Ba a Gama da Kolmani ba, Tinubu Ya Amince da Sabon Aikin Hako Man Fetur

Ba a Gama da Kolmani ba, Tinubu Ya Amince da Sabon Aikin Hako Man Fetur

  • Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da fara hako man fetur a Tsibirin Tongeji da ke Ipokia, lamarin da ya buɗe sabon babi ga tattalin arzikin jihar Ogun
  • Gwamna Dapo Abiodun ne ya sanar da labarin a lokacin da ya karɓi jagororin rundunar sojin ruwa, inda ya nuna cewa matakin na da muhimmanci
  • Akwai rade-radin cewa tashar jiragen ruwa ta Olokola za ta canja yanayin safarar kaya da tsaro a yankin, amma cikakken tasirin hakan na nan tafe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Ogun – Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da fara ayyukan hako man fetur na kasuwanci a Tsibirin Tongeji da ke Karamar Hukumar Ipokia a Jihar Ogun.

Wannan bayani ya fito ne daga bakin Gwamnan Jihar Ogun, Dapo Abiodun, wanda ya ce amincewar ta zo ne tare da umarnin fara wani muhimmin aikin tashar jiragen ruwa da aka dade ana jira.

Kara karanta wannan

Kaduna: Gwamna ya sha alwashi, zai ceto mutum sama da 170 da 'yan ta'adda suka sace

Gwamnan jihar Ogun Dapo Abiodun a ofis
Gwamnan Ogun da sojojin ruwan Najeriya a ofishinsa. Hoto: Dapo Abiodun
Source: Facebook

Sakon da ya wallafa a X ya nuna cewa gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karɓi kwamandan rundunar sojin ruwa, Rear Admiral Abubakar Abdullahi Mustapha, tare da manyan jami’ansa.

Bola Tinubu ya amince da hako mai a Ogun

Gwamna Dapo Abiodun ya ce Shugaba Tinubu ya bayar da umarni kai tsaye na fara hako man fetur na kasuwanci a Tsibirin Tongeji, yana mai cewa nan gaba kaɗan al’umma za su fara ganin ayyuka na tafiya a yankin.

Ya bayyana cewa aikin hako man zai taimaka wajen haɗa al’ummomin gabar teku cikin manyan ayyukan tattalin arziki na ƙasa, tare da samar da damar aikin yi da ƙarfafa tattalin arzikin yankin.

A cewarsa, aikin na da matuƙar muhimmanci ga gwamnatin Najeriya, musamman ganin yadda zai taimaka wajen bunƙasa arzikin kasa.

Maganar tashar jirgin ruwa a jihar Ogun

Gwamnan ya kuma bayyana cewa Shugaba Tinubu ya amince da fara aiki nan take kan aikin tashar jirgin ruwan Olokola da ke karamar hukumar Ogun Waterside, bayan shekaru ana jira.

Kara karanta wannan

Bello Turji ya firgita a cikin daji, yana gudun neman tsira zuwa wurare

Ya ce tashar jiragen ruwa, wacce ke da darajar biliyoyin Daloli, za ta taimaka matuƙa wajen rage cunkoso a tashoshin jiragen ruwan Legas, tare da buɗe sabon hanyar safarar kaya ta gabar teku.

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu
Shugaba Bola Ahmed Tinubu lokacin da ya je Katsinai. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Abiodun ya ce Shugaban ƙasa ya nuna ƙwarin gwiwa cewa ya kamata aikin ya yi nisa sosai tsakanin yanzu da shekara mai zuwa, musamman ganin yadda hanyar bakin teku za ta zama wata muhimmiyar hanya ta jigilar kaya.

Sabuwar sunan tashar da batun tsaro

Gwamnan ya ƙara da cewa sabuwar tashar jiragen ruwan za ta kasance da suna Blue Marine Economic Zone, suna da ke nuni da muhimmancin wurin da kuma damar tattalin arziki da ke tattare da shi.

Ya yabawa Rundunar Sojin Ruwa ta Najeriya bisa kafa sansanin ayyuka a Tsibirin Tongeji, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen hana shige da fice ba bisa ƙa’ida ba daga Jamhuriyar Benin.

A nasa jawabin, Rear Admiral Abubakar Abdullahi Mustapha ya bayyana Jihar Ogun a matsayin wuri mai matuƙar muhimmanci ga tsaron ƙasa.

Maganar hako mai a Kolmani

A wani labarin, mun kawo muku cewa kamfanin man Najeriya na NNPCL ya bayyana cewa yana cigaba da aikin hako mai a Kolmani.

Kara karanta wannan

Kujerar Hajji, sabon gida da wasu kyaututtuka 3 da Gwamna Abba ya yi waijin Fatima

NNPCL ya kara da cewa a kokarin da ya ke na ganin aikin ya kammala, ya yi nasarar samo mai a rijiyoyi guda hudu da ya tona a wajen.

Ya bayyana cewa aikin zai habaka tattalin arzikin jihohin Gombe da Bauchi, Arewa maso Gabas, kasa baki daya wajen samar da ayyuka.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng