An Tura Shugaban Darikar Kadiriyya Kurkuku bayan Gurfanar da Shi a Kotun Kano

An Tura Shugaban Darikar Kadiriyya Kurkuku bayan Gurfanar da Shi a Kotun Kano

  • Kotun majistare a Kano ta bayar da umarnin tsare Sheikh Ibrahim Isa Makwarari bayan kasa cika sharudan beli da aka gindaya masa
  • Ana tuhumarsa da mallakar takardun fili da ake zargin na bogi ne, lamarin da ya samo asali daga rikicin wani fili a tsakiyar birnin Kano
  • Rahotanni sun nuna cewa kotun ta dage shari’ar zuwa wani lokaci na daban domin ci gaba da sauraron karar bayan tsare wanda ake zargi

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Kano - Wata kotun majistare da ke zama a Kano ta bayar da umarnin tsare malami kuma shugaban tsagin Darikar Qadiriyya, Sheikh Ibrahim Isa Makwarari, a gidan gyaran hali.

Kotun ta dauki wannan mataki ne bayan wanda ake tuhuma ya kasa cika sharuddan belin da aka amince masa a kan zargin mallakar takardun fili na bogi.

Kara karanta wannan

Binciken makamai: Malami na tsaka mai wuya a hannun hukumar DSS, ya fito ya yi magana

Sheikh Ibrahim Isa Makwarari
Yadda aka tafi da Sheikh Ibrahim Isa Makwarari gidan gyaran hali. Hoto: Arewa Update
Source: Facebook

Rahoton Kano Times ya ce Sheikh Ibrahim Makwarari ya bayyana a gaban Kotun Majistare mai lamba 53 da ke Normansland, Kano, inda aka karanta masa tuhumar mallakar takardun fili da ake zargi na bogi ne.

Tuhumar da ake yi wa Sheikh Ibrahim Makwarari

A cewar bayanan kotun da aka gurfanar da shi, ana zargin Sheikh Makwarari da mallakar takardun fili guda biyu da ake cewa na bogi ne.

Takardun na dauke da sunayen Alƙasim Usman Baba da Audu Danyaro Fagge, kuma ana alakanta su da wani fili da ke kan titin Ahmadu Bello Way a Kano.

Rahoton ya nuna cewa ana rikici kan mallakar filin, lamarin da ya sa aka shigar da kara domin bincike kan sahihancin takardun da ake zargin yana rike da su.

Yadda aka nemi belin malamin Musuluncin

Lokacin da aka karanta masa tuhuma a gaban kotu, Sheikh Ibrahim Makwarari ya musanta laifin da ake zarginsa da aikatawa.

Kara karanta wannan

Abubakar Malami ya yi magana game da makamai da DSS ta gano a 'gidansa' na Kebbi

Lauyansa, A. T. Shehu, ya nemi a ba shi beli, yana mai tabbatar wa kotu cewa wanda yake karewa zai kasance a shirye domin halartar shari’a duk lokacin da aka bukata.

Sai dai lauyan masu gabatar da kara, Nura A. Salisu, ya yi adawa da bukatar, yana cewa wanda ake zargi ya ki amsa gayyatar ‘yan sanda tun daga watan Oktoba, 2025, har sai da aka kama shi bisa umarnin kotu.

Sharuddan beli da ya gaza cikawa

A hukuncinsa, alkalin kotun ya amince da beli a kan kudi Naira miliyan 20 tare da masu tsaya masa guda biyu daga jihar Kano.

Kotun ta umarci cewa daya daga cikin masu tsaya masa ya kasance hakimin gunduma daga kowace karamar hukuma, tare da wasikar shaida daga majalisar masarauta.

An kuma bukaci dayan mai tsaya masa ya kasance dan kasuwa a Kano, tare da mika fasfo na kasa da kasa na wanda ake tuhuma da hotunan fasfo na masu tsaya masa.

Sheikh Ibrahim Isa Makwarari
Sheikh Isa Makwarari da aka rufe a Kano. Hoto: Darikar Qadiriyya Radio
Source: Facebook

Rahoton da Premier Radio ya wallafa a Facebook ya ce bayan bayar da belin, an gano cewa Sheikh Makwarari bai cika dukkan sharudan da kotu ta shimfida ba.

Kara karanta wannan

An cafke babban malamin Musulunci, an kai shi kotu kan cinye filaye a Kano

Sakamakon haka, kotu ta bayar da umarnin tsare shi a Gidan Gyaran Hali na Kano har sai ya cika sharudan, kuma an dage shari’ar zuwa ranar 12, Fabrairu, 2026.

Maganar gwamnatin Kano kan Sheikh Makwarari

A wani rahoton, kun ji cewa Kwamishinan kudi na jihar Kano, Hon. Abduljabbar Garko ya yi bayani game da kama Sheikh Isa Makwarari.

Hon. Garko ya sanar da cewa an kama malamin ne bisa zarge-zargen da jama'a suka yawaita a kansa kan zargi a badakalar filaye.

Kwamishinan ya kara da cewa za a hukunta duk wanda aka samu da laifi komin matsayin da ya ke da shi a gwamnati ko a wani bangare.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng