Murna Ta Koma ciki: Dangote Ya Kara Farashin Litar Man Fetur a Najeriya

Murna Ta Koma ciki: Dangote Ya Kara Farashin Litar Man Fetur a Najeriya

  • Matatar Dangote ta sanar da kara farashin fetur bayan karewar bukukuwan ƙarshen shekara, inda ta ɗaga farashin zuwa N799 kan kowace lita
  • Sakamakon hakan, gidajen mai na MRS za su rika sayar da litar man fetur kan N839, kamar yadda sanarwar matatar Dangote ta bayyana
  • Matatar ta sanar da cewa matakin na da nufin tabbatar da daidaiton kasuwa da wadatar fetur a faɗin ƙasa ba tare da tsaiko ga kowa da kowa ba

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Lagos – Matatar Dangote ta ƙara farashin fetur daga N699 zuwa N799 kan kowace lita, bayan kammala bukukuwan ƙarshen shekara da kamfanin ya ce ya rage farashi domin rage wa ‘yan Najeriya nauyi.

Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da matatar ta fitar a daren Litinin, 26 ga Janairun 2026, inda ta bayyana cewa sabon tsarin farashin zai shafi sayarwa a matakin matatar da kuma a gidajen mai.

Kara karanta wannan

Jerin manyan sojoji 16 da hedkwatar tsaro 'ta gano' suna da hannu a shirin kifar da Tinubu

Motocin dakon mai da Alhaji Aliko Dangote
Motocin dakon mai a hagu, Aliko Dangote a dama. Hoto: Dangote Industries
Source: Facebook

Punch ta wallafa cewa sanarwar ta ce, gidajen mai na MRS za su rika sayar da fetur kan N839 kan kowace lita, bisa sabon daidaiton farashin da aka aiwatar.

Dalilin Dangote na kara farashin fetur

Matatar Dangote ta ce an yi wannan kari ne domin dawo da farashin zuwa matakin da zai dore a dogon lokaci, tare da jawo daidaito a kasuwa da sauƙin samun mai ga jama’a.

Gidan talabijin na Legas ya ce sanarwar ta ce:

“Bayan karewar lokacin bukukuwa, an kara farashin litar fetur domin daidaita kasuwa da sauƙin samu.”

Matatar ta tunatar da cewa a lokacin bukukuwan karshen shekara, ta ɗauki matakin rage farashi na wucin gadi domin taimaka wa ‘yan Najeriya a lokacin da kashe-kashen kudi ke ƙaruwa.

Tarihin rage farashi a matatar Dangote

A cewar matatar, wannan ne karo na biyu a jere da take ɗaukar nauyin rage farashi a lokacin bukukuwa, domin kare muradun ƙasa.

Kara karanta wannan

Dogara: Kiristan da aka ce zai maye Shettima a 2027 ya fito ya yi magana

A shekarar 2024, matatar ta ce ya taimaka wajen tallafin jigilar kaya, yayin da a 2025 ya rage farashin fetur domin sauƙaƙa wa jama’a.

Sai dai matatar ta nuna damuwa cewa duk da rage farashin a wancan lokaci, gidajen mai da dama ba su aiwatar da sabon farashin ba, lamarin da ya hana ‘yan Najeriya cin moriyar ragewar.

Yawan fetur da Dangote ke samarwa

Babban jami’in gudanarwa na matatar Dangote, David Bird, ya bayyana cewa matatar na ci gaba da samar da kusan lita miliyan 50 na fetur a kullum domin kasuwar cikin gida.

Ya ce ana ci gaba da fitarwa da rarraba fetur a duk faɗin ƙasa ba tare da matsala ba, inda ya tabbatar da cewa tsarin aiki na matatar na tafiya yadda ya kamata.

Matatar Dangote da ke jihar Legas
Wani sashe na matatar Dangote da ke Legas. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Dangote ya yi kyautar sama da N10bn

A wani rahoton, kun ji cewa Alhaji Aliko Dangote ya yi taron na musamman tare da manyan dillalan siminti na kamfaninsa a jihar Legas.

A yayin taron, Dangote ya raba wa dilolin kyautar motoci, kontenonin siminti, tsabar kudi da sauran kayayyakin da za su yi amfani da su.

Ya bayyana cewa kayayyaki da kudin da aka raba sun haura darajar Naira biliyan 10, yana mai cewa an yi haka ne domin karfafa dilolin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng