Shiri Ya Baci: 'Yan Boko Haram Sun Kashe Sojoji, Sun Cafke Wani Babban Soja a Borno

Shiri Ya Baci: 'Yan Boko Haram Sun Kashe Sojoji, Sun Cafke Wani Babban Soja a Borno

  • 'Yan ta'addan Boko Haram dauke da makamai sun kai wani harin kwanton bauna kan dakarun sojojin Najeriya a jihar Borno
  • Harin na 'yan ta'addan ya jawo asarar rayukan dakarun sojoji bayan da aka bude musu wita ba zato ba tsammani a cikin daji
  • Majiyoyi sun bayyana adadi mabambanta na sojojin da aka kashe, yayin da aka tabbatar da sace wani babban soja

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Borno - 'Yan ta'addan Boko Haram sun kai wani harin kwanton bauna kan dakarun sojoji wanda ya jawo asarar rayuka a jihar Borno.

Harin na 'yan Boko Haram ya jawo asarar rayukan akalla sojojin Najeriya tara tare da bacewar wasu.

'Yan Boko Haram sun kashe sojoji a Borno
Babban hafsan rundunar sojojin kasan Najeriya, Laftanar Janar Waidi Shaibu Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Rahoton kafar Reuters ya nuna cewa harin ya auku ne a ranar Litinin, 26 ga watan Janairun 2026.

'Yan Boko Haram sun farmaki sojoji

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun take yarjejeniyar sulhu, sun afkawa Katsinawa

Majiyoyin sun ce 'yan ta'addan sun kai harin ne ta hanyar amfani da abubuwan fashewa da bindigogi.

Sun kai farmakin ne dai kan jerin sojoji fiye da 30 da ke sintiri a kafa a wajen garin Damask, kusa da iyakar Jamhuriyar Nijar.

“Mun rasa sojoji tara a kwanton ɓauna da ’yan ta’addan Boko Haram suka yi mana, yayin da wasu da dama har yanzu ba a san inda suke ba."

- Wani jami'in soja

An dasa abin fashewa a hanyar sojoji

Jami’in, wanda ya buƙaci a sakaya sunansa, ya ce sojojin suna tazarar kilomita 25 daga sansaninsu lokacin da suka tarwatse zuwa kowane bangare sakamakon ruwan wuta da ’yan ta’addan suka rika yi musu ba tare da kakkautawa ba.

“’Yan ta’addan sun tayar da wani abin fashewa da suka riga suka dasa a kan hanya, lamarin da ya ƙara yawan mace-mace da ruɗani a tsakanin sojojin."

- Wani jami'in soja

An sace babban soja a harin Boko Haram

Ya ce sojoji takwas ne kawai suka samu damar komawa sansani, yayin da sauran suka bace, ciki har da kwamandansu mai mukamin Manjo.

Kara karanta wannan

Daga fitowa gida, 'yan Boko Haram sun harbe malamin addini da jami'an tsaro har lahira

“Wani mutum da ya bayyana kansa a matsayin ɗan Boko Haram ne ke ɗaukar kiran wayar kwamandan, lamarin da ke nuna yana hannun ’yan ta’addan."

- Wani jami'in soja

Wasu sojoji sun yi nasarar tsira

Jaridar Leaderahip ta ce wata majiya daban ta ce sojoji bakwai sun mutu a artabu, wasu sojoji 11 sun tsere, amma an kama wasu 13 ciki har da kwamandan mai mukamin Manjo.

'Yan Boko Haram sun sace babban soja a Borno
Taswirar jihar Borno, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original
“Manjon ya yi gumurzu ƙwarai, amma daga ƙarshe aka kama shi, kuma Boko Haram suka kwace wayarsa."

- Wata majiya

Ya-Mulam Kadai, kakakin wata rundunar sa-kai da gwamnati ke ɗaukar nauyinta wadda ke taimaka wa sojoji a Damask, ya tabbatar da adadin waɗanda suka mutu da kuma waɗanda suka ɓace.

Ya ce rundunar bincike ta soji da aka tura wurin harin ta gano gawarwakin sojoji tara da aka kashe.

'Yan Boko Haram sun kashe malami

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu 'yan ta'addan Boko Haram sun yi aika-aika ta hanyar kashe wani malamin addini a jihar Borno.

'Yan ta'addan sun kashe malamin addinin ne tare da mafarauta biyu, da wasu fararen hula a kauyen Tarfa da ke cikin karamar hukumar Biu a jihar Borno.

Tsagerun 'yan ta'adan yan ta'addan sun kai wannan farmaki ne da misalin karfe 4:00 na yammaci, inda suka bude wuta kan mai uwa da wabi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng