Bayan Manoma Sun Tafka Asara a Arewa, An ba Gwamnatin Tinubu Shawara kan Shigo da Shinkafa
- An fara neman gwamnatin tarayya karkashin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta dakatar da shigo da shinkafa daga kasashen ketare
- Wani kwamitin manufofin noma da ke samun goyon bayan fadar shugaban kasa ya nuna damuwarsa kan adadin shinkafar da ke cikin Najeriya
- Ya ce alkaluman kasuwannin duniya sun nuna cewa 'yan Najeriya sun shigo da shinkafa sama da tan miliyan 2 kan makudan kudade
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Wani kwamitin tsara manufofin harkar noma da gwamnatin tarayya ke marawa baya ya ba da shawarar rufe dukkan kofofin shigo da shinkafa a hukumance.
Kwamitin ya dogara ne da raguwar hauhawar farashin abinci da hujjojin da ke nuna cewa yawaitar shinkafa a Najeriya ta samo asali ne daga yawan shigo da ita daga waje, ba a gida aka noma ta ba.

Kara karanta wannan
Jerin manyan sojoji 16 da hedkwatar tsaro 'ta gano' suna da hannu a shirin kifar da Tinubu

Source: Getty Images
Wannan shawara na zuwa ne a lokacin da 'yan Najeriya suka kashe sama da N1tn wajen shigo da tan miliyan 2.4 na shinkafa cikin kasar, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Haka zalika, manoman shinkafa sun tafka asara a bana saboda yawna shigo da ita daga waje, wanda ya jawo faduwar farashi saboda yawan da ta yi a kasuwanni.
Yadda shigo da shinkafa ya wuce gona da iri
Idan aka duba alkaluman kasuwannin duniya, yawan shinkafar da aka shigo da ita Najeriya a 2025 ya nuna yadda aka fitar da makudan kudaden ketare, kodayake alkaluman kiyasi ne kawai.
Bisa farashin Thailand, kowane tan guda na shinkafa na kai wa kusan $370, wanda hakan na nuna cewa tan miliyan 2.4 zai ci Dalar Amurka miliyan 888, wanda ya yi daidai da kusan N1.26tn a farashin canji na babban bankin Najeriya.
Farashin shinkafar Indiya kuma ya fi sauki, kowane tan na kai wa kusan $347, wanda zai sa kudin ya koma kusan Dalar Amurka miliyan 832.8, kwatankwacin N1.18tn.

Kara karanta wannan
Shugaba Tinubu 'ya amince' da kirkiro sabuwar jiha 1 a Najeriya, an bayyana sunanta
An nemi a dakatar da shigo da shinkafa
Biyo bayan shigo da tan miliyan 2.4, kwamitin ya ba da shawarar cewa gwamnatin tarayya ta rufe bodar shigo da shinkafa "ganin cewa hauhawar farashin abinci ya fadi kasa da kashi 14%."
Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar bayan taro na biyu na tsarin National Agribusiness Policy Mechanism (NAPM) da aka gudanar a Abuja a watan Disambar 2025, in ji rahoton Bussiness Day.

Source: Getty Images
An kaddamar da wannan tsarin ne a watan Mayun 2025 domin hada kan manufofin abinci da noma na Najeriya ta hanyar amfani da sahihan bayanai. Kwamitin kula da harkokin abinci na shugaban kasa, ke kula da wannan tsari.
"Najeriya na da isasshen abinci, amma wadatar abinci musamman shinkafa da alkama har yanzu ya dogara ne kan shigo da su, wanda hakan ke nuna nakasu a tsarin noma na cikin gida," in ji sanarwar.
Farashin abinci ya sauka a Abuja
A wani labarin, kun ji cewa farashin wasu muhimman kayan abinci da ake amfani da su yau da kullum ya sake sauka a kasuwannin Babban Birnin Tarayya Abuja.

Kara karanta wannan
Ta tabbata an yi yunkurin yi wa Tinubu juyin mulki, sojojin Najeriya sun fitar da bayanai
Binciken kasuwa da aka yi ya nuna cewa bayan bukukuwan Kirsimeti, farashin kayan abinci kamar tumatir, barkono, albasa, dankali da wake ya ragu a yawancin kasuwanni.
Wasu mazauna yankin sun ce raguwar farashin ta kawo musu sauƙi, amma sun bukaci gwamnati ta tabbatar da dorewar lamarin, ganin yadda ƙarfin sayen jama’a ke ƙara raguwa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng