An Dauke Wuta a Najeriya, Turakun Lantarki Sun Dauke Karo na 2 cikin Kwana 5
- Mafi yawan 'yan Najeriya sun koma gidan jiya bayan da turakun wutar lantarki suka fadi karo na ciki a cikin shekarar 2026
- Rahotanni sun bayyana cewa turakun wuta da ke kai hasken lantarki ga kamfanonin rarraba wuta 11 sun fadi warwas
- Gwamnati ta ce ana kokarin maido da wutar lantarki a fadin kasa, duk da ana ci gaba da samun matsalolin faduwar turakun wuta
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Tsarin wutar lantarki na kasa ya sake fuskantar matsala bayan da aka samu rusowar turakun wutar latarki a ranar Talata, 27 ga watan Janairu, 2026.
Wannan shi ne karo na biyu da aka samu rugujewar tsarin wutar lantarki a shekarar 2026, lamarin da ya sake tayar da hankalin al’umma da masu ruwa da tsaki a bangaren makamashi.

Source: Getty Images
The Cable ta wallafa cewa an bayyana wannan lamari ne ta hanyar wani sakon gaggawa da da hukumar da ke kula da hasken wutar lantarki ta Nigeria National Grid, ta fitar.
Turakun wutar lantarki sun dauke
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa sanarwar ta tabbatar wa ‘yan kasa cewa tsarin rarraba wuta na kasa ya shiga mawuyacin hali.
Hukumar Nigerian Independent System Operator (NISO) ita ma ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta bayyana cewa zuwa karfe 10.54 na safiyar ranar Talata.
Ta kara da cewa an dakatar da rarraba wuta ga dukkannin kamfanonin rarraba wutar lantarki guda 11 (DisCos).

Source: Twitter
Rahoton ya ce wannan na nufin babu ko digon wutar lantarki da ke zuwa ga kamfanonin a wancan lokaci da turakun wutar suka fadi.
A lokacin da ake sa ran a shawo maganin wutar lantarki a shekarar nan ta 2026, sai ga shi daga shiga sabuwar shekarar ana ta samun matsala.

Kara karanta wannan
Badakalar fansho: Abdulrasheed Maina ya shaki iskar 'yanci bayan shekaru 8 a garkame
Lokacin kamfe, Bola Tinubu ya yi alkawarin zai dage wajen ganin wutar lantarki ya wadata.
Ina wuraren da rashin wuta ya shafa?
Bayanan sun nuna cewa DisCos da abin ya shafa sun hada da Abuja, Benin, Eko, Enugu, Ibadan, Ikeja, Jos, Kaduna, Kano, Port Harcourt da Yola.
Wannan jerin ya nuna cewa babu wani bangare na kasar nan da bai fuskanci katsewar wuta ba a lokacin da turakun suka samu matsala.
Wadannan kamfanoni su ne ke da alhakin rabar wutar lantarkin da suka sayo zuwa jihohin Najeriya.
TCN: Ana samun hasken wutar lantarki
A baya, kun samu labarin kamfanin TCN ya sanar da cewa an kai megawatt 5,713.6 na samar da hasken lantarki ranar 2 ga Maris, 2025, wanda ya zarce matsayin baya.
Amma kamfanin ya ce duk da haka, wannan ci gaba bai kai matsayin mafi girma da aka taba cimmawa na na megawatt 5,801.60 a shekarar 2021, inda wuta ta fara wadata.
Sanarwar da kamfanin ya fitar ta yi nuni da cewa duk da haka, an samu gagarumar nasara a tarihin samar da hasken wuta a Najeriy, yayin da kae fafutukar samun karin hasken wuta a sassa da dama.
Asali: Legit.ng
