Ta Tabbata An Yi Yunkurin Yi Wa Tinubu Juyin Mulki, Sojojin Najeriya Sun Fitar da Bayanai
- Babbar hedkwatar rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da cewa an yi yunkurin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu
- Mai magana da yawun DHQ, Manjo Janar Samaila Uba ya tabbatar da cewa kwamitin bincike ya mika rahotonsa a wurin da ya dace
- A watan Oktoba, 2025 ne aka fara yada jita-jitar cewa hukumar DIA ta kama wasu sojoji bisa zargin kitsa juyin mulki a Najeriya
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da cewa an yi yunkurin yi wa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu juyin mulki a Najeriya.
A watan Oktoban 2025 ne aka samu rahoton cewa Hukumar Leken Asiri ta kasa (DIA) ta tsare wasu sojoji, da suka kunshi masu mukamin Kyaftin da Birgediya-Janar, bisa zargin yunkurin hambarar da gwamnatin Shugaba Tinubu.

Source: Twitter
An gama bincike kan zargin juyin mulki
A yau Litinin ne jaridar Daily Trust ta buga labarin yadda kwamitin da ya binciki jami’an da aka kama ya mika rahoton abubuwan da ya gano ga shugaban kasa.
A cikin wata sanarwa da ya fitar bayan mika rahoton, daraktan yada labarai na hedkwatar tsaro (DHQ), Manjo Janar Samaila Uba, ya tabbatar da cewa kwamitin ya mika rahotonsa a wurin da ya dace.
Janar Uba ya bayyana cewa duk wadanda aka samu da laifi za a gurfanar da su a gaban kotun soji domin fuskantar shari’a daidai da Dokar Rundunar Soji da sauran ka'idojin aikin soja.
“Rundunar Sojin Najeriya (AFN) tana sanar da jama’a cewa an kammala bincike kan wannan batu, kuma an aika da rahoton ga manyan hukumomin da suka dace kamar yadda doka ta tanada," in ji shi.
Rundunar Sojoji ta fara sakin bayanai
Sanarwar ta kara da cewa:

Kara karanta wannan
Juyin mulki: Sojoji sun mika rahoto kan jami'ai 16 da ake zargi ga shugaba Tinubu
"Binciken ya gano wasu jami’ai da ake zargi da kulla makircin kifar da gwamnati, wanda hakan ya saba wa dabi’u da ka’idojin aiki na jami'an rundunar sojin kasar nan.”
Kakakin DHQ ya bayyana cewa fitar da wannan bayani ga jama'a na nufin tabbatar da gaskiya tare da mutunta adalci da bin ka’idojin shari’a.

Source: Twitter
A cewarsa, rundunar soji za ta ci gaba da kasancewa mai biyayya da mutunta kundin tsarin mulkin Najeriya, kamar yadda jaridar Punch ta kawo.
Janar Uba ya karkare da cewa:
"Wadannan matakai da aka dauka na hukunci ne kawai, kuma wani sashi ne na matakan da gidan soja ke dauka don tabbatar da oda, tarbiyya, da ingancin aiki a tsakanin dakarunmu."
Halin da sojojin da aka kama ke ciki
A wani rahoton, kun ji cewa an fara rokon Shugaba Tinubu da gwamnatinsa su duba halin da sojojin da aka kama kan zargin kitsa juyin mulki ke ciki a wurin da aka kulle su.
Kungiyar mai rajin kare dimokuradiyya mai suna Concerned Pro-Democratic Activists of Nigeria ta bayyana damuwa kan halin da wasu jami’an soji da aka tsare ke ciki.
Ta ce wasu daga cikin jami’an da aka tsare tun Oktoban 2025 na fama da rashin lafiya mai tsanani, ba tare da samun kulawar likitoci yadda ya kamata ba.
Asali: Legit.ng
