Ana Rokon Tinubu Ya Sauke Sheikh Abdullahi Saleh daga Shugabancin NAHCON
- Mambobin hukumar kula da aikin Hajji ta kasa, NAHCON, sun mika koke ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan abin da suka kira matsalolin shugabanci
- A cikin takardar, kwamishinonin sun yi zargin cewa salon jagoranci da tafiyar da kudi na shugaban hukumar ya janyo tarnaki ga ayyukan NAHCON
- Rahoto ya nuna cewa shugaban hukumar ya taba cewa wasu korafe-korafen na fitowa ne saboda wasu dalilai, ba wai hujjojin da suka shafi aiki ba
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Wasu mambobin hukumar gudanarwar Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Kasa, NAHCON, sun rubuta takardar koke ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu, inda suka bukaci a cire shugaban hukumar, Farfesa Abdullahi Saleh Usman.
Rahotanni sun nuna cewa an rubuta takardar ne a ranar 19, Janairu, 2026, kuma ta kunshi jerin zarge-zarge kan yadda ake tafiyar da harkokin hukumar.

Source: Facebook
Daily Trust ta wallafa cewa mambobin hukumar sun bayyana cewa matakin da suka dauka ya biyo bayan dogon lokaci na lura da abin da suka kira gazawa a shugabanci, duk da kokarin da suka ce sun sha yi na gyara al’amura ta hanyar tattaunawa.
'Yan NAHCON ta suka yi korafi
Takardar koken ta samu sa hannun kusan dukkan mambobin hukumar, ciki har da kwamishinonin da ke wakiltar sassa daban-daban da yankunan kasar nan.
Daga cikinsu akwai Farfesa Abubakar A. Yagawal mai kula da tsare-tsare da bincike, Prince Anofi Elegushi na sashen lasisi, da Prince Aliu Abdulrazaq mai kula da manufofi da harkokin kudi.
Sauran sun hada da wakilan shiyyoyin Arewa ta Tsakiya, Arewa maso Gabas, Arewa maso Yamma, Kudu maso Yamma, Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu, tare da wakilan JNI da NSCIA.
Zargin da ake wa shugaban NAHCON
A cikin koken, rahotanni sun nuna cewa mambobin hukumar sun zargi shugaban NAHCON da rashin bin ka’idojin tafiyar da kudin gwamnati.
Tribune ta rahoto sun ce ana yawan kashe kudi ba tare da amincewar hukumar ba, tare da bayar da kwangiloli fiye da iyakar kasafin kudi da aka amince da shi.
Takardar ta kuma yi ikirarin cewa ana gudanar da wasu kwangilolin aikin Hajji ba tare da samun takardar amincewa daga Hukumar BPP ba, lamarin da suka ce ya saba wa doka da tsarin aiki
Martanin shugaban NAHCON kan korafin
Kokarin jin ta bakin Farfesa Abdullahi Saleh Usman bai yi nasara ba a lokacin hada wannan rahoto, domin mai taimaka masa a bangaren yada labarai ya ce yana cikin taro.
Sai dai a wata hira da ya taba yi a baya, shugaban ya ce mafi yawan korafe-korafen da ke fitowa daga cikin hukumar na da alaka da dalilai na karan kai.

Source: Facebook
Ya bayyana cewa wasu na jin haushi ne saboda ba su samu wasu damammaki ba, yana mai cewa hakan ba ya nufin akwai laifi a tafiyar da hukumar.
NAHCON ta kawo sababbin dokoki
A wani labarin, mun kawo muku cewa shugaban hukumar NAHCON ya sanar da wasu sababbin dokoki a jigilar mahajjata ta shekarar 2026.

Kara karanta wannan
'Yan bindiga sun yi wa shugaban karamar hukuma, jami'an tsaro kwanton bauna a Zamfara
A bayanin da hukumar ta yi, ta ce an dauki sababbin matakai game da dukkan mahajjatin da ya yi jinkiri jirginsa ya tashi bai zo wajen ba.
Haak zalika hukumar hajji ta kawo wasu dokoki da suka shafi lafiyar maniyyata da fara raba tikitin tafiya Saudiyya da wuri domin rage matsaloli.
Asali: Legit.ng

