Awanni da Shigar Abba APC, Kotu Ta Garkame Wasu Manyan Ma'aikatan Gwamnatin Kano
- Kotun tarayya ta tura shugaban hukumar zabe ta Jihar Kano Farfesa Sani Malumfashi gidan yari kan zargin karkatar da Naira biliyan daya
- ICPC ta yi zargin cewa wadanda ake zargin sun yi amfani da asusun wata gona wajen sace kudaden hukumar KANSIEC a 2024
- Mai shari'a James Omotosho ya ba da umarnin tsare jami'an a gidan yarin Kuje har sai sun shigar da takardar neman beli a gaban kotu
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Wata Babbar Kotun Tarayya dake Abujata ba da umarnin tsare shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Kano (KANSIEC), Farfesa Sani Malumfashi, a gidan yari.
An yanke wa Farfesa Malumfashi wannan hukunci ne tare da sakataren KANSIEC, Anas Muhammed Mustapha, da kuma Mataimakin daraktan akawu, Ado Garba.

Source: UGC
Zargin karkatar da N1.02bn a Kano
Mai shari'a James Omotosho ya ba da umarnin tsare ma'aikatan uku ne a ranar Talata biyo bayan zarginsu da hannu a wawure Naira biliyan 1.02, in ji rahoton Daily Trust.
Alkalin ya bayar da umarnin tsare su ne bayan da hukumar ICPC ta gurfanar da su kan tuhume-tuhume shida da suka shafi karkatar da kuɗaɗen jama'a.
ICPC ta yi zargin cewa jami'an hukumar zaɓen sun karkatar da kuɗaɗen ne daga asusun hukumar KANSIEC zuwa wasu asusun banki na wata gona mai suna SLM Agro Global Farm.
A cewar hukumar yaƙi da rashawar, tsakanin watannin Nuwamba da Disambar 2024, waɗanda ake zargin sun haɗa baki wajen karɓar tsabar kuɗi har Naira miliyan 450 ta asusun gonar dake bankin Jaiz.
Sauran kuɗaɗen da ake zargin an karkatar sun haɗa da Naira miliyan 310 da kuma Naira miliyan 260 waɗanda duka aka tura su zuwa asusun gonar, lamarin da ya saɓa wa dokar hana safarar kuɗaɗen haram ta 2022.
Tattaunawa kan neman belin waɗanda ake zargi
Yayin da aka karanta musu tuhume-tuhumen, Farfesa Malumfashi da abokan aikinsa sun bayyana cewa ba su da laifi, inda lauyansu, Mahmud Magaji (SAN), ya roƙi kotu ta ba su beli.
Lauyan ya bayyana cewa waɗanda ake zargin sun kasance suna kiyaye belin da hukumar ICPC ta ba su tun da fari ba tare da sun karya doka ba, don haka ya kamata kotu ta amince da belinsu.
Duk da haka, lauyan mai gabatar da ƙara, Dr. Osuobeni Akponimisingha, ya nuna rashin amincewa da buƙatar belin ta baki, inda ya ce ya bar wa kotu ikon yanke hukunci, in ji rahoton Vanguard.

Source: Original
Hukuncin alkali da tura su gidan yarin Kuje
A cikin gajeren hukuncin da ya yanke, Mai shari'a Omotosho ya ƙi amincewa da buƙatar belin ta baki, inda ya bayyana cewa dole ne lauyoyin su shigar da takardar neman beli a hukumance.
Alkali ya umarci jami'an tsaro da su tafi da waɗanda ake zargin zuwa gidan yarin Kuje dake Abuja domin tsare su har zuwa lokacin da za a sake tattaunawa kan batun belin nasu.
An ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar Laraba domin bai wa hukumar ICPC damar mayar da martani kan takardun neman belin da za a shigar.
Gwamnan Kano, Abba ya shiga APC
A wani labari, mun ruwaito cewa, Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya shiga jam'iyyar APC a hukumance a ranar Litinin, 26 ga Janairu, 2026.

Kara karanta wannan
Binciken makamai: Malami na tsaka mai wuya a hannun hukumar DSS, ya fito ya yi magana
Wannan na zuwa ne kwanaki uku bayan Abba ya mika takardar ficewa daga jam'iyyar NNPP a mazabarsa da ke karamar hukumar Gwale a Kano.
Tsohon shugaban jam'iyyar APC na kasa, Abdullahi Ganduje da Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Barau Jibrin ne suka karbi Gwamna Abba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

