Ayyukan da Gwamnatin Kano za Ta Saka a gaba bayan Abba Ya Koma APC
- Gwamnatin Kano ta ce tana kara kaimi wajen samar da manyan kayayyakin more rayuwa a kananan hukumomin jihar 44
- Ma'aikatar kananan hukumomi ta Kano ta ce an ware kaso mai tsoka na kasafin kudin 2026 ga ilimi, lafiya da ababen more rayuwa
- Gwamnatin ta APC ta ce adalci da daidaito ne jigon raba romon dimokuradiyya a karkashin Mai girma Abba Kabir Yusuf
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa tana kara zage damtse domin samar da muhimman kayayyakin more rayuwa a fadin kananan hukumomi 44 na jihar.
Ma'aikatar kananan hukumomi ta jihar ce ta tabbatar da hakan, inda ta ce an dauko gabarar aikin ne da nufin cike gibin ci gaba da ya dade yana addabar al’ummomin karkara.

Kara karanta wannan
Jerin manyan sojoji 16 da hedkwatar tsaro 'ta gano' suna da hannu a shirin kifar da Tinubu

Source: Facebook
Daily Trust ta wallafa cewa Kwamishinan kananan hukumomi da harkokin masarauta na jihar, Alhaji Mohammed Tajo Othman, ne ya tabbatar da haka.
Gwamnatin Abba ta dauko manyan ayyuka
Trust radio ta wallafa cewa Mohammed Tajo Othman bayyana hakan yayin da yake bayani kan manufofi da manyan ayyukan da ma’aikatarsa ke aiwatarwa a karkashin mulkin Gwamna Abba Kabir Yusuf.
A wata sanarwa da ya fitar, Mohammed Tajo Othman ya ce gwamnatin jihar ta fi mayar da hankali kan muhimman fannoni kamar kiwon lafiya a matakin farko.
Haka kuma ana mayar da hakali a kan samar da ruwan sha, ilimi, noma, wutar lantarki da kuma hanyoyin karkara.
Ya bayyana cewa bunkasa ababen more rayuwa na da matukar muhimmanci wajen inganta rayuwar al’umma tare da kara yawan samar da arziki a jihar.
A cewarsa, dabarun da ma’aikatar ke bi sun yi daidai da kudurin gwamnan jihar na tabbatar da adalci, gaskiya da rarraba albarkatu cikin daidaito a fadin Kano.
Gwamnati ta yi kasafi da bukatun jama'a
Kwamishinan ya kara da cewa ana gyara makarantu da suka lalace domin inganta koyarwa da koyo da koyarwa a fadin Kano.

Source: Facebook
Haka kuma an gina hanyoyin karkara domin saukaka wa manoma jigilar amfanin gona zuwa kasuwanni, lamarin da zai kara karfin sarkar darajar noma.
Alhaji Mohammed Tajo Othman ya bayyana cewa dukkannin wadannan tsare-tsare suna samun cikakken goyon bayan kasafin kudi.
Ya ce a cikin kasafin kudin jihar na shekarar 2026 da ya kai Naira tiriliyan 1.368, an ware 31% ga bangaren ilimi,16% ga lafiya, yayin da ababen more rayuwa suka samu 25%.
Dangane da ilimi, ya ce an dauki fiye da malamai 6,000 aiki, an shigar da malamai ‘yan sa kai 2,000 cikin aikin gwamnati, an gyara dubunnan dakunan karatu, sannan an raba kusan kayan makaranta 789,000 ga dalibai.
Ya kara da cewa an rage kudin makaranta a manyan makarantun gwamnati da 50%, an farfado da tallafin karatu zuwa kasashen waje ga masu digirin digirgir, kuma jihar Kano ta zo ta daya a fadin Najeriya a jarabawar NECO ta 2025.
An dakatar da ayyukan islamiyya a Kano
A wani labarin, mun wallafa cewa hukumar ilimi ta karamar hukumar Kumbotso a Kano ta bayar da umarnin dakatar da ayyukan makarantar Islamiyya ta Halqatul Mu’awiyya da ke unguwar Sabuwar Gandu.
Wannan mataki ya biyo bayan zargin cewa makarantar na shirin gudanar da saukar karatun Alƙur’ani Mai Girma ba tare da bin ƙa’idoji da dokokin da suka dace ba, kamar yadda hukumar ta bayyana.
Sanarwar dakatarwar ta fito ne a rubuce, inda Sakataren Ilimi na ƙaramar hukumar, Aminu Abdullahi, ya sanya wa takardar hannu, inda ta kara da cewa an rufe makarantar ne saboda wasu dalilai.
Asali: Legit.ng

