'Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari a Katsina, an Kashe Jami'an Tsaro
- Tsagerun 'yan bindiga dauke da makamai sun kai wani harin ta'addanci a jihar Katsina da ke yankin Arewa maso Yammacin Najeriya
- Harin wanda 'yan bindigan suka kai a cikin dare lokacin da mutane ke kwance a gidajensu, ya jawo asarar rayukan mutanen da ke taimakawa wajen samar da tsaro
- Rundunar hadin gwiwa ta tsaro ta kara daura damarar ci gaba da sintiri a yankin da lamarin ya auku domin hana sake aukuwar wani hari makamancinsa a nan gaba
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Katsina - 'Yan bindiga sun hallaka jami'an tsaro guda uku yayin wani hari da suka kai a jihar Katsina.
'Yan bindigan sun kai harin ne a kauyen Kauran Pawa Mahuta C, da ke karamar hukumar Dandume a jihar Katsina.

Source: Facebook
Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.
'Yan bindiga sun kai hari a Katsina
Lamarin ya faru ne da tsakar daren Laraba, da misalin karfe 12:24 na dare, lokacin da maharan dauke da makamai suka mamaye ƙauyen.
Rundunar tsaro ta haɗin gwiwa, wadda ta kunshi ‘yan sanda, sojoji da kuma C-Watch, ta yi artabu da ‘yan bindigan na wani lokaci mai tsawo, lamarin da ya tilasta musu tserewa.
'Yan bindiha sun kashe 'yan sa-kai
Mutane ukun da aka kashen dai jami'an tsaro ne na 'yan sa-kai wadanda ke taimakawa wajen yaki da tsagerun 'yan bindiga.
An bayyana sunayen waɗanda suka rasu sakamakon harin 'yan bindigan da Yahaya Sa’adu mai shekaru 37, Yahaya Yahaya mai shekaru 33, da Mika Musa mai shekaru 43, dukkansu mazauna ƙauyen Mahuta C.
An garzaya da mutanen da aka harba zuwa asibitin gwamnati na Dandume, inda likitoci suka tabbatar da rasuwarsu.
Hukumomi sun tabbatar da cewa ana ci gaba da farautar waɗanda suka aikata harin domin cafke su, yayin da rundunonin tsaro na haɗin gwiwa ke ci gaba da sintiri a yankin domin hana sake afkuwar irin wannan hari.

Source: Original
Karanta karin wasu labaran kan 'yan bindiga
- Amarya, kawayenta da aka sace awanni kafin aurenta sun kubuta daga 'yan bindiga
- 'Yan bindiga sun yi wa sojoji kwanton bauna a Zamfara, an samu asarar rayuka
- 'Yan bindiga sun yi wa shugaban karamar hukuma, jami'an tsaro kwanton bauna a Zamfara
- 'Yan bindiga sun kutsa wuraren ibada a Kaduna, an sace mutane sama da 100
'Yan bindiga sun kashe mutane a Plateau
A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga dauke da makamai sun kai harin 'ta'addanci a karamar hukumar Jos ta Kudu ta jihar Plateau.
'Yan bindigan sun kai harin ne a wani wurin da ake hakar ma'adanai ba bisa ka'ida ba da ke yankin Kuru da ke karamar hukumar Jos ta Kudu.
Binciken farko ya nuna cewa 'yan bindiga sun kashe mutum bakwai masu hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba, kuma mutanen sun zauna a wurin ne har tsakar dare.
Asali: Legit.ng

