Yunkurin Juyin Mulki: Sojojin Najeriya 16 za Su Fuskanci Hukuncin Kisa
- Akalla jami’an soji 16 da ake zargi da yunkurin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu za su fuskanci hukunci mai tsanani idan kotu ta tabbatar da laifinsu
- Rahotanni sun nuna cewa binciken da rundunar soji ta gudanar tun watan Oktoba, 2025 ya tabbatar da samunsu da hannu a yunkurin kifar da gwamnatin Tinubu
- Biyo bayan lamarin, wasu tsofaffin hafsoshin soji sun ce dokar sojin Najeriya ta tanadi hukuncin kisa ga duk wanda aka samu da laifin yunkurin kifar da gwamnati
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Abuja – Aƙalla jami’an soji 16 da ake zargi da shirya yunkurin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu za su fuskanci hukunci mai tsanani, ciki har da kisa, bisa tanadin dokokin rundunar soji ta Najeriya.
Jami’an da ake zargin sun hada da masu mukamai daga matakin Kyaftin har zuwa Birgediya Janar, kuma an tsare su ne bayan samun bayanan sirri kan wani shiri da ake zargin yana da nufin kifar da gwamnatin farar hula.

Source: Facebook
Rahoton Daily Trust ya nuna cewa wannan na zuwa ne bayan da rundunar sojin ta amince cewa jami’an da aka tsare tun watan Oktoba, 2025 suna da hannu a yunkurin kifar da gwamnati a binciken da aka kammala.
Doka ta tanadi hukuncin kisa a juyin mulki
Tsofaffin hafsoshin soji biyu, Janar Bashir Adewinbi mai ritaya da Manjo Bashir Galma mai ritaya, sun bayyana cewa yunkurin juyin mulki babban laifi ne a rundunar soji.
A cewarsu, dokar Rundunar Sojin Najeriya ta tanadi hukuncin kisa ga duk wanda aka kama da laifin yunkurin kifar da gwamnati a kasar nan.
Janar Adewinbi ya ce:
“Idan an tabbatar da yunkurin juyin mulki, babu wata hanya da za su tsira. Hukuncin da doka ta tanada shi ne kisa, sai dai idan Shugaban kasa ya yi amfani da ikonsa ya sassauta hukuncin.”
Ya kara da cewa manufar hukuncin mai tsanani ita ce ya zama darasi ga duk wanda ke da tunanin kawo cikas ga dimokuradiyya a Najeriya.
Manjo Galma kuwa ya ce duk wanda ya shiga rundunar soji dole ne ya fahimci cewa yana bin dokoki biyu ne – dokar soja da kuma kundin tsarin mulkin Najeriya.
An yi wa sojoji hukuncin kisa a baya
Rahotanni sun bayyana cewa a tarihin Najeriya, an taba samun shari’o’in yunkurin juyin mulki da dama da suka kai ga hukuncin kisa
A watan Disamba, 1985, gwamnatin Ibrahim Babangida ta sanar da dakile wani yunkurin juyin mulki, inda aka kama Janar Mamman Vatsa da wasu jami’ai.
Daga bisani, a watan Maris na shekarar 1986, an zartar da hukuncin kisa ta hanyar harbi ga jami’ai 10 da aka kama ciki har da Vatsa.

Source: Facebook
A watan Yuli, 1995, gwamnatin Sani Abacha ta yanke wa mutane 40 hukunci kan yunkurin juyin mulki, ciki har da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo da Shehu Musa Yar’Adua da aka daure.

Kara karanta wannan
Jerin manyan sojoji 16 da hedkwatar tsaro 'ta gano' suna da hannu a shirin kifar da Tinubu
Yadda aka so yin juyin mulki a Najeriya
A wani rahoton, mun kawo muku cewa an kara samun bayanai game da yunkurin juyin mulkin da ake ce wasu sojoji sun shirya yi a Najeriya.
Bayanan da suka fito sun nuna cewa wani Kanal da ba a bayyana sunansa ba ne ya jagoranci shirya juyin mulkin saboda rashin samun karin matsayi.
Binciken da hukumomi ke yi sun nuna cewa an samu wasu muhimman takardu a cikin motar sojan tare da bayanai kan kudin da aka tura wa jama'a.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

