Zance Ya Fito: Barau Ya Fadi Abin da Tinubu Ya Gayawa Jagororin APC kafin Shigowar Abba

Zance Ya Fito: Barau Ya Fadi Abin da Tinubu Ya Gayawa Jagororin APC kafin Shigowar Abba

  • Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya yi magana kan shigowar Gwamna Abba Kabir zuwa jam'iyyar APC
  • Sanata Barau ha bayyana cewa jagororin APC a Kano sun samu sako daga wajen Shugaba Bola Tinubu gabanin shigowar Abba cikin jam'iyyar
  • Ya bayyana cewa tun da gwamnan na Kano ya riga ya shigo APC, za su ba shi dukkanin hadin kan da yake bukata

​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Mataimakin shugaban majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya bayyana yadda ta kaya tsakanin Shugaba Bola Tinubu da jagorin APC a Kano kan shigowar Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Sanata Barau ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya umarci jagororin APC a Kano da su ba Gwamna Abba Kabir Yusuf cikakken goyon baya gabanin shigowarsa jam’iyyar.

Tinubu ya yi magana da jagororin APC a Kano
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, Sanata Barau Jibrin da Gwamna Abba Kabir Yusuf na Kano Hoto: Mohammed Umaru Bago, Barau I Jibrin
Source: Facebook

Sanata Barau ya bayyana hakan ne yayin tattaunawa da manema labarai wadda ya sanya bidiyonta a shafinsa na Facebook a ranar Talata, 27 ga watan Janairun 2026.

Kara karanta wannan

Abin da Kwankwaso da mutanen Kano suka dauki hadewar Gwamna Abba da Ganduje a APC

Bola Tinubu ya ba jagororin APC shawara

Ya ce Shugaba Tinubu ya shawarci masu ruwa da tsaki na APC da su yi aiki kafaɗa da kafaɗa da gwamnan tare da kauce wa duk wani abu da zai iya ɗauke masa hankali daga sauke nauyin shugabanci yadda ya kamata ga al’ummar jhar Kano.

"Babu shakka ya gaya mana mu je mu zauna mu yi aiki tare da gwamna, kuma dama uba nagari abin da zai fada kenan tun da yana da kishin Kano yana da kishin Najeriya."
"Ba shakka ya gaya mana a je a zauna a yi aiki tare kuma a taimaka masa. Duk uba zai yi jan hankali ga 'ya'yansa."
"Dama can a wannan tafarkin na ke. Ai tun da ya shigo jam'iyyarmu, mun zama uwa daya uba daya da shi."

- Sanata Barau Jibrin

Shirin jam'iyyar APC kan Gwamna Abba

Mataimakin shugaban majalisar dattawan ya ce dole ne APC a Kano ta maida hankali yanzu wajen tallafa wa Gwamna Abba Kabir Yusuf domin ya yi nasara, yana mai jaddada cewa haɗin kai a cikin jam’iyyar shi ne mabuɗin samun ci gaba.

Kara karanta wannan

An fara siyasa: Barau ya sauya sunan kungiyarsa bayan Abba Kabir ya koma APC

Barau ya kara da cewa bayan shigowar gwamnan APC, duk wata fafatawa ta siyasa da muradin kashin kai a cikin jam’iyyar ya kamata a ajiye su gefe domin tabbatar da kwanciyar hankali da ci gaban jihar.

A cewarsa, hana gwamnan damar samun wa’adi na biyu zai lalata kokarin da ake yi a halin yanzu tare da kawo cikas ga harkokin mulki a jihar.

Sanata Barau ya taya Abba murnar shiga APC
Sanata Barau Jibrin da Abba Kabir Yusuf wajen taron shigowar gwamnan APC Hoto: Barau I. Jibrin
Source: Facebook

Barau ya sha hakura da takarar gwamna

Da yake magana kan gogewarsa a siyasa, Barau ya tuna lokuta da dama da ya ja da baya domin haɗin kan jam’iyya, ciki har da fafatawa kan kujerar shugabancin majalisar wakilai da kuma zaɓubbukan gwamna a Kano.

Ya jaddada cewa Shugaba Tinubu ya fahimci sarkakiyar siyasa, kuma ya karfafa shugabannin APC a Kano da su rungumi gwamnan a matsayin na su.

'Dan siyasar ya nemi ya yi takarar gwamnan Kano a 2023, amma a karshe ya rike kujerarsa ta Sanata mai wakiltar Arewacin kano a majalisar dattawa.

Barau ya hakura da takarar gwamna

A wani labarin kuma, kun ji cewa Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ya jingine burinsa na yin takarar gwamnan Kano a 2027.

Kara karanta wannan

Bayan gama tarbar Abba a APC, Barau ya tabo batun burinsa na takarar gwamna a 2027

Sanata Barau Jibrin ya bayyana cewa ya fasa yin takarar gwamna a zaben 2027 ne saboda shigowar Gwamna Abba Kabir zuwa jam'iyyar APC.

Mataimakin shugaban majalisar dattawan ya nuna cewa ya yi hakan ne don ba Gwamna Abba cikakken hadin kan da yake bukata don yin nasara.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng