Atiku ko Peter Obi: Baba Ahmed Ya Fadi Wanda Ya Dace Ya Samu Tikitin ADC a 2027

Atiku ko Peter Obi: Baba Ahmed Ya Fadi Wanda Ya Dace Ya Samu Tikitin ADC a 2027

  • Ana ci gaba da muhawara kan wanda zai zama dan takarar shugaban kasa a karkashin inuwar jam'iyyar hadaka ta ADC
  • Tsohon mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin siyasa, Hakeem Baba-Ahmed, ya shiga sahun masu yin magana kan batun
  • Hakeem Baba-Ahmed ya bayyana wanda ya fi cancanta a cikin 'yan siyasar da ke da niyyar yin takarar shugaban kasa a karkashin ADC

​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Tsohon mai ba shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu shawara kan harkokin siyasa, Hakeem Baba-Ahmed, ya yi magana kan Atiku Abubakar.

Hakeem Baba-Ahmed ya ce mafi girman gudummawar da Atiku zai iya bayarwa ga Najeriya ita ce ya janye daga duk wata niyya ta tsayawa takarar shugaban kasa a zaɓen shekarar 2027.

Hakeem Baba-Ahmed ya yi magana kan takarar shugaban kasa a 2027
Tsohon Mai ba shugaban kasa shawara, Hakeem Baba-Ahmed Hoto: Hakeem Baba-Ahmed
Source: UGC

Hakeem Baba-Ahmed ya bayyana hakan ne yayin da yake magana a shirin The Morning Show na tashar talabijin ta Arise News a ranar Alhamis, 22 ga watan Janairun 2026.

Kara karanta wannan

Tikitin ADC: Baba Ahmed ya samo mafita ga Peter Obi kan fafatawa da su Atiku, Amaechi

Hakeem Baba-Ahmed ya ba Atiku shawara

Ya ce idan Atiku ya yanke shawarar kin tsayawa takara a 2027, hakan zai aika da sako mai karfi ga ’yan Najeriya cewa akwai yiwuwar samun sabon tsarin siyasa, maimakon ci gaba da maimaita fitattun ’yan siyasa iri ɗaya.

“Daga cikin dukkan waɗannan abubuwa, dole ne a samu wani abu da Atiku da kansa zai iya yi. Ɗaya daga cikinsu shi ne ya daina nacewa cewa dole sai ya sake tsayawa takara. Kuma zan bayyana dalilaina."

- Hakeem Baba-Ahmed

Baba-Ahmed ya kara da cewa janyewar Atiku daga takara mataki ne da yake karkashin ikonsa gaba ɗaya, kuma hakan na iya sake fasalin siyasar adawa gabanin babban zaɓen mai zuwa.

Wa ya cancanci samun tikitin ADC?

Duk da roƙonsa ga Atiku da ya sake tunani kan takarar shugaban ƙasa, Baba-Ahmed ya bayyana cewa tsohon mataimakin shugaban kasar shi ne mafi cancanta daga cikin masu neman tikitin jam’iyyar ADC idan aka bi tsarin amfani da deliget.

Kara karanta wannan

2027: Alamu sun nuna wasu ministoci da hadimai za su rasa mukamansu a gwamnatin APC

Ya ce gogewarsa, tasirinsa a faɗin ƙasa, karfin tsarinsa da amintattun magoya bayansa sun ba shi fifiko a kan sauran masu takara a cikin jam’iyyar ADC.

“Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar yana da gogewa, yana da tasiri, yana da tsari mafi ƙarfi da magoya baya masu aminci, kuma ya fi fahimtar dabarun siyasar cikin gida na jam’iyya fiye da sauran."
"Tikitin ADC a buɗe yake, amma zai yi matuƙar wahala wani ya same shi ba tare da Atiku Abubakar ba."

- Hakeem Baba-Ahmed

Hakeem Baba-Ahmed ya yi suka

Har ila yau, ya soki masu kira da a tanadi tikitin jam’iyyar ga mutum guda, yana mai cewa irin wannan kiran ya saɓa wa ka’idojin dimokuraɗiyya.

“Waɗanda ke cewa dole ne a bai wa wani takamaiman mutum tikitin jam’iyya suna tafiya ne saɓanin tsarin dimokuraɗiyya."

- Hakeem Baba-Ahmed

Hakeem Baba-Ahmed ya ba Atiku Abubakar shawara
Hakeem Baba-Ahmed wanda ya taba zama mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin siyasa Hoto: Hakeem Baba-Ahmed
Source: Twitter

Duk da bayyana irin ƙarfinsa a cikin jam’iyyar, Baba-Ahmed ya sake jaddada kiran da yake yi wa Atiku da ya hakura da takarar shugaban ƙasa.

“Abu mafi muhimmanci da jam’iyyar ADC za ta iya yi, kuma babbar sadaukarwar da Atiku zai iya yi wa wannan ƙasa bayan duk shekarun da ya shafe yana aiki da kokarin gina dimokuraɗiyya, ita ce ya yanke shawarar kada ya sake tsayawa takarar shugaban kasa a 2027.”

Kara karanta wannan

Atiku ya yi magana kan sace masu ibada a Kaduna, ya fadi kuskuren gwamnati

- Hakeem Baba-Ahmed

Nwajiuba ya shiga sahun masu neman tikitin ADC

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon karamin Ministan ilmi, Emeka Nwajiuba, ya bayana aniyarsa ta neman takarar shugaban kasa a zaben 2027.

Tsohon Ministan kuma tsohon dan majalisar wakilan ya bayyana cewa zai tsaya takra ne karkashin inuwar jam'iyyar ADC mai adawa.

Emeka Nwajiuba ya jaddada cewa ƙalubalen da Najeriya ke fuskanta a halin yanzu na buƙatar shugabanci mai dogaro da tsare-tsare bayyanannu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng