Shugaba Tinubu Ya Fadi Halin da Yake Ciki kan Gudanar da Mulkin Najeriya

Shugaba Tinubu Ya Fadi Halin da Yake Ciki kan Gudanar da Mulkin Najeriya

  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da sabon kwamitin gudanarwa na hukumar FCC mai kula da daidaito wajen al'amuran kasar nan
  • Mai girma Bola Tinubu ya nemi afuwa kan jinkirin da aka samu wajen rantsar da mambobin kwamitin gudanarwar na FCC
  • Shugaban kaar ya kuma bayyana yadda abubuwa suke yi masa yawa wajen gudanar da harkokin mulkin Najeriya

​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi magana kan gudanar da mulkin Najeriya.

Shugaba Tinubu ya bayyana cewa tafiyar da harkokin Najeriya aiki ne mai matuƙar nauyi, yana mai cewa ayyukan sun yi masa yawa.

Tinubu ya ce aikin Najeriya yana da girma sosai
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: @aonanuga1956
Source: Facebook

Jaridar The Punch ta ce Shugaba Tinubu ya faɗi hakan ne a ranar Alhamis, 22 ga watan Janairun 2026 yayin da yake ba da haƙuri kan jinkirin rantsar da sabon kwamitin gudanarwa na hukumar FCC.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya tura jakadu zuwa Amurka da wasu kasashen Turai 3

Me Tinubu ya ce kan mulkin Najeriya?

“Tabbas ina yi muku barka da rana. Da farko dai, ina ba ku haƙuri kan jinkirin wannan rantsuwa."
"Aikin wannan kasa yana da matukar nauyi, kuma ku ma kuna daga cikin waɗanda ke ɗauke da wannan nauyi.”

- Shugaba Bola Tinubu

Tinubu ya rantsar da mambobin FCC

A wajen bikin da aka gudanar a fadar shugaban kasa da ke Abuja, Shugaba Tinubu ya rantsar da shugabar FCC, Hajiya Hulayat Omidiran, tare da kwamishinoni 37 da ke wakiltar jihohi 36 da babban birnin tarayya, Abuja.

Yayin da yake kira ga sababbin mambobin da su yi riko da adalci, jajircewa, kishin kasa da aiki tukuru, Shugaba Tinubu ya bayyana FCC a matsayin hukuma mai muhimmanci.

Shugaba Bola Tinubu ya bayyana cewa aikin hukumar shi ne karfafawa da daidaita al'amuran Najeriya.

“Ƙasa da ke dogaro da ’ya’yanta ba ta da wata amana mafi alheri da ta wuce mutanenta. Muna da yawan jama'a, muna da ƙwarewa, karfi da baiwar da Allah Ya ba mu domin gina kasarmu.”

Kara karanta wannan

Atiku ya yi magana kan sace masu ibada a Kaduna, ya fadi kuskuren gwamnati

- Shugaba Bola Tinubu

Tinubu ya ba su shawara

Shugaba Tinubu ya bukaci sababbin jami’an da su rika tambayar kansu gudunmawar da za su bayar wajen ci gaba, bunkasa, kwanciyar hankali da haɗin kan Najeriya, jaridar The Sun ta kawo labarin.

"Dole ne mu rika tambayar kanmu a kowane lokaci, mene ne gudunmawarmu wajen ci gaba, bunƙasa, kwanciyar hankali da haɗin kan wannan ƙasa?”
"Ba lallai ne kullum mu rika tambayar abin da kasa za ta yi mana ba, a’a, mu tambayi kanmu abin da za mu yi wa kasa domin ta zama mafi girma.”

-Shugaba Bola Tinubu

Tinubu ya rantsar da mambobin kwamitin gudanarwa na hukumar FCC
Shugaba Bola Tinubu tare da shugabar hukumar FCC a wajen rantsuwar kama aiki Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

An ba Shugaba Tinubu tabbaci

Da take jawabi, Hajiya Hulayat Omidiran ta tabbatar wa shugaban kasa cewa hukumar za ta gudanar da aikinta bisa dokar kasa da kuma manufar Renewed Hope ta wannan gwamnati.

"Ina tabbatar wa Mai girma shugaban kasa cewa a karkashin jagorancina, hukumar za ta aiwatar da aikinta na kundin tsarin mulki yadda ya kamata, bisa manufar Renewed Hope."

Kara karanta wannan

Abubuwan da Abba Kabir ya tattauna da Tinubu ana maganar shigarsa APC

“A madadinmu baki ɗaya, muna alƙawarin karfafa amfanin bambancinmu, tare da farfaɗo da fata da burin ’yan Najeriya.”

- Hajiya Hulayat Omidiran

Tinubu ya tura jakadu zuwa kasashen waje

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da tura jakadu zuwa kasashen waje.

Shugaba Tinubu ya amince da tura Ambassada Ayodele Oke a matsayin jakandan Najeriya a kasar Faransa da ke nahiyar Turai.

Hakazalika, Mai girma Bola Tinubu ya amince da tura Kanar Lateef Are a matsayin jakandn Najeriya zuwa kasar Amurka.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng