Daga Barin Kurkuku, AbdulRasheed Maina Ya Fara Tone Tone kan Abubakar Malami
- Tsohon Shugaban kwamitin gyara fasalin fansho, Abdulrasheed Maina ya yi magana game da zargin da hukumomi ke yi wa Abubakar Malami
- Ya ce kadarorin da ake alakanta wa Abubakar Malami SAN ba su kai kashi daya cikin hudu na abin da aka yi zargin ya wawure ba
- Maina ya yabawa gwamnatin yanzu kan rikon gaskiya da bin doka, sabanin gwamnatin baya bayan an sako shi daga gidan yari
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Abdulrasheed Maina, tsohon shugaban Kwamitin Shugaban Kasa kan gyaran fansho, ya bayyana akwai kadarori masu tarin yawa a hannun Abubakar Malami SAN.
Ya ce kadarorin da hukumomi suka danganta tsohon Ministan Shari’a da handame wa, ba su kai ko kusa da rabin abin da aka yi zargin wawurewa ba.

Kara karanta wannan
Badakalar fansho: Abdulrasheed Maina ya shaki iskar 'yanci bayan shekaru 8 a garkame

Source: Twitter
Jaridar The Cable ta wallafa cewa A cewarsa, abin da aka gano zuwa yanzu bai kai kashi daya cikin hudu na dukiyoyin da ake zargin an karkatar ba.
AbdulRasheed Maina ya taso Malami a gaba\
Business day ta ruwaito cewa AbdulRasheed Maina ya fadi hakan ne yayin da yake karbar lambar yabo ta R'ule of Law and Courage Award' daga Kungiyar Lauyoyin Najeriya (NBA) a Abuja.
Ya ce hukumomi sun fara ne kawai, amma akwai sauran dukiyoyi masu yawa da har yanzu ba a gano ba, yana mai jaddada cewa ya kamata a ci gaba da bincike.
AbdulRasheed Maina ya yabawa gwamnatin da ke mulki a yanzu bisa yadda take tafiyar da lamarin, yana mai cewa tana nuna gaskiya, rikon amana da bin doka.
A ganinsa, tsarin da ake a kai yanzu ya saba da yadda al’amura suka kasance a karkashin gwamnatin baya ta marigayi Shugaba Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan
Binciken makamai: Malami na tsaka mai wuya a hannun hukumar DSS, ya fito ya yi magana
A cewarsa, matakan da ake dauka yanzu suna nuni da aniyar tabbatar da adalci da gaskiya a harkokin mulki.
Maina ya magantu kan gwamnatin Buhari'
Ya yi zargin cewa manyan jami’an gwamnati a wancan lokaci, ciki har da marigayi Shugaba Muhammadu Buhari sun roke shi ya dawo gida Najeriya.

Source: Facebook
AbdulRasheed Maina ya ce tsohuwar Ministar Kudi Kemi Adeosun, tsohon Mashawarcin Tsaron Kasa Babagana Monguno, da kuma Abubakar Malami, sun je Abu Dhabi domin rokon sa ya dawo Najeriya.
A cewarsa, ya ki amincewa da bukatar tasu, inda ya ce daga bisani suka koma Najeriya suka matsa wa mahaifiyarsa lamba domin ta shawo kansa ya dawo.
Ya bayyana cewa wannan ya faru ne saboda tsohon Shugaba Goodluck Jonathan ya sanar da su rawar da ya taka wajen kwato kudin Naira tiriliyan 1.63 a lokacin mulkinsa.
AbdulRasheed Maina ya fito daga kurkuku
A baya, mun wallafa cewa Abdulrasheed Maina, tsohon shugaban Kwamitin Gyaran Tsarin Fansho da aka rushe (PRTT), ya samu ‘yanci daga gidan yari bayan shafe shekaru takwas a daure.
An tsare Maina a cibiyar gyaran hali ta Kuje da ke Abuja, babban birnin tarayya, inda yake zaman daurin da kotu ta yanke masa bayan kama shi da laifin handame kudin 'yan fansho.
Har yanzu dai hukumomin da abin ya shafa ba su fitar da sanarwar hukuma da ke bayani dalla-dalla kan yadda aka aiwatar da sakin ba bayan aika shi kurkuku da kotu ta yi a 2021.
Asali: Legit.ng
