Kano: Yadda Ake Kyamatar Yan Uwan Fatima da Aka Yi wa Kisan Gilla a Zaman Makoki
- Wasu daga cikin ’yan uwan Fatima Abubakar da aka kashe tare da ’ya’yanta shida sun koka cewa ana nuna musu kyama yayin zaman makoki
- Daya daga cikinsu ta ce dangin mijin marigayiyar na kyamar su, har ta kai an hana su gaisuwa, duk da cewa su ma mutuwar ta shafe su matuƙa
- Ta bayyana cewa lamarin kisan gilla ya jefa su cikin baƙin ciki da kunci, tana cewa har yanzu suna jin zafi kuma ba sa samun kwanciyar hankali
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Wasu daga cikin yan uwan Fatima Abubakar da aka yi wa kisan gilla da 'ya'yanta shida sun koka kan halin da suke ciki.
Yan uwan matar da ta rasa ranta dalilin kisan gilla suka ce ana kyamarsu a gidan da ake zaman makoki duk da cewa su ma mutuwar ta shafe su.

Source: Facebook
Yan uwan marigayiya Fatima sun koka
Daya daga cikin yan uwan, Sadiya Abubakar ya bayyana haka a faifan bidiyo da jaridar Freedom Radio ta wallafa a shafin Facebook.
Sadiya ta ce dangin mahafin yaran da aka hallaka suna nuna musu kyama musamman yayin zaman makoki da ake yi.
Ta ce sun je gaisuwa a unguwar amma ba su samu mijin marigayiyar ba, sai suka bukaci gaishe da babarsa amma aka hana su.
Ta ce:
"Tun da aka ce dan uwanmu ne ya yi wannan abu, sai ake ganin kamar daga jininmu ne, kamar ana nuna mana abu na rashin dadi.
"Da muka je kofar Nasarawa muka yi gaisuwa, to mijin bayanan, sai na ce to zan je wurin babarsa na yi mata gaisuwa sai aka ce a'a.
"In dawo ka da rai ya baci, sai na rasa ma'anar wannan magana, wato suna nufin daga dangin na mu ne, ba za mu so mu yi wannan abin ba."

Source: Facebook
Kano: Halin da yan uwan Fatima ke ciki
Sadiya ta ce wallahi abin da ya faru yana taba su sosai kuma suna cikin kunci kan lamarin da ya faru na kashe-kashe da yaron ke yi.
Ta ce abin takaici ne yadda yar uwarsu ta rasa ranta a mummunan hali amma kuma ana kyamarsu saboda dan uwansu ne ya aikata haka.
"Mu ma ba a son ranmu wannan abin ya faru ba, 'dan yayanmu ne, ya kashe kanwar babarsa da kuma kanwarsa da aka kwakule mata ido.
"Mu dai wannan mutuwa da aka yi wallahi har yanzu muna jin zafin mutuwar nan, bacci ma idan ina yi maganganu na ke yi."
- Sadiya Abubakar
Kisa gilla: Sarki Sanusi ya roki Abba alfarma
Mun ba ku labarin cewa Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya yi jimamin kisan gilla da aka yi wa wata mata da 'ya'yanta shida wanda ya tayar da hankali.

Kara karanta wannan
Mutanen Dorayi sun fadi ainihin abin da ya faru kan kisan Fatima da yaranta 6 a Kano
Basaraken ya bukaci Gwamna Abba Kabir Yusuf da ya rattaba hannu kan hukuncin kisa ga masu laifin kisan kai.
Sarkin ya ce rashin aiwatar da hukuncin kisa na kara bai wa masu aikata kisan gilla kwarin gwiwar ci gaba da aikata laifuffuka.
Asali: Legit.ng

