Wasu 'Yan Kasuwa 4 Sun Fada Tarkon 'Yan Bindiga a Hanyar Dawowa Gida a Kaduna
- Yan bindiga sun tare wasu sanannun yan kasuwa hudu a karamar hukumar Kajuru ta jihar Kaduna, sun tafi da su cikin daji
- Rahotanni sun nuna cewa yan kasuwar sun fada hannun yan bindigar ne a hanyarsu ta dawowa daga kasuwar Moro
- Wani jami'in gwamnatin Kaduna da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce za su fitar da sanarwa da zaran sun kammala tattara bayanai
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kaduna, Nigeria - A kalla 'yan kasuwa hudu ne wasu mahara suka yi garkuwa da su yayin da suke hanyar komawa gida bayan sun yi sayayya a kasuwar Maro da ke karamar hukumar Kajuru a jihar Kaduna.
Wata majiya da ta tabbatar da faruwar lamarin ta bayyana cewa, lamarin ya faru ne a yammacin ranar Juma’a sa’ilin da mutanen ke dawowa daga kasuwar Maro.

Source: Original
Yadda maharan suka tare yan kasuwa
Jaridar Leadership ta ruwaito cewa 'yan bindigar sun yi wa 'yan kasuwar kwanton bauna a hanyar Maro zuwa Kajuru, suka tattara su suka yi awon gaba da su zuwa cikin daji.
Wannan sabon harin garkuwa da mutane na zuwa ne yayin da ake ci gaba da kokarin ceto fiye da mutane 100 da aka sace a Kurmin Wali, shi ma a cikin karamar hukumar Kajuru.
Lamarin ya faru ne yayin da miyagun 'yan bindiga suka shiga coci guda uku, lokacin da jama'a suka taru domin yin ibadar karshen mako a ranar Lahadin da ta gabata.
Martanin shugaban CAN da gwamnati
Yayin da yake zantawa da wakilin The Nation ta wayar taraho, Shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) reshen Arewa, Rabaran John Hayab, ya bayyana cewa bai riga ya samu cikakken tabbaci kan lamarin ba.
Amma duk da haka, ya yi kira ga gwamnati da hukumomin tsaro da su bi sawun miyagun 'yan bindigar da suka sace wadannan 'yan kasuwa.
"Muna kira ga gwamnati da ta jajirce wajen kakkabe miyagun mutanen da ke son haddasa matsala a jihar nan. Wasu mutane suna son haifar da rudani ne kawai," in ji shi.
Gwamnatin Kaduna na shirin sakin bayanai
A daya bangaren kuma, wani babban jami’in gwamnati da ya bukaci a sakaya sunansa, ya bayyana cewa yana jiran samun cikakken bayani kafin ya yi magana a hukumance.
Jami'in ya nuna taka-tsantsan ne domin guje wa raddi irin na harin Kurmin Wali da aka taba musantawa a baya.
"Kun tuna abin da ya faru game da batun Kurmin Wali. Na tattauna da shugabannin tsaro kan wannan sabon lamarin, kuma ina jiran tabbaci daga gare su kafin fitar da sanarwa. Ku ba ni lokaci kadan, zan yi bayani dalla-dalla," in ji shi.

Source: Facebook
Har zuwa lokacin hada wannan rahoton, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, DSP Mansir Hassan, bai amsa kiran waya ko dawo da kiran da aka yi masa ba.
Yan bindiga aun kashe malami a Kaduna
A wani rahoton, kun ji cewa malamin addinin Musulunci, Alaramma Bello Abubakar, wanda ke tafsirin Alƙur’ani a masallacin JIBWIS ya rasa ransa a hannun yan bindiga a Kaduna.
Lamarin ya faru ne a unguwar Layin Dan’auta a karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna lokacin da malamin ya ci karo da ‘yan bindiga.
Jihar Kaduna na daga cikin jihohin Arewa da ke fama da matsalolin tsaro da hare-haren yan bindiga wanda ke jawo asarar rayuka da dukiyoyin al'umma.
Asali: Legit.ng


