An Samu Miliyoyi: Abba Hikima Ya Mika Kudin da Aka Tara wa Haruna Bashir
- Lauya Abba Hikima ya bayyana cewa an tara miliyoyi domin taimaka wa Malam Haruna Bashir bayan kisan matarsa da ’ya’yansa shida
- Hikima ya ce an miƙa dukkan kuɗin cikin asusun banki tare da yi wa wadanda suka taimaka addu'o'i da fatan alheri
- Daga cikin gudunmawar da aka samu, Injiniya Usman Ahmad Zun-Noorayne ya kawo Naira miliyan 3.4 da ya tattara daga al’umma
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Lauya Abba Hikima ya bayyana miliyoyin da aka samu bayan fara neman gudunmawa ga Haruna Bashir wanda ya shiga mummunan yanayi.
Malam Haruna Bashir shi ne wanda aka hallaka matarsa mai suna Fatima Abubakar da 'ya'yanta guda shida da tsakar rana a cikin gidansu.

Source: Facebook
Kisan gilla: An tara miliyoyi ga Haruna Bashir
Lauya Abba Hikima ya bayyana haka ne a yau Juma'a 23 ga watan Janairun 2026 a shafinsa na Facebook inda ya yabawa al'umma game da kokarin da suka yi.
Hikima ya ce a yan kwanakin da aka yi ana tara kudin, an samu N25m wanda aka rika tura cikin asusun bankinsa da kuma wasu hanyoyi da aka tara kudin.
"Alhamdulillahi. A cikin waɗannan kwanaki, mun tattara kuɗi Naira Miliyan 25 a cikin asusuna kuma, yau kwana 6 da wannan rasuwa, na miƙa wannan amana taku ga Mal. Haruna Bashir kai tsaye cikin asusun bankin sa.
"Na ba shi kwafin shige da ficen kudi na asusuna sannan mun je bankinsa domin rufe asusun nashi domin tsare masa wannan kuɗi har sai abubuwa sun lafa. "

Source: Facebook
Yadda aka samu N25m daga al'ummar Najeriya
Abba Hikima ya ce daga cikin kudin da aka tara, akwai wani Injiniya Usman Ahmad Zun-Noorayne ya tura masa bayan samu daga wurin jama'a.
Ya ce sun tura kudin a banki a yau Juma'a saboda rashin aiki gobe Asabar 24 ga watan Janairun 2026 da muke ciki.
Daga karshe, ya yi addu'ar Ubangiji ya saka wa kowa da alheri tare da rokon Allah ya tsare masa dukiya ya albarkace ta.
"Daga cikin wannan kuɗi, akwai N3,400,000 da Injiniya Usman Ahmad Zun-Noorayne ya tura min wadda ita ma a wajen al’umma ya tattara. Mun tura wannan kudi yau saboda rashin aikin banki gobe Asabar.
"Allah ya sakawa kowa da alkhairi. Allah ya tsare masa wannan dukiya. ya albarkace shi. Ameen."
- Abba Hikima
Kisan gilla: Lauya ya ja hankalin mutane
A baya, mun ba ku labarin cewa wani lauya a Kano ya ce kiran a gaggauta kashe masu laifin kisan uwa da ’ya’yanta shida ya saɓa wa dokokin Najeriya.
Ya bayyana cewa dole ne kotu ta samu wanda ake zargi da laifi, tare da kammala dukkan matakan ɗaukaka ƙara, kafin hukuncin kisa.
Lauyan ya gargadi jama’a kan ɗaukar doka a hannu, yana mai cewa dole ne a bar shari’a ta bi ƙa’ida duk da tsananin laifi.
Asali: Legit.ng

