'Yan Bindiga Sun Karya Yarjejeniyar Sulhu a Katsina, An Kashe Bayin Allah

'Yan Bindiga Sun Karya Yarjejeniyar Sulhu a Katsina, An Kashe Bayin Allah

  • 'Yan bindiga dauke da makamai sun yi aika-aika yayin da suka kai wasu hare-haren ta'addanci a jihar Katsina
  • Hare-haren dai an kai su ne cikin dare duk da yarjejeniyar sulhu da aka kulla da 'yan bindiga a yankin da lamarin ya auku
  • Mazauna yankin sun yi kira ga gwamnati da ta gaggauta daukar matakan da suka dace domin dakile matsalar rashin tsaro

​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Katsina - Akalla mutane takwas ne suka rasa rayukansu bayan wasu ’yan bindiga sun kai hare-hare a jihar Katsina.

'Yan bindigan sun kai hare-haren ne a wasu kauyuka na karamar hukumar Dandume ta jihar Katsina.

'Yan bindiga sun kai hare-hare a Katsina
Gwamna Dikko Umaru Radda sanye da kayan rundunar C-Watch Hoto: Dikko Umaru Radda
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ce hare-haren na 'yan bindiga sun faru ne da daren ranar Laraba, 21 ga watan Janairun 2026.

'Yan bindiga sun farmaki kauyuka a Katsina

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun farmaki masu hakar ma'adanai a Plateau, an samu asarar rayuka

Wadannan barna da aka yi sun shafi kauyukan Baraje, Kirijan, Shugu, Kauran Pawa da Unguwar Jika, yayin da akalla mutane 11 suka jikkata, jaridar The Punch ta zo da rahoton.

Shaidun gani da ido sun ce ’yan bindigan sun shiga kauyukan ne cikin duhun dare, suna harbe-harbe ba kakkautawa, lamarin da ya jefa jama’a cikin firgici.

An kuma ce an sace mutum daya yayin da aka lalata gidaje da shaguna tare da sace babura, wayoyin hannu da sauran kayayyaki masu amfani.

Wani mazaunin yankin ya ce:

“Muna cikin gida muna shirin kwanciya barci sai muka ji karar harbe-harbe. Sun lalata shaguna da gidaje, sannan suka tafi da babura, wayoyi da sauran kayayyaki.”

Mazauna yankunan sun bayyana hare-haren a matsayin hujja ta gazawar yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimmawa a jihar kwanan nan, inda suka bukaci gwamnati da hukumomin tsaro da su ɗauki matakan tsaro na gaggawa domin magance tabarbarewar tsaro.

Me hukumomi suka ce kan harin?

Ƙoƙarin jin ta bakin rundunar ’yan sandan jihar Katsina bai yi nasara ba, domin ba a samu damar tuntuɓar kakakin rundunar a lokacin hada wannan rahoto ba.

Kara karanta wannan

Yadda tubabbun 'yan bindiga suka taimaka aka kashe tsageru 50 a Katsina

Da aka tuntubi shugaban karamar hukumar Dandume, Bishir Sabi’u Gyazama, ya tabbatar da faruwar hare-haren, amma ya ki yin cikakken bayani, yana mai cewa yana kan hanyarsa ta dawowa daga Katsina.

Karamar hukumar Dandume ta na tsakanin Faskari, Danja da Sabuwa a yankin Kudancin jihar Katsina kuma ta na da kusanci da Birnin Gwari a Kaduna.

'Yan bindiga sun karya yarjejeniyar sulhu

Sai dai wani mazaunin kauyen Baraje, Malam Nura, ya bayyana cewa maharan sun iso kusan tsakar dare, suna haska fitilu tare da harbe-harbe cikin gidaje.

'Yan bindiga sun kashe mutane a Katsina
Taswirar jihar Katsina, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

A cewarsa, an riga an birne waɗanda aka kashe bisa tsarin addinin Musulunci, yayin da waɗanda suka jikkata ke karɓar magani a babban asibitin Funtua.

Mazauna yankunan da abin ya shafa sun nuna matukar damuwa kan sake ɓarkewar tashin hankalin.

Sun bayyana hare-haren a matsayin karya yarjejeniyar zaman lafiya da aka cimma a bara tsakanin ’yan bindiga da al’ummomin yankin, wadda ta tanadi zaman lafiya da haɗin kai.

Sun roki gwamnati da hukumomin tsaro da su kara kaimi wajen kare rayuka da dukiyoyi, tare da hana sake aukuwar irin waɗannan hare-hare.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kutsa wuraren ibada a Kaduna, an sace mutane sama da 100

'Yan bindiga sun kashe masu hakar ma'adanai

A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga dauke da makamai sun kai hari kan wani wurin da ake hakar ma'adanai a jihar Plateau.

'Yan bindigan sun kashe mutane takwas a harin da suka kai a wani wurin da ake hakar ma'adanai a karamar hukumar Jos ta Kudu.

Dakarun sojoji sun kai dauki zuwa wurin da lamarin ya auku, inda suka gano kwankon harsasan da 'yan bindigan suka yi amfani da su.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng