El Rufai Ya Saka Ayar Tambaya kan Yadda Ake Yaki da Cin Hanci da Rashawa a Najeriya
- Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya yi tsokaci kan yadda ake yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya
- Nasir El-Rufai ya zargi gwamnatin Najeriya da tafiyar da harkokin kasa ba tare da bin ka'ida ba, inda ya ce hakan na ds illa sosai
- Hakazalika, tsohon gwamnan ya bayyana cewa mutanen da ke bangaren adawa sun fi fuskantar barazana wajen yaki da cin hanci da rashawa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya zargi gwamnatin Najeriya da tafiyar da ƙasa ba tare da bin ka'ida ba.
Malam Nasir El-Rufai ya bayyana cewa ana gudanar da mulki ne ba tare da ɗaukar alhakin ayyuka yadda ya kamata ba.

Source: Twitter
Nasir El-Rufai ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a taron muhawarar Daily Trust karo na 23, wanda aka gudanar ranar Alhamis, 22 ga watan Janairun 2026 a birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan
Binciken makamai: Malami na tsaka mai wuya a hannun hukumar DSS, ya fito ya yi magana
Nasir El-Rufai ya koka kan yaki da cin hanci
El-Rufai ya yi gargaɗi kan abin da ya kira son kai wajen yaƙi da cin hanci da rashawa, yana mai cewa wannan dabara na raunana dimokuraɗiyya, lalata gaskiya da kuma rage amincewar jama’a ga gwamnati.
Ya bukaci a kawo ƙarshen tsare mutane ba tare da cikakken bincike ba, yana mai gargadin cewa kama mutane babu hujja da tsare su na dogon lokaci ya zama ruwan dare.
Tsohon gwamnan na Kaduna ya kuma ce ana amfani da dabarar cafke mutane ne a matsayin hanyar tsoratarwa, ba don neman adalci ba.
El-Rufai ya nuna damuwa kan abin da ya bayyana a matsayin son kai wajen gurfanarwa, musamman ga mutanen da ake ganin suna sukar gwamnati ko kuma adawa da ita.
Ya ce irin waɗannan ayyuka suna take ’yancin ɗan Adam na kuma suna raunana tubalin dimokuraɗiyya a hankali.
El-Rufai ya yi zargi kan gwamnatin Najeriya
Tsohon gwamnan ya kuma zargi gwamnati da kare masu cin hanci da rashawa da ke cikin masu mulki, yana mai bayyana halin da ake ciki a matsayin “mulki ba tare da bin ka'ida ba".
Ya ce yawanci ana bin zargin cin hanci da tsanani ne ga ’yan adawa, yayin da waɗanda ke kusa da mulki ake watsi da su ko kuma a bar su, su sasanta kansu ta hanya daban.
A cewarsa, ba a tuhumar 'yan APC da rashin gaskiya sannan ana amfani da yakin wajen muzguna wa 'yan adawa da kuma kokarin jawo mutane sun shigo jam'iyya mai-ci.
“Ana tafiyar da mulki ba tare da bin ka'ida ba. Muna gudanar da zaɓe, muna kafa hukumomi, muna sanar da kwato kadarori, amma daftarin mulki yana ci gaba da kasancewa abin da ake jingina da shi ne kawai."
"Cin hanci ya zama abu mai haɗari ga wasu da ke cikin adawa, abin tattaunawa ga waɗanda ke tsaka-tsaki kuma suke son komawa APC. Ba a zargin 'yan APC da cin hanci.”
- Nasir El-Rufai

Source: Twitter
Tsohon gwamnan Kaduna ya ba da shawara
Ya yi kira ga shugabannin siyasa, kungiyoyin fararen hula da al’umma gaba ɗaya da su matsa lamba domin a aiwatar da gyare-gyare.
El-Rufai ya ce kawo karshen tsare mutane ba tare da bincike ba da kuma aiwatar da dokokin yaƙi da cin hanci ba tare da nuna bambanci ba, wajibi ne ta fuskar doka.
A 'yan kwanakin nan an ji yadda EFCC da DSS suka tsare Abubakar Malami wanda ya yi minista na kusan shekaru takwas a mulkin Muhammadu Buhari.
El-Rufai ya yabi gwamnatin Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya yabawa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
El-Rufa'i ya yi yabon ne bisa matakin da gwamnatin tarayya ta ɗauka kan yaƙi da garkuwa da mutane, na kin ba da kudin fansa.
Tsohon gwamnan ya bayyana cewa ya kamata a karfafa wa gwamnati gwiwa a kan wannan mataki, domin hakan zai taimaka wa Najeriya wajen yaki da tsaro.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

