Jerin Manyan Sojoji 16 da Hedkwatar Tsaro 'Ta Gano' Suna da Hannu a shirin Kifar da Tinubu
- Hedkwatar tsaron Najeriya (DHQ) ta tabbatar da an yi yunkurin yi wa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu juyin mulki a shekarar da ta wuce
- Mai magana da yawun DHQ, Manjo Janar Samaila Uba ya ce kwamitin bincike ya mika rahoton abubuwan da ya gano game da lamarin
- Ya ce an gano laififfukan da sojoji 16 suka aikata ciki harda fara shirin kifar da gwamnati mai ci, wanda ya saba wa dokar gidan soja
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Hedkwatar tsaron Najeriya ta bayyana cewa, kwamitin bincike na musamman da ta kafa kan zargin yunkurin juyin mulki ya mika rahoto.
An kafa kwamitin ne domin bincikar jami’an sojoji 16 da ake zargi da rashin tarbiyya, saba wa ka’idojin aiki, da sauran laifuffuka.

Source: Facebook
Wane mataki zaa dauka kan sojoji 16?

Kara karanta wannan
Ta tabbata an yi yunkurin yi wa Tinubu juyin mulki, sojojin Najeriya sun fitar da bayanai
Hedkwatar sojojin ta kara da cewa yanzu haka jami’an za su fuskanci shari’a a gaban kotun soja, kamar yadda Vanguard ta rahoto.
Darakta yada labarai na hedkwatar tsaron Najeriya, Manjo Janar Samaila Uba, ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja.
Idan za a iya tunawa, hedikwatar tsaron (DHQ) ta sanar da kama wadannan jami’ai ne a watan Oktoban 2025 bisa zargin hannu a yunkurin hambarar da gwamnati mai ci.
Zargin kitsa juyin mulki
A yanzu kuma, Janar Uba ya tabbatar da cewa an kammala bincike kamar yadda tsarin aikin soja da dokoki suka tanada, kamar yadda Daily Trust ta kawo.
Janar Uba ya bayyana cewa binciken ya duba dukkan al'amuran da suka shafi ayyukan jami’an, inda aka gano cewa da dama daga cikin sojojin suna da laifuffukan da za su amsa a gaban kotu, ciki har da zargin kulla makircin kifar da gwamnati.
Jerin sojojin da za su fuskanci shari'a
Rahotanni sun nuna cewa jami’an da ake tsare da su sun hada da Birgediya-Janar daya, Kanal daya, Laftanal Kanal hudu, Manjo biyar da Kyaftin biyu.
Sauran sun hada da Laftanar daya, sai kuma Kwamanda daya daga Rundunar Sojin Ruwa da Squadron Leader daya daga Rundunar Sojin Sama.
Sunayen sojojin da ake zargi da hannu a shirin juyin mulkin sune:
1. Birgediya-Janar Musa Abubakar Sadiq daga Nasarawa
2. Kanal M.A. Ma’aji daga Neja
3. Laftanal Kanal S. Bappah Daga Bauchi
4. Laftanal Kanal A.A. Hayatu Daga Kaduna
5. Laftanal Kanal Dangnan daga Filato
6. Laftanal Kanal M. Almakura daga Nasarawa
7. Manjo A.J. Ibrahim daga Gombe
8. Manjo M.M. Jiddah daga Katsina
9. Manjo M.A. Usman daga Abuja
10. Manjo D. Yusuf daga Gombe
11. Manjo I. Dauda daga Jigawa
12. Kyaftin I. Bello (DSSC 43)
13. Kyaftin A.A. Yusuf
14. Laftanar S.S. Felix (DSSC)
15. Lieutenant Commander D.B. Abdullahi (Sojin Ruwa)
16. Squadron Leader S.B. Adamu (Sojin Sama)
Mafi yawan wadannan jami’ai mambobi ne na rukunin sojin kasa masu kula da sadarwa da masu kula da kayan yaki.

Source: Twitter
Sojoji sun mika rahoton bincike ga Tinubu
A wani labarin, kun ji cewa kwamitin da aka kafa ya mika wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu rahoton binciken da ya gudanar kan zargin wasu sojojin da yunkurin kifar da gwamnatinsa.
Majiyoyin sun bayyana cewa sama da watanni biyu aka kwashe ana.tsaurara tambayoyi da bincike mai zurfi a kan zargin, wanda DIA ta jagoranta.
Wata majiya da ke da masaniya kan binciken ta shaida cewa an.kammala aikin kuma an mika rahoton ga shugaban kasa.
Asali: Legit.ng

