'Aikinku bai Kare ba': Gwamnatin Tinubu Ta Waiwaiyi Tsofaffin Sojoji, Za Su Kare Ƙasa

'Aikinku bai Kare ba': Gwamnatin Tinubu Ta Waiwaiyi Tsofaffin Sojoji, Za Su Kare Ƙasa

  • Gwamnatin Tarayya ta bayyana shirin tura tsofaffin sojoji domin kare wuraren da ba su samu cikakken tsaro ba
  • Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya), ya kafa kwamitin mutum 18 domin dawo da wadannan wurare
  • Musa ya ce amfani da tsofaffin sojoji zai rage dogaro da farmakin soja kaɗai, ya ƙara sahihan bayanan sirri, tare da gina amincewa tsakanin al’umma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Gwamnatin Tarayya ta bayyana shirinta na tura tsofaffin sojoji domin taimakawa wajen tsare wuraren da ba gwamnati ke iko da su ba a fadin Najeriya.

Matakin na daga cikin dabarun karfafa tsaron kasa da kuma farfado da harkokin tattalin arziki a yankunan da rikice-rikice suka daɗe suna addabarsu.

Gwamnatin Tinubu za shirya amfani da tsofaffin sojoji domin tsaro
Ministan tsaro, Christopher Musa da Shugaba Bola Tinubu. Hoto: HQ Nigerian Army, Bayo Onanuga/Facebook.
Source: Facebook

Za a sake amfani da tsofaffin sojoji

Wannan ya biyo bayan kaddamar da kwamitin mutum 18 da Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya), ya yi domin dawo da wadannan wurare, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

Juyin mulki: Yadda Kanal na soja ya tsara kifar da Gwamnatin Bola Tinubu

Kwamitin zai kuma duba hanyoyin sake tsara lamuran tsaro da tsofaffin sojoji domin su bada gudunmawa ga tsaron kasa.

Janar Musa ya bayyana cewa tura tsofaffin sojoji zai taimaka wajen cike gibin tsaro a wuraren da ikon gwamnati bai kai ba.

Ya ce gogewar da wadannan tsofaffin sojoji suke da ita za ta taimaka wajen tsaro, ci gaba da kuma hadin kai da al’ummomin yankuna.

A cewarsa, wannan tsari yana nuna sauyi daga dogaro da farmakin soja kaɗai zuwa tsarin tsaro mai dorewa da haɗin gwiwa.

Ministan ya jaddada cewa shirin zai magance tushen matsalolin tsaro da suka shafi tattalin arziki da zamantakewa a yankuna masu rikici.

Sojoji za su yi amfani da tsofaffin jami'ansu
Hafsan sojojin Najeriya, Laftanar-janar Waidi Shaibu. Hoto: HQ Nigerian Army.
Source: Facebook

Amfanin da tsofaffin sojojin za su yi

Kwamitin na da umarnin sake tsara tsofaffin sojoji domin su taimaka wajen bunkasa tattalin arzikin kasa da kare wuraren da ba su cikakken tsaro.

Musa ya ce gwamnati na son tabbatar da cewa tsofaffin sojojin da suka yi wa kasa hidima suna samun rayuwa mai amfani bayan ritaya.

Ya kara da cewa hada tsofaffin sojoji cikin tsaro da ci gaba zai karfafa mallakar tsaro a cikin al’umma da gina amincewa, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Jerin manyan sojoji 16 da hedkwatar tsaro 'ta gano' suna da hannu a shirin kifar da Tinubu

Ministan ya bukaci mambobin kwamitin su fito da sababbin dabaru da shawarwari masu amfani domin samar da cikakken tsarin tsaro mai dorewa.

Mambobin kwamitin sun fito daga sassa daban-daban ciki har da Ma’aikatar Tsaro, Nigerian Legion, Sojoji, Rundunar Ruwa da ta Sama.

A baya, an dade ana kira da a shigar da tsofaffin sojoji cikin tsarin tsaro domin rage nauyin da ke kan sojojin da ke bakin aiki.

Sojoji sun bankado kaburburan Boko Haram

A wani labari, rundunar soji ta samu gagarumar nasara bayan kutsawa cikin yankin Timbuktu Triangle, wani yanki da ake dangantawa da Boko Haram da ISWAP.

A yayin ci gaba da kakkabe ‘yan ta’adda, sojoji sun yi artabu da mayakan kungiyar Boko Haram, lamarin da ya janyo asara ga dukkan bangarorin biyu.

Rundunar ta ce an gano kaburburan ‘yan ta’adda da dama, abin da ke nuna irin mummunan raunin da aka yi musu a wadannan hare-hare da aka kai kansu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.