Bidiyo: Lokuta 3 da Aka Ga Shugaba Tinubu Ya Yi Tuntube Ya Fadi a wajen Taro

Bidiyo: Lokuta 3 da Aka Ga Shugaba Tinubu Ya Yi Tuntube Ya Fadi a wajen Taro

  • Shugaba Bola Tinubu ya yi tuntube a kasar Turkiyya yayin ziyarar karfafa dangantakar diflomasiyya da cinikayya tsakanin kasashen biyu
  • Sai dai, ba wannan ne karon farko da aka taba ganin Tinubu ya yi tuntube a bainar jama'a ba, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce kan lafiyarsa
  • Legit Hausa ta zakulo lokuta uku da aka taba ganin Tinubu ya yi tuntube, wani wurin ma har ya fadi a wajen taruka, da kuma bidiyon da aka samu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

A matsayinsa na shugaban ƙasa kuma tsohon gwamnan Jihar Legas, Bola Ahmed Tinubu ya ja hankulan jama'a a wasu lokuta da ya yi tuntube ya fadi a bainar jama'a

Waɗannan lokuta, waɗanda bidiyon su ya karade kafafen sada zumunta, sun haifar da tattaunawa game da lafiyar Tinubu da kuma kwarin jikinsa a matsayinsa na shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya yi tuntube a Turkiyya, ya fadi kasa yayin ziyara a kasar

Shugaba Bola Tinubu ya sha faduwa a wasu tarurruka da ya halarta
Shugaba Bola Tinubu ya na jawabi a wani taro, lokacin yakin neman zabensa a 2023. Hoto: @officialABAT
Source: Twitter

Legit Hausa ta yi bitar lokuta uku da aka ruwaito Shugaba Tinubu ya yi tuntube ko ya faɗi yayin gudanar da ayyukansa na hukuma a ciki da wajen Najeriya.

Tuntube a jihar Kaduna – Maris 2021

A watan Maris na shekarar 2021, jaridar The Punch ta ruwaito cewa Bola Ahmed Tinubu, wanda a lokacin yake neman takarar shugabancin ƙasa, ya yi tuntube a Kaduna.

Wani bidiyo da jaridar ta wallafa ya nuna yadda Tinubu ya yi tuntube a tsakanin kujeru biyu yayin da ya isa wurin taron bitar "Arewa House" karo na 11.

Nan take mataimakansa da wasu baƙi suka tallafa masa ya tashi, inda aka ci gaba da gudanar da taron ba tare da samun wani tsaiko ba.

Kalli bidiyon a kasa:

Faɗuwa a ranar Dimokuradiyya – 2024

A watan Yunin 2024, kafar watsa labarai ta BBC ta ruwaito cewa Shugaba Tinubu ya zame tare da faɗuwa kasa yayin wani taro na murnar cikar Najeriya shekaru 25 da dawowar dimokuradiyya.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu 'ya amince' da kirkiro sabuwar jiha 1 a Najeriya, an bayyana sunanta

Shugaban, wanda a lokacin yake da shekaru 72, ya faɗi ne yayin da yake ƙoƙarin hawa motar da za ta zagaya da shi a filin "Eagle Square" dake Abuja.

Daga baya a wannan daren, yayin da yake jawabi a wurin liyafar cin abinci, Tinubu ya yi barkwanci inda ya ce:

"Na ga bidiyo na ya karade ko'ina a kafafen sada zumunta bayan na faɗi."

Kalli bidiyon jawabin Tinubu da jaridar Punch ta wallafa a kasa:

Shugaba Bola Tinubu ya fadi a Turkiyya
Shugaba Bola Tinubu a saman mota lokacin da ake faretin ranar dimokuradiyya a Eagle Square, Abuja. Hoto: @officialABAT
Source: Twitter

Tuntube a kasar Turkiyya – Janairu 2026

A cikin wannan watan na Janairun 2026, jaridar Guardian Nigeria ta ruwaito cewa Shugaba Tinubu ya yi tuntube ya fadi yayin wani faretin karramawa a ƙasar Turkiyya.

Bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta ya nuna shugaban ya fadi, amma ya yi nasarar mikewa da taimakon na-kusa da shi tare da ci gaba da tattakin faretin.

Kalli bidiyon faduwar da Sahara Reporters ta wallafa a X:

'Tinubu bai ji ciwo ba' - Fadar shugaban kasa

A wani labari, mun ruwaito cewa, fadar shugaban kasa ta yi bayanin abin da ya faru da Shugaba Bola Tinubu a taron maraba da aka shirya masa a Turkiyya.

Kara karanta wannan

Badaru ya gana da Kwankwaso bayan ficewar Abba daga NNPP? An gano gaskiya

Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga ya ce Tinubu ya ci tuntube ne da wani karfe, wanda ya sa ya fadi, amma ya ce shugaban bai ji rauni ba.

Bayo Onanuga ya tabbatar da cewa Tinubu na cikin koshin lafiya kuma ya ci gaba da ayyukan da aka tsara masa a ziyarar aikin da ya fara a kasar Turkiyya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com