Amarya, Kawayenta da Aka Sace Awanni kafin Aurenta Sun Kubuta daga ’Yan Bindiga

Amarya, Kawayenta da Aka Sace Awanni kafin Aurenta Sun Kubuta daga ’Yan Bindiga

  • Wata amarya da kawayenta a Sokoto sun samu ‘yanci bayan kwanaki 49 a hannun ‘yan bindiga, bayan biyan kuɗin fansa Naira miliyan 10
  • An sace su ne sa’o’i kaɗan kafin bikin aure a ƙauyen Chacho da ke ƙaramar hukumar Wurno da ke jihar mai fama da matsalar rashin tsaro
  • Mazauna yankin sun nemi Gwamnatin Tarayya ta ɗauki tsauraran matakan tsaro da amfani da fasahar zamani wajen yaƙar ‘yan bindiga

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Sokoto - Wata amarya a Jihar Sokoto tare da kawayenta da aka sace su, sun samu ‘yanci bayan shafe kwanaki 49 a hannun ‘yan bindiga a cikin daji.

Rahotanni sun bayyana cewa an sace amaryar da kawayenta ne ‘yan sa’o’i kaɗan kafin bikin aurensu, a ƙauyen Chacho da ke ƙaramar hukumar Wurno ta Jihar Sokoto.

Kara karanta wannan

Makwabtan Fatima da aka kashe da yaranta 6 a Kano sun fusata rundunar 'yan sanda

Amarya ta kubuta daga yan bindiga bayan kwana 49 a hannunsu
Taswirar jihar Sokoto da ake yawan kai hare-haren yan bindiga. Hoto: Legit.
Source: Original

Amarya da kawayenta sun bar hannun 'yan bindiga

Majiyoyi daga yankin sun tabbatar da cewa an sake su ne bayan iyalansu sun biya kuɗin fansa Naira miliyan 10, tare da sababbin babura uku da wasu kayayyaki da ‘yan bindigar suka buƙata, cewar Tribune.

Al’ummar yankin sun ce wannan lamari ya lalata farin cikin ƙauyen gaba ɗaya, musamman ganin yadda shirye-shiryen biki suka kai kololuwa kafin satar ta faru.

Wani daga cikin dangin waɗanda aka sace, wanda ya buƙaci a ɓoye sunansa, ya ce lamarin ya jefa al’umma cikin tsoro da firgici, inda babu yadda mutanen ƙauyen marasa makamai za su iya kare kansu daga ‘yan bindigar.

Binciken bayanai ya nuna cewa an riƙe matan ne a wata maɓoyar ‘yan bindiga a cikin dazukan Sububu, waɗanda suka shafi wasu sassan ƙananan hukumomin Isa da Sabon Birni, har ma suna kaiwa Jihar Zamfara da Jamhuriyar Nijar.

An jima ana kallon dazukan Sububu a matsayin maɓoyar ‘yan bindiga da ke addabar al’ummomi a Sokoto, Kebbi da Zamfara.

Kara karanta wannan

Trump ya tsorata da barazanar kashe shi, ya yi alwashin shafe Iran a duniya

Yan bindiga sun sako amarya da kawayenta da suka sace a Sokoto
Ministan tsaron Najeriya, Christopher Musa. Hoto: HQ Nigerian Army.
Source: Facebook

Yawan kudi da aka ba 'yan bindiga

Wani ɗan uwan wadannan bayin Allah ya bayyana cewa saboda rashin ikon iyalin wajen cika buƙatun fansa da ‘yan bindigan ke ta sauyawa ya jawo suka dade a tsare a cewar Vanguard.

Ya ce tattaunawar fansa ta ɗauki makonni bakwai, inda daga ƙarshe aka biya Naira miliyan 10, aka ba da babura uku da aka kiyasta kuɗinsu kusan Naira miliyan 1.8 kowanne, tare da wasu kayan abinci.

Ya ce:

“Mu mutanen ƙauye ne. Ba mu da irin wannan kuɗi a gida ko a banki. Mun sayar da kayayyakinmu, dabbobi da dukiya, sannan muka roƙi mutane masu tausayi kafin mu iya tara kuɗin.”

Wani mazaunin yankin ya ce satar ta nuna irin wahalar da mutanen karkara ke fuskanta a kullum sakamakon laifuka masu tashin hankali da ke rusa rayuka da mafarkai.

Ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta samar wa jami’an tsaro kayan zamani domin gano ‘yan bindiga, yana mai cewa al’ummomi ba za su iya tinkarar wannan matsala su kaɗai ba.

Kara karanta wannan

Takarar 2027: Yadda ake son tada rikici a ADC da matakin da Atiku ya dauka

Harin Amurka ya rikita 'yan ta'adda a Sokoto

Mun ba ku labarin cewa hare-haren makaman Amurka a Sokoto sun janyo cece-kuce, inda ake cewa kungiyar Lakurawa ce aka kai wa hari.

Rahotanni sun nuna Lakurawa na kokarin guduwa daga Sokoto zuwa Nijar ko Chadi bayan an kashe sama da mutum 150.

Masana sun gargadi cewa hare-haren kasashen waje na iya kara tsananta tsaro da haddasa ramuwar gayya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.