Soyayya Ta Rikide: Budurwa Ta Yi Wani Irin Mutuwa bayan Ziyartar Saurayi a Abuja
- Wani saurayi a birnin Abuja ya shiga tashin hankali bayan mutuwar budurwarsa da ta kawo masa ziyara na musamman
- Matar ta rasu a Abuja a ranar Laraba bayan ziyarartar saurayinta a Dei-Dei, inda aka ce ta fara amai bayan cin abinci
- Rahoto ya ce saurayin ne ya kira ’yan uwanta da dare, ya bayyana cewa ta mutu a asibitin Kubwa yayin da ake yi mata magani
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja – An ruwaito mutuwar wata mata mai suna Esther bayan ta kai ziyara gidan saurayinta a birnin tarayya Abuja.
Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne a ranar Laraba 21 ga watan Janairun shekarar 2026 a unguwar Dei-Dei da ke birnin.

Source: Twitter
Yadda Esther ta rasu a gidan saurayi
Wani mazaunin yankin mai suna Dauda ya bayyana wa Punch cewa Esther ta bar gida a ranar Laraba 21 ga watan Janairun 2026 domin ziyartar saurayinta.

Kara karanta wannan
Badakalar fansho: Abdulrasheed Maina ya shaki iskar 'yanci bayan shekaru 8 a garkame
Ya ce daga baya a cikin dare, saurayin ya kira babban yayanta ya sanar da shi cewa Esther ta rasu.
Dauda ya ce saurayin ya bayyana masa cewa ya saya wa Esther abinci ne, amma bayan ta ci abincin sai ta fara amai.
Ya ce saurayin ya garzaya da ita zuwa Asibitin Kubwa, inda ta rasu yayin da ake kokarin yi mata magani.
Dauda ya kara da cewa tun bayan sanar da mutuwar budurwar mai suna Esther, saurayin ya kashe wayarsa tare da wayar Esther, kuma har yanzu ba a san inda yake ba.
Ya ce:
“Esther ta bar gida da rana a ranar 21 ga Janairu, 2026, ta shaida wa ’yar uwarta cewa za ta je banki a Dei-Dei. Amma ba ta sake dawowa gida ba.
“Daga bisani a daren ranar, babban yayanta ya samu kira daga wani mutum da bai bayyana sunansa ba, wanda ya ce shi ne saurayin Esther ya saya mata abinci, bayan ta ci sai ta fara amai, hakan ya sa ya kai ta Asibitin Kubwa, inda ta rasu."

Kara karanta wannan
Kaduna: Gwamna ya sha alwashi, zai ceto mutum sama da 170 da 'yan ta'adda suka sace

Source: Original
Abin da 'yan sanda suka ce kan lamarin
Da wakilin Legit Hausa ya tuntubi Jami’ar hulda da jama’a ta rundunar ’yan sandan Abuja, Josephine Adeh, ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce rundunar tana ci gaba da bincike.
Ta ce:
“Mun san da faruwar lamarin kuma muna gudanar da bincike.”
Ta tabbatar da cewa idan an kammala bincike za ta waiwayi yan jarida domin su san halin da ake ciki.
Lamarin ya haifar da ce-ce-ku-ce a tsakanin jama’a, yayin da ake jiran sakamakon binciken ’yan sanda domin gano gaskiyar abin da ya faru da Esther, cewar Leadership.
'Yar Amurka ta mutu yayin ziyartar 'dan Najeriya
Kun ji cewa yan sanda sun fara bincike kan mutuwar da wata 'yar Amurka ta yi lokacin da ta zo Najeriya domin haduwa da saurayinta.
Matar yar shekara 60 a duniya, Jacqueline Bolling Elton ta mutu ne a asibiti bayan ta kamu da rashin lafiyar da har lokacin rahoton ba a gano ba.
Rundunar Yan Sanda ta ajiye gawar matar a dakin ajiyar gawarwaki na asibitin Warri, ta kuma kama saurayin mamaciyar.
Asali: Legit.ng