'Yan Ta'adda Sun Take Yarjejeniyar Sulhu, Sun Afkawa Katsinawa
- Wasu 'yan ta'adda sun sake kai hari garin Dandume a jihar Katsina duk da yarjejeniyar zaman lafiya da aka kulla a kwanakin baya
- A wannan hari da suka kai, jami’an tsaro sun dakile shi cikin gaggawa wanda ya ceci rayukan bayin Allah da ke zaune a yankin
- Sai dai bayan an kora su daga Dandume, ‘yan bindigan sun kai mummunan hari Chibauna a Funtua, duka a cikin jihar Katsina
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Sabuwar matsala ta afkawa yankin Dandume da ke Karamar Hukumar Dandume a Jihar Katsina a daren Litinin, 25 ga watan Janairu, 2026.
Rahotanni daga mazauna yankin sun bayyana cewa jami’an tsaro sun kai dauki cikin hanzari, lamarin da ya tilasta wa maharan tserewa ba tare da sun yi mummunar barna ba.

Source: Facebook
Bakatsine ya wallafa a shafin X cewa abin da aka tabbatar shi ne sace babur guda daya kacal a yayin artabun.
Yadda sojoji suka dakile harin 'yan ta'adda
Sojojin kasar nan sun samu nasarar dakile harin da 'yan ta'adda suka kitsa kai wa Dandume bayan samun bayanan sirri.
A sakon da Bakatsine ya wallafa, ya ce:
“Martanin gaggawa da jami’an tsaro suka yi a Dandume ya hana faruwar abin da zai iya zama bala’i. Wannan ya nuna muhimmancin bayanan sirri da hadin kai da al’umma.”
Sai dai duk da wannan nasara, wasu mazauna Dandume sun shaida cewa har yanzu mutane na cikin fargaba, suna kwana cikin shiri.

Source: Twitter
Sun kara da kira ga gwamnati da ta kara tsaurara matakan tsaro musamman a hanyoyin da ke hada kananan hukumomi.
Wasu 'yan ta'adda sun afkawa gari a Katsina
Bayan ficewar 'yan ta'addan daga Dandume, rahotanni sun ce ‘yan bindigar sun sake haduwa tare da kai hari a kauyen Chibauna da ke Karamar Hukumar Funtua.
A nan ne aka ruwaito kisan fararen hula, sace wasu da dama, da kuma wawashe dukiyoyin jama’a.
Wannan lamari ya sake tayar da hankalin al’umma, musamman ganin cewa yankin na daga cikin wuraren da aka taba kulla yarjejeniyar zaman lafiya da ‘yan bindiga.
Majiyar ta kara da cewa:
“Abin tambaya yanzu shi ne: ta ya ‘yan bindiga ke yawo daga Karamar Hukuma zuwa wata ba tare da shinge ba? Kuma ina yarjejeniyoyin zaman lafiya suka dosa?”
'Yan ta'adda sun karya yarjejeniya a Katsina
A baya, mun wallafa cewa akalla mutane takwas ne suka rasa rayukansu bayan wasu ‘yan bindiga sun kai munanan hare-hare a wasu kauyuka a Dandume da ke Katsina.
Rahotanni sun nuna cewa harin ya faru ne da daren ranar Laraba, 21 ga watan Janairu, 2026, lokacin da yawancin jama’a ke shirin kwanciya barci
Shaidun gani da ido sun bayyana cewa maharan sun shiga kauyukan ne cikin duhun dare, suna harbi ba tare da nuna tausayi ba, hakan ya jefa jama’a cikin mummunar firgici.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

