Tikitin ADC: Baba Ahmed Ya Samo Mafita ga Peter Obi kan Fafatawa da Su Atiku, Amaechi
- Tsohon mai ba shugaban kasa shawara, Hakeem Baba-Ahmed, ya yi tsokaci kan abubuwan da ke faruwa a jam'iyyar ADC
- Hakeem Baba-Ahmed ya bayyana cewa Atiku Abubakar ya fi sauran 'yan takara damar samun tikitin ADC idan har za a yi zaben fidda gwani na deliget
- Hakazalika, ya ba da shawara ga Peter Obi kan yadda zai iya samun tikitin zama dan takarar shugaban kasa na ADC
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Tsohon mai ba shugaban kasa shawara, Hakeem Baba-Ahmed, ya ba da shawara ga Peter Obi kan samun tikitin takarar jam'iyyar ADC.
Hakeem Baba-Ahmed ya ce Peter Obi na bukatar gyara dabarun siyasarsa idan yana fatan zama dan takarar shugaban kasa a zaben fidda gwani na ADC.

Source: Facebook
Baba-Ahmed ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, 22 ga watan Janairun 2026 yayin da yake magana a shirin 'The Morning Show' na gidan talabijin din Arise TV.

Kara karanta wannan
Kotun kolin Najeriya ta kunyata wadanda suka nemi a dawo da shari'ar Hamza Al Mustapha
Batun tikitin ADC a 2027
A yayin hirar, ya yi nazari kan damar da Peter Obi yake da ita a cikin hadakar adawa, tare da kwatanta shi da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar.
A cewarsa, Atiku na da babban rinjaye a tsarin zaben fidda gwani na taron deliget, saboda kwarewarsa a harkar jam’iyya da fahimtarsa kan yadda dimokuradiyyar cikin gida ke aiki.
“Mataimakin shugaban kasa Atiku ya fi sauran ‘yan takara nesa ba kusa ba wajen iya nasara ta hanyar zaben fidda gwani."
"Hakan ya samo asali ne daga kwarewarsa, yalwar goyon baya a fadin kasa, ingantattun tsare-tsare, da kuma mutane masu biyayya. Haka kuma, ya fi kowa fahimtar dabarun siyasar cikin jam’iyya.”
- Hakeem Baba-Ahmed
Hakeem Baba-Ahmed ya ba Peter Obi shawara
Baba-Ahmed ya ce duk da cewa Peter Obi babban dan siyasa ne mai karfi, salon da yake bi a halin yanzu ya yi kadan a cikin hadakar jam’iyyun da ke kunshe da gogaggun ‘yan siyasa.

Kara karanta wannan
Binciken makamai: Malami na tsaka mai wuya a hannun hukumar DSS, ya fito ya yi magana
“Ina ganin Gwamna Peter Obi da mutanensa ba sa taimaka wa kansu sosai."
- Hakeem Baba-Ahmed
Ya yaba da yadda Obi ke yawan mu’amala da jama’a da kuma kusantarsa da talakawa, yana mai cewa hakan na daga cikin karfin da yake da shi.
“Ina ganin shi ne dan siyasar da ya fi yawan zagayawa kasar nan a ‘yan lokutan nan, kuma hakan alheri ne a gare shi. Yana kokarin kasancewa tare da talakawa, wanda shima abu ne mai kyau.”
- Hakeem Baba-Ahmed
An yi muhimmin kira ga Peter Obi
Sai dai ya gargade shi da cewa dole ne ya fahimci canjin yanayin siyasar da kuma irin ‘yan siyasar da yanzu yake fafatawa da su a cikin hadakar ADC.
“Abin da ya kamata ya yi yanzu shi ne ya zauna da mutanensa, ya fahimci cewa yanzu yana takara ne da ‘yan siyasa masu tsauri da gogewa, wadanda suma suna da buri iri daya da nasa."
- Hakeem Baba-Ahmed

Source: Facebook
Baba-Ahmed ya kuma shawarci Peter Obi da ya koyi darasi daga salon Atiku, musamman wajen kula da magoya baya da rage rikice-rikicen cikin jam’iyya.

Kara karanta wannan
2027: Alamu sun nuna wasu ministoci da hadimai za su rasa mukamansu a gwamnatin APC
“Abin da mataimakin shugaban kasa Atiku ya yi na kira ga mutanensa da su kwantar da hankali, su guji cin zarafi da musayar kalamai marasa dadi, abu ne da ya dace."
"Ya kamata Peter Obi ya yi hakan ninki biyu."
- Hakeem Baba-Ahmed
Peter Obi zai iya barin ADC
A wani labarin kuma, kun ji cewa wani mai sharhi kan al'amuran jama'a, Jide Ojo, ya yi tsokaci kan zaman Peter Obi a jam'iyyar ADC.
Jide Ojo ya bayyana cewa akwai yiwuwar tsohon dan takarar shugaban kasar ya fice daga jam'iyyar ADC kafin babban zaben 2027.
Ya bayyana cewa Peter Obi zai iya ficewa daga jam'iyyar ADC idan har ya gaza samun tikitin takarar shugaban kasa.
Asali: Legit.ng