Sojoji Sun Kutsa Babban Sansanin Boko Haram, Sun Bankado Kabarin 'Yan Ta'adda
- Rundunar soji ta samu gagarumar nasara bayan kutsawa cikin yankin Timbuktu Triangle, wani yanki da ake dangantawa da karfin Boko Haram da ISWAP
- A yayin ci gaba da kakkabe ‘yan ta’adda, sojoji sun yi artabu da mayakan Boko Haram, lamarin da ya janyo asara ga dukkan bangarorin biyu
- Rundunar ta ce an gano kaburburan ‘yan ta’adda da dama, abin da ke nuna irin mummunan raunin da aka yi musu a wadannan hare-hare da aka kai kansu
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Borno - Rundunar sojin Najeriya karkashin Operation HADIN KAI ta ce ta ci gaba da samun galaba kan ‘yan Boko Haram da ISWAP bayan kutsawa cikin Timbuktu Triangle, yankin da ake dauka a matsayin muhimmin sansaninsu.
Rahoton ya bayyana cewa hare-haren da sojojin suka kai sun janyo mummunar asara ga cibiyoyin ‘yan ta’adda tare da raunana hanyoyin sadarwarsu da dabarunsu a yankin.

Source: Facebook
Wannan bayani ya fito ne daga jami’in yada labarai na rundunar hadin gwiwa ta Arewa maso Gabas, Laftanar Kanar Sani Uba, a wata sanarwa da ya fitar a X.
An kutsa babban sansanin Boko Haram
Sanarwar ta bayyana cewa a sabon matakin da sojoji ke dauka, dakarun Operation HADIN KAI sun kakkabe muhimman wuraren ‘yan ta’adda a Timbuktu Triangle.
Vanguard ta rahoto cewa daga cikin wuraren da aka kwato akwai Tergejeri, Chiralia da yankunan Ajigin da Abirma, inda sojoji suka samu cikakken iko.
A yayin wannan aiki, an rika cin karo da ‘yan ta’adda da ke tserewa, inda sojojin suka bude musu wuta, lamarin da ya yi sanadin hallaka ‘yan ta’adda da dama.
Asarar rayuka da aka yi a artabun
Rundunar ta bayyana cewa a yayin wannan sabon artabu, wasu jaruman sojoji da mambobin Civilian Joint Task Force sun rasa rayukansu yayin kare kasa.
Wasu kuma sun samu raunuka, inda aka dauke su cikin gaggawa ta jiragen saman rundunar soji zuwa cibiyar kula da lafiya ta runduna ta 7.
A lokacin jigilar wadanda suka jikkata, jiragen saman rundunar sojin sun bayar da kariya domin tabbatar da tsaro da kuma cigaba da kai farmaki kan ‘yan ta’adda.
Sojoji sun gano kabarin Boko Haram
A wani karin bayani, rundunar ta ce an gano kaburburan da ke dauke da gawar ‘yan ta’adda kimanin 20, wadanda aka kashe a yayin artabu a Timbuktu Triangle.
An bayyana cewa abokan ‘yan ta’addan ne suka birne su a boye, abin da ke kara tabbatar da girman asarar da suka yi yayin gwabzawa.

Source: Facebook
Laftanar Kanar Sani Uba ya ce nasarar ta rusa farfagandar ‘yan ta’adda, yana mai jaddada cewa halin tsaro a yankin Arewa maso Gabas na nan daram.
An gano rumbun boko Haram a Borno
A wani labarin, mun kawo muku cewa dakarun Najeriya sun ragargaji 'yan ta'addan Boko Haram a wani farmaki da suka kai musu.
Rundunar soji ta sanar da cewa ta gano wani rumbun da Boko Haram ke ajiye kayayyakin da suke amfani da su a karkashin kasa.
Dakarun Najeriya sun sanar da cewa sun samo abubuwan amfanin yau da kullum a rumbun 'yan ta'addan, ciki har da kayan abinci da magunguna.
Asali: Legit.ng

