'Ya Bindiga Sun Farmaki Masu Hakar Ma'adanai a Plateau, an Samu Asarar Rayuka

'Ya Bindiga Sun Farmaki Masu Hakar Ma'adanai a Plateau, an Samu Asarar Rayuka

  • 'Yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ta'addanci kan wani wurin hakar ma'adanai a jihar Plateau
  • Tsagerun 'yan bindigan sun hallaka mutanen da ke hakar ma'adanai bayan sun yi musu dirar mikiya da tsakar dare
  • Rundunar sojojin Najeriya ta bayyana abin da ta gani lokacin da dakarunta suka je wurim da lamarin ya auku a karamar hukumar Jos ta Kudu

​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Plateau - Rundunar sojojin Najeriya ta tabbatar da mutuwar mutane bakwai sakamakon wani harin dare da 'yan bindiga suka kai a jihar Plateau.

'Yan bindigan sun kai harin ne a wani wurin hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba a Capitex, yankin Kuru da ke karamar hukumar Jos ta Kudu a jihar Plateau.

'Yan bindiga sun kashe mutane a Plateau
Gwamnan jihar Plateau, Caleb Manasseh Mutfwang Hoto: @CalebMutfwang
Source: Facebook

Tashar Channels tv ta ce wata babbar majiya daga jami’an sojoji ta ce jami’an tsaro sun gano harsasai a wurin yayin da suke gudanar da bincike.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi wa sojoji kwanton bauna a Zamfara, an samu asarar rayuka

'Yan bindiga sun kai hari a Plateau

Harin ya faru ne da misalin ƙarfe 1:00 na dare a ranar Laraba, 21 ga watan Janairun 2026 lokacin da wasu da ake zargin ’yan bindiga ne suka kai farmaki wurin da nufin kwashe ma’adanai da aka hako ba bisa ƙa’ida ba.

Dakarun sashe na 6 na Operation Safe Haven (OPSH) sun samu labarin lamarin da misalin karfe 8:40 na safe ta hannun wani mazaunin yankin, inda nan take suka tashi zuwa wurin domin dawo da zaman lafiya.

“Dakarun sashe na 6 na Operation Safe Haven sun samu rahoto cewa an harbe masu hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba guda bakwai har lahira."
"An harbe su ne da misalin ƙarfe 1:00 ta hannun wasu da ake zargin ’yan bindiga ne a wani wurin hakar ma’adanai a Kuru, karamar hukumar Jos ta Kudu a jihar Plateau."

- Wata majiya

Sojoji sun amsa kiran gaggawa

Majiyar ta kara da cewa sojojin sun gano kwankon harsasai guda 10 masu kaurin 7.62mm da ake zargin maharan ne suka yi amfani da su.

Kara karanta wannan

Sojojin sama sun yi ruwan wuta kan 'yan ta'adda a Borno, an kashe tantirai da dama

“Da isowarsu wurin, dakarun sun duba yankin gaba ɗaya tare da gano kwankon harsasai guda 10 masu kaurin 7.62mm.

- Wata majiya

An kwashe gawarwakin waɗanda suka mutu zuwa asibitin kula da lafiya a matakin farko (PHC) da ke Dabwak, Kuru, domin yi musu rajista da kuma shirye-shiryen binne su daga iyalansu.

An kashe masu hakar ma'adanai ba bisa ka'ida ba

Binciken farko ya nuna cewa mamatan masu hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba ne, kuma sun zauna a wurin har tsakar dare, jaridar Leadership ta kawo labarin.

'Yan bindiga sun kai hari a jihar Plateau
Taswirar jihar Plateau, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Abin da suka yi ya saɓa wa haramcin da gwamnatin jihar Plateau ta kafa kan hakar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba da kuma hakar dare.

“Waɗanda abin ya shafa masu hakar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba ne, kuma sun zauna a wurin har dare, sabanin dokar da ta hana hakar dare da hakar ba bisa ƙa’ida ba a jihar Plateau."

- Wata majiya

Rundunar sojojin ta kuma bayyana cewa an jinkirta kai rahoton lamarin, inda ta danganta hakan tsoron fuskantar hukunci sakamakon dokar hana hakar ma’adanai da dare.

Kara karanta wannan

Yadda tubabbun 'yan bindiga suka taimaka aka kashe tsageru 50 a Katsina

'Yan bindiga sun kashe sojoji

A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga dauke da makamai sun yi wa dakarun sojoji kwanton bauna a jihar Zamfara.

Tantiran 'yan bindigan sun danawa dakarun sojojin tarko ne lokacin da suke dawowa daga wajen wani farmaki da suka kai a cikin daji.

Duk da kokarin da jami'an tsaron suka yi wajen fatattakar 'yan bindigan, an samu asarar rayukan sojoji biyar da dan sanda daya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng