An Yi Rashi: Babban Mai Rike da Sarauta Kuma Surukin Tsohon Gwamna a Najeriya Ya Rasu
- An yi rashi na wani babban mai rike da sarauta a jihar Legas wanda ya yi bankwana da duniya a ranar Laraba, 28 ga watan Janairun 2026
- Otunba na Legas kuma Lisa na ife, Adekunle Ojora, ya yi bankwana da duniya me dai bayan ya kwashe kusan shekara 100 a cikinta
- Marigayin ya kasance suruki ga tsohon gwamnan jihar Kwara kuma tsohon shugaban majalisar dattawa a mulkin Muhammadu Buhari
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Legas - Babban basarake mai rike da sarautar Otunba na Legas Adekunle Ojora, ya yi bankwana da duniya.
Otunba na Legas kuma Lisa na Ife, ya rasu yana da shekara 93 a duniya a ranar Laraba, 28 ga watan Janairun 2026.

Source: Twitter
Iyalan marigayin sun sanar da rasuwarsa ne ta wata sanarwa da suka fitar a ranar Laraba, 28 ga watan Janairun 2026, wadda aka sanya a shafin X.
Surikin Bukola Saraki ya rasu
A cikin sanarwar, Toyin Ojora-Saraki, ’yar marigayin kuma matar tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, ta ce za a binne Otunba Ojora a birnin Legas bisa tanadin addinin Musulunci.
An haifi Otunba Ojora ne a ranar 13 ga Yuni, 1932, kuma ya kasance fitaccen mutum a harkokin gargajiya, al’adu da masarautun Legas, inda aka san shi da asali, hikima da hidima ga al’umma.
A tsawon rayuwarsa, Otunba Ojora ya taka muhimmiyar rawa wajen kiyaye martabar al’adun Yarbawa, tsarin masarauta da haɗin kan iyalan masu sarauta a Legas.
Otunba Adekunle Ojora ya rasu ya bar ’ya’ya, jikoki da 'ya'yan jikoki masu yawa, tare da tarihi mai girma na kasancewa ginshiƙi a tarihin masarauta da al’adun Legas.
An sanar da rasuwar Otunba na Legas
“Da cikakken miƙa wuya ga nufin Allah Maɗaukakin Sarki (SWT), iyalan Ojora na Legas suna sanar da rasuwar ubanmu, Otunba Adekunle Ojora, Otunba na Legas kuma Lisa na Ife, wanda ya koma ga Mahaliccinsa da safiyar yau."
“Yana da shekara 93 a duniya, kuma za a birne shi a Legas bisa tanadin addinin Musulunci. Ya bar mata, Erelu Ojolape Ojora, da ’ya’yansa, jikokinsa da 'ya'yan jikoki."
“Muna roƙon al’umma da su taya mu da yin addu’a ga Allah Ya gafarta wa bawansa, wanda ya rayu rayuwa mai mutunci, Ya sanya masa sauƙi a kabari, Ya kuma ba shi Aljannar Firdausi.”
- Toyin Ojora-Saraki

Source: Twitter
Otunba Ojora ya kasance shahararren jigo a harkokin kasuwanci da shugabanci, inda aikinsa ya shafi aikin jarida, hidimar jama’a, siyasa da jagoranci a manyan kamfanoni tun bayan samun ’yancin kai na Najeriya.
Ya riƙe manyan mukamai masu tasiri, ciki har da shugabanci a manyan kamfanoni na dogon lokaci, tare da kasancewa cikin tsantsar tushen al’adun gargajiya da masarautar Yarbawa da ta Legas.
Mahaifin kyaftin din Super Eagles ya rasu
A wani labarin kuma, kun ji cewa mahaifin kyaftin din tawagar Super Eagles, Wilfried Ndidi, ya yi bankwana da duniya.
Mahaifin nasa mai suna, Sunday Ndidi, wanda tsohon jami'in soja ne, ya rasu sakamakon hadarin mota mai muni da ya faru a jihar Delta.
Hadarin motar ya faru ne a garin Umunede, daga bisani aka garzaya da shi asibitin Agbor, amma likitoci suka tabbatar da cewa rai ya yi halinsa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

