'Yan Bindiga Sun Kafa Sharuddan Sakin Mutane Sama da 100 da Suka Sace a Kaduna

'Yan Bindiga Sun Kafa Sharuddan Sakin Mutane Sama da 100 da Suka Sace a Kaduna

  • Masu ibada sama da 100 a coci da 'yan bindiga suka sace a Kaduna na ci gaba da zama a tsare kwanaki bayan aukuwar lamarin
  • Tsagerun 'yan bindigan da suka sace su, sun kafa sharuddan da suke so a cika musu kafin su kyale mutanen su shaki iskar 'yanci
  • Sun bukaci a ba su miliyoyi a matsayin kudin fansa tare da neman a hado musu da babura kafin su yarda su saki mutanen

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kaduna - 'Yan bindiga sun lafta kudaden fansan da suke so a ba su kafin sakin masu ibada a coci da suka sace a Kaduna.

Mai Unguwar Kurmin Wali, Ishaku Dan’azumi, ya bayyana cewa ’yan bindigar da suka sace kusan masu ibada 177 sun buƙaci a biya Naira miliyan 250 tare da babura 20 domin sakin su.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun take yarjejeniyar sulhu, sun afkawa Katsinawa

'Yan bindiga sun bukaci kudin fansa kan sace masu ibada a Kaduna
Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna na gudanar da jawabi Hoto: Senator Uba Sani
Source: Facebook

Jaridar Vanguard ta ce Ishaku Dan'azumi ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai ta wayar tarho a daren Litinin, 26 ga watan Janairun 2026.

Wadanne sharudda 'yan bindiga suka kafa?

Ishaku Dan’azumi ya ce bukatar ta biyo bayan sace-sacen jama’a da ya faru ranar Lahadi, 17 ga Janairu, 2026, a lokacin da ake gudanar da ibada a coci-cocin yankin.

Ya ce harin ya shafi coci uku da suka haɗa da Cocin Cherubim and Seraphim 1 da 2, da kuma Cocin Evangelical Church Winning All (ECWA).

A cewarsa ’yan bindigan sun yi zargin cewa al’ummar Kurmin Wali sun sace babura 17 da aka kwace a hannunsu a lokacin wani samamen sojoji a karamar hukumar Kajuru.

“’Yan bindigan sun kira suka ce dole al’ummar Kurmin Wali su biya Naira miliyan 250 tare da samar da babura 20 kafin su saki masu ibadar da suka sace."

- Ishaku Dan’azumi

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun karya yarjejeniyar sulhu a Katsina, an kashe bayin Allah

'Yan bindiga sun yi magana game da kayan babura

Ya kara da cewa maharan sun kuma zargi wasu daga cikin al’ummar yankin da cire wasu sassa daga sauran baburan da suka rage, jaridar Leadership ta kawo labarin.

Fiye da masu ibada 100 har yanzu na ci gaba da kasancewa a hannun masu garkuwa da mutane bayan sace su, lamarin da ke kara tayar da hankalin mazauna yankin da shugabannin addini.

Duk da cewa hukumomin tsaro da jami’an gwamnati sun tabbatar da cewa ana ci gaba da ƙoƙarin ganin an saki mutanen ba tare da wani rauni ba, har zuwa lokacin rubuta wannan labari ba a sanar da samun wata nasara ba.

'Yan bindiga sun bukaci a ba su babura a Kaduna
Taswirar jihar Kaduna, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

An san inda 'yan bindigan suke

Wani jami’in tsaro da ya nemi a sakaya sunansa ya ce an gano inda aka kai waɗanda aka sace, amma ’yan bindigan na amfani da su a matsayin garkuwa domin hana kai hare-haren sama kan sansaninsu.

A halin yanzu, kokarin jin ta bakin rundunar ’yan sandan jihar Kaduna bai yi nasara ba.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun farmaki masu hakar ma'adanai a Plateau, an samu asarar rayuka

'Yan bindiga sun sace 'yan kasuwa

A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga dauke da makamai sun yi garkuwa da wasu 'yan kasuwa a Kaduna.

'Yan bindigan dai sun yi wa 'yan kasuwar kwanton bauna a hanyar Maro zuwa Kajuru, suka tattara su suka yi awon gaba da su zuwa cikin daji.

Tsagerun 'yan bindigan dai sun sace 'yan kasuwan ne guda hudu lokacin da suke kan hanyar komawa gida bayan sun yo sayayya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng