Daga Fitowa Gida, 'Yan Boko Haram Sun Harbe Malamin Addini da Jami'an Tsaro Har Lahira

Daga Fitowa Gida, 'Yan Boko Haram Sun Harbe Malamin Addini da Jami'an Tsaro Har Lahira

  • 'Yan ta'adda da ake zargin mayakan Boko Haram ne sun hallaka wani Fasto da mafarautan da suka kokarin fafatawa da su a jihar Borno
  • Shugaban mafarauta da 'yan banga na shiyyar Arewa maso Gabas, Mallam Shawulu Yohanna ya ce maharan sun harbe mutane biyar har lahira a harin
  • Ya ce 'yan ta'addan sun shiga kauyen Tarfa da ke karamar hukumar Biu da misalin karfe 4:00 na yammacin ranar Laraba da ta gabata

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Borno, Nigeria - Miyagun 'yan ta’addan Boko Haram sun kashe wani malamin addini, mafarauta biyu, da wasu fararen hula a kauyen Tarfa da ke cikin karamar hukumar Biu a jihar Borno.

Kauyen Tarfa wani yanki ne mai nisa a Biu wanda yake iyaka da karamar hukumar Hawul ta jihar ta Borno.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sake kai hari a Katsina, an kashe jami'an tsaro

Jihar Borno.
Taswirar jihar Borno a Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Shugaban mafarauta da 'yan banga na shiyyar Arewa maso Gabas, Mallam Shawulu Yohanna, ya tabbatar da kai hari wannan kauye, kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto.

Boko Haram ta kashe mutum 5 a Borno

Mallam Shawulu ya bayyana cewa 'yan ta'addan sun kai wannan farmaki ne da misalin karfe 4:00 na yammacin ranar Laraba da ta gabata, inda suka bude wuta kan mai uwa da wabi.

"Abun takaici ne yadda wasu 'yan ta'adda suka far wa kauyen Tarfa na karamar hukumar Biu a ranar Larabar da ta gabata.
"Na samu labarin cewa an kashe jami'an runduna ta guda biyu, da kuma wani Fasto na cocin E.Y.N da kuma wasu fararen hula da ba ruwansu mutum biyu," in ji shi.

Mafarauta sun tari mayakan Boko Haram

Ya bayyana cewa wasu mafarauta su shida da ke aiki a karkashinsa sun yi kokarin artabu da 'yan ta'addan, amma maharan sun fi karfinsu da makamai, hakan ya sa suka rinjaye su.

Kara karanta wannan

Kotu ta hukunta makiyayan da suka saki dabbobi a gonakin manoma

A cewar shugaban rundunar mafarautan, maharan sun shiga garin ne a lokacin da mafi yawan jama'a suka dawo daga gona bayan girbin gyada, wake, da sauran amfanin gona.

"Shi marigayi Faston (ba a bayyana sunansa ba) ya dawo daga gona ne da misalin karfe 4:00 na yamma, ya tsorata da ya fara jin karar harbe-harbe, yana fitowa waje daga gidansa sai 'yan ta'addan suka harbe shi ya mutu," in ji Shawulu.
Babagana Zulum.
Gwamnan jihar Barno, Farfesa Babagana Zulum na ganawa da majalisar zartarwa ta jiha Hoto: @ProfZulum
Source: Original

Yunkurin jin ta bakin mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Borno, ASP Nahum Kenneth Daso, ya ci tura domin layin wayarsa ba ya shiga, sannan bai amsa sakonnin da aka tura masa ba, in ji Vanguard.

Sojoji sun ragargaji 'yan Boko Haram

A wani labarin, kun ji cewa dakarun sojoji sun samu gagarumar nasara bayan kutsawa cikin yankin Timbuktu Triangle, wani yanki da ake dangantawa da Boko Haram da ISWAP.

Kara karanta wannan

Majalisar dattawa ta tabo batun kisan matar aure da 'ya'yanta a Kano

Rahoton ya bayyana cewa hare-haren da sojojin suka kai sun janyo mummunar asara ga cibiyoyin ‘yan ta’adda tare da raunana hanyoyin sadarwarsu.

Sojojin suk kuma gano kaburburan da ke dauke da gawar ‘yan ta’adda kimanin 20, wadanda aka kashe a yayin artabu a Timbuktu Triangle.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262