Shugaba Tinubu 'Ya Amince' da Kirkiro Sabuwar Jiha 1 a Najeriya, An Bayyana Sunanta
- Alamu sun nuna cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da kirkiro jiha daya a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya
- Wasu majiyoyi daga fadar shugaban kasa ne suka bayyana hakan, sun ce Tinubu na duba yiwuwar share hawayen inyamurai
- An ce Tinubu ya fi aminta da kafa jihar Anioma, wacce Sanata Ned Nwoko na jihar Delta ke jagorantar fafutukar samar da ita
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Akwai alamun cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu na iya kirkiro karin jiha guda daya kacal bayan Majalisar Dokoki ta Kasa ta kammala gyaran kundin tsarin mulki.
An gano cewa jihar Anioma, wadda masu fafutukar samar da ita ke cewa za ta rage radadin jin ana mayar da yankin Kudu maso Gabas saniyar ware, ita ce ke kan gaba wajen samun wannan dama.

Kara karanta wannan
Ta tabbata an yi yunkurin yi wa Tinubu juyin mulki, sojojin Najeriya sun fitar da bayanai

Source: Facebook
Jaridar Vanguard ta tattaro a Abuja cewa tattaunawa da tuntubar juna ta yi nisa tsakanin masu ruwa da tsaki wajen shawo kan wadanda ke adawa da kirkirar jihar Anioma da sanya ta a Kudu maso Gabas.
Fafutukar Sanata Ned Nwoko
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Sanata Ned Nwoko ya sake jaddada kiran neman goyon baya daga al'ummar Inyamurai domin ganin an tabbatar da Anioma a matsayin jiha ta shida a shiyyar Kudu maso Gabas.
Idan za a tuna, an samu adawa mai karfi daga wasu kungiyoyi a jihar Delta wadanda ba sa son a cire Anioma daga jihar Delta a kaita Kudu maso Gabas.
Su wadannan kungiyoyin suna ganin cewa idan ma za a samar da jihar, to kamata ya yi ta tsaya a shiyyar Kudu maso Kudu, wanda hakan zai sa jihohin yankin su karu zuwa bakwai.
A halin yanzu, shiyyar Kudu maso Gabas tana da jihohi biyar ne kacal, wanda hakan ya sa ta kasance shiyyar da ta fi kowace karancin jihohi a Najeriya.

Kara karanta wannan
Juyin mulki: Sojoji sun mika rahoto kan jami'ai 16 da ake zargi ga shugaba Tinubu
Matsayar fadar shugaban kasa
Majiyoyi daga fadar shugaban kasa sun bayyana cewa jihar Anioma ce kawai ake duba yiwuwar kirkirowa da gaske, kuma za ta fito ne a matsayin jiha ta shida a Kudu maso Gabas.
A cewar majiyar, Shugaba Tinubu na shirin daukar wannan mataki ne da nufin magance korafe-korafen da aka dade ana yi na rashin daidaito.
Wata majiya ta ce:
"Da yiwuwar a samar da jihar Anioma domin cika muradin yankin Kudu maso Gabas da ma Inyamurai baki daya diyya.
"Shugaban kasa Tinubu na sane da dukkan hujjojin masu goyon baya da na masu adawa, amma yana kallon Anioma a matsayin wadda tafi kowace bukatar samar da jiha dacewa."

Source: UGC
Duk da cewa har yanzu ba a tantance ranar da Tinubu zai gana da masu ruwa da tsaki kan wannan batu ba, majiyoyi sun ce ganawar za ta zo ne bayan tuntubar jagororin Majalisa, wadanda ake ganin sun gamsu da ra'ayin, in ji PM News.
An yi yunkurin kifar da gwamnatin Tinubu
A wani rahoton, kun ji cewa rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da cewa an yi yunkurin yi wa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu juyin mulki a Najeriya.
A watan Oktoba, 2026, aka kama tare da tsare wasu dakarun sojoji bisa zargin hannu a kitsa shirin kifar da Shugaba Bola Tinubu, daga bisani aka kafa kwamitin bincike.
Rundunar bayyana cewa duk wadanda aka samu da laifi za a gurfanar da su a gaban kotun soji domin fuskantar shari’a daidai da Dokar Rundunar Soji da sauran ka'idojin aikin soja.
Asali: Legit.ng
