Rundunar Sojojin Najeriya Ta Yi Magana kan Kuskuren Jefawa Mutane Bama Bamai a Neja

Rundunar Sojojin Najeriya Ta Yi Magana kan Kuskuren Jefawa Mutane Bama Bamai a Neja

  • Rundunar sojin saman Najeriya ta fara gudanar da bincike kan zargin kuskuren jefa bama-bamai kan fararen hula a jihar Neja
  • Wasu rahotanni sun nuna cewa jirgin sojoji ya kai hari bisa kuskure, inda ya kashe manoma a yankin karamar hukumar Mariga
  • Mai magana da yawun sojojin saman Najeriya ya jajantawa iyalan wadanda aka ruwaito sun rasa rayukansu da wadanda suka jikkata

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Niger, Nigeria - Rundunar Sojin Saman Najeriya (NAF) ta kaddamar da bincike na gaggawa kan zargin kashe fararen hula yayin wasu hare-haren sama da jiragenta suka kai a jihar Neja.

Ana dai zargin jirgin sojojin Najeriya ya yi kuskuren jefa dama-bamai kan bayin Allah da ba su ji ba kuma ba su gani ba ranar 25 ga watan Janairu a kauyen Kurigi da ke Karamar Hukumar Mariga a Jihar Neja.

Kara karanta wannan

'Dan bindiga da ya hana Turji, yaransa sakewa ya mutu, an kashe shi wurin sulhu

Jirgin sojojin Najeriya.
Jirgin yaki na rundunar sojojin saman Najeriya a bakin aiki Hoto: @NigAirForce
Source: Twitter

Sojojin sama sun fara bincike

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa a martaninta na farko bayan bullar labarin, rundunar sojin ta fara gudanar da bincike, wanda za a yi bude domin gano hakikanin abin da ya faru.

Darakta a bangaren yada labarai na rundunar NAF, Air Commodore Ehimen Ejodame, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba.

Ya ce tawagar bincike kan hadurran da suka shafi fararen hula (CHAI) ta rundunar sojojin saman Najeriya ce za ta gudanar da binciken.

A cewarsa, rundunar ta dauki alhakin labarin asarar rayuka da raunuka da aka ruwaito, sannan ta nuna damuwarta ga dukkan wadanda lamarin ya shafa.

Abin da rundunar sojojin sama ta fada

Ya sake jaddada cewa kiyaye rayukan 'yan Najeriya shi ne babban ginshiki a ayyukansu na soja, kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Ejodame ya ce:

“A shekarar da ta gabata, rundunar NAF ta ci gaba da kokarin aiwatar da shirinta na rage radadi da bayar da agaji ga fararen hula (CHMR-AP).

Kara karanta wannan

Juyin mulki: Yadda Kanal na soja ya tsara kifar da Gwamnatin Bola Tinubu

"Kuma NAF ta sanya batun kariya ga fararen hula a dukkan matakai na ayyukanta a sahun gaba, tana karfafa horo, ka’idoji, da matakan kariya da nufin rage cutarwa a hare-haren sama.
“Dangane da wannan batu, rundunar sojojin sama ta kaddamar tawagar bincike kan hadurran da suka shafi fararen hula (CHAI) domin fara bincike na gaggawa kuma dalla-dalla kan lamarin da aka ruwaito.”
Jihar Neja.
Taswirar jihar Neja da ke Arewacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Yadda sojoji ke kiyaye doka a ayyykansu

Kakakin sojojin sama ya nanata cewa rundunar tana tafiya ne bisa ka'idojin da doka ta shinfida, nauyin da ya rataya a wuyanta, da kuma kwatanta gaskiya.

Ya bayar da tabbacin cewa rundunar NAF ta kuduri qniyar “daukar alhakin abin da ya faru, aiwatar da gyare-gyaren da suka dace, da kuma kare rayukan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba."

Sojojin sama sun kashe yan ta'adda a Borno

A wani labarin, kun ji cewa dakarun sojojin saman Najeriya sun nuna bajinta a ci gaba da kokarin da suke na samar da tsaro a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya.

Sojojin sun yi nasarar rugurguza maboyar ‘yan ta’adda tare da kashe da dama daga cikinsu a yankunan bakin ruwa na karamar hukumar Kukawa da ke jihar Borno.

Majiyoyi sun bayyana cewa sojoji sun kai hare-haren ne bayan tsawon makonni na tattara sahihan bayanan sirri da yin bincike, wanda ya tabbatar da karuwar zirga-zirga 'yan ta'adda.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262