na rana.
'Yan bindigan sun kai farmakin ne kan jami’an rundunar ’yan sandan Mobile Force (PMF) 27 daga sansanin Guga, a lokacin da suke sintiri na yau da kullum.
A cewar majiyar, direban motar sintirin ya rasa ikon sarrafa ta ne bayan da aka soma harbe-harbe, lamarin da ya sa motar ta kife a gefen hanya.
Jami’an da suka mutu nan take sun haɗa da UC ASP Abubakar Abdullahi, Insp. Umar Ahmed, da Sajan Kailani Kabir.
An sace makaman 'yan sanda
Majiyar ta kara da cewa maharan sun kwace makaman jami’an da suka haɗa da bindigar AK-47 mai harsasai 30, bindigar Tokarev mai harsasai takwas, da kuma bindigar harbi daga nesa.
Wasu jami’ai biyu sun jikkata a harin; Cpl. Daniel Japet ya samu karaya, yayin da Cpl. Abdulaziz Sani ya samu raunin harbin bindiga.
An gaggauta kai dauki
Kwamandan yankin Funtua ya gaggauta tura tawagar haɗin gwiwar jami’an ’yan sanda tare da sojojin Operation FANSAN YANMA zuwa wurin da lamarin ya faru.

Source: Original
An garzaya da gawarwakin da kuma waɗanda suka jikkata zuwa babban asibitin Funtua domin duba gawarwaki da kuma kula da lafiyar masu dauke da rauni.
Hukumomin tsaro sun rufe dukkan hanyoyin fita da ake zargi ’yan bindigan za su bi, tare da fara ayyukan bincike domin kama maharan da kuma kwato makaman da aka sace.
'Yan bindiga sun kai hare-hare a Katsina
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun kashe mutane bayan sun kai wasu hare-haren ta'addanci a jihar Katsina.
'Yan bindigan sun kai hare-haren ne a wasu kauyuka na karamar hukumar Dandume ta jihar Katsina, inda suka hallaka akalla mutane tara da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba.
Shaidun ganau ba jiyau ba sun ce ’yan bindigan sun shiga kauyukan ne cikin duhun dare, suna harbe-harbe ba kakkautawa, lamarin da ya jefa jama’a cikin firgici.
Asali: Legit.ng
